Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

nan idan kin gama ci zanzo na Kai ki d'akin can Kamar sai kinfi sakewa acan" "Toh Aunty ngd da dawainiya" "Lah ba komai na sakar mata murmushi na fito daga d'akin. Na Shiga nawa mimi ce kawai a kwance da alama mahfuz ya fita massallaci. Wanka na Shiga dan tuni na watsar da wankan jego na koma normal wanka. Ina fitowa daga bandaki yayi daidai da shigowar mahfuz bai d'auke idonsa akaina ba ya zuba min Ido Nida kayana nasan hali, ya matsu yaga Ina sallah "Mallama Wai har yanzu shiru nafara gajiya fa" "Tab kwana ashirin kawai da haihuwa sai nayi arbain fa" "Wlh baki isa ba tab so kike na mutu kenan ya zauna a gefen gado,na gama shafe shafena na saka kayan shan iska. Ina sai kayi sallah zamuci abinci ko na zubo yanzu"? Bari ayi sallah Isha Kar nazo na kasa tafiya massallaci. "Tom mu tafi Palo mu zauna" Na dauki Mimi nayi gaba ya biyoni a baya. A Palo muka zauna Muna kallo muna tab'a hira Yana latsa wayarsa hankalinsa dai Yana Kan wayar gabad'aya. Sai ni kedai ke zuba surutuna har aka Kira sallah Isha ya fita massallaci bai dawo gidan ba sai wajen tara daga zuwa massallaci abincin ma da na jera Mana ya hucce tuni na cika nayi fam zuciyata ta fara rayamin kodai zance yaje take naji hankalina ya tashi,Ina tsoron tsinaniyar yarinya nan Mai nacin tsiya ce ta dawo rayuwar mijina wayata na d'auko dan na kirashi sai gashi ya shigo,da carbinsa a hannu da jalabiyar sa. "Daga zuwa massallaci abban Mimi"? Ina k'ofar gida wlh da Hamisu muke ta hira da kin leko zaki ganmu ai Sai a lokacin hankalina ya kwanta Muna cikin cin abincin Muka ji motsin bud'e k'ofar d'akin sai ga ummi ta fito da dogon hijabinta har kasa mahfuz ko kad'an bai dago ba Ina k'ok'arin Magana tace "Aunty dama bacci nakeji shine nace ko Zaki nunamin d'akin"? Mik'ewa nayi Ina sude hannuna nace "eee zomuje nama dauka kinyi baccin ne wlh' Nayi gaba tana bina a baya har muka fice daga palon,dama d'akin duk da baa kwana a ciki Ina yawan gyarawa Ina Kuma turarawa sai dai ba bandaki a ciki, bandakin a tsakar gida yake idan nayi baki da bandakin tsakar gidan suke amfani ,Yan uwa ke Shiga bandakin cikin daki. Muna Shiga d'akin nace "dafatan d'akin ya Miki"? Kai sosai ma wlh yayi aunty ngd Allah yasaka da alheri" "Lah ba komai ai an Zama daya sai dai nace sai dasafe kenan" "Toh aunty sai da safe a shafa min Kan Mimi" Da murmushi na amsa Mata na fito daga d'akin. Sai da muka gama cin abincin na kwashe komai na Kai kitchen na dawo na tarar da mahfuz na latse latse a wayarsa. Nima wayata na d'auko na hau latsawa Ina chatting Ina kallo kafin goma naji bacci ya fara k'ok'arin daukana. Hakane yasa na kashe data na kalli mahfuz daya danke wayar sa da hannu biyu nace "Tom nidai bacci nakeji zanje na kwanta" "Kije kiyi kwanciyar ki dan ni ba bacci nake ji ba ko na biki daki ciwon maran zaki sani a banza nidai na fara gajiya fa tam" "Kazo muje mu kwanta na maka tausa wlh Zan maka dabaru" "Naki fa kibar ni na cigaba da hira da abokina" Ya hasko min fuskar wayarsa Inda naga sunan Abdul din da Abokina "Ai shikenan sai ka shigo" Bai bani amsa ba Ina shiga ciki na canza kayan jikina zuwa na bacci Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani bansan lokacin da ya shigo ba. Washegari da wuri na tashi dan na hada breakfast dan mahfuz da wuri yake fita. Ina cikin soya dankali naji sallamar ummi. Na amsa Mata daga kitchen ina mamakin me ya sa ta tashi da wuri haka. Har kitchen tazo ta sameni muka gaisa da ita Ina satar kallonta Ina San yanda take shigar hijabi har kasa da alama tana da kamun Kai "Aunty Ina tsintsiya nayi shara"? "Ummi dan Allah koma kiyi kwanciyarki dan kawai ki tayani aiki Kika taso" "Dan Allah karki hanani tun jiya nakeso na tayaki kina hanani" karfe Tara zanje wajen da zamuyi program din shiyasa na tashi da wuri" Duk yanda naso hanata ki tayi akan dole na nuna Mata wajen da tsintsiya yake ta d'auko ta fara share palon. Har tsakar gidan naji tana sharewa. Sai da ta gama ta Kara shigowa da bokitin mopping da abin mopping din tana cikin mopping mahfuz ya fito daga d'aki cikin shigar suit sai kamshin turare yake. Adaidai lokacin da Nima na fito da farantin abincin karyawarsa. Gaisuwar ummi ya amsa ba yabo ba fallasa ya tambayeta ya bakunta ta sunkuyar da Kai tana murmushi nidai idona nakanta atoh karta sake ta kallarmin miji ganin na ajiye farantin a gabansa yasa ta ajiye abin mopping din tana "idan ya gama na dawo na karasa" Hankalinta na Kara gani,dan naga tana nesa nesa da mijina haka nakeso shima mijina ya iya tsare gida. "Mai kike murmushi ke kadai"? Tambayar da mahfuz ya jefomun kenan "Wlh yarinya nan nada hankali mahfuz da gani ta samu tarbiyya sosai duk da a Lagos take zaune" Tab'e baki yayi bai ce min komai ba Nima ban Kara magana ba har ya gama cin abincinsa Ya Mike zai tafi na tafi dan na raka shi munje bakin k'ofa ya juyo Yana "Na manta ban fada Miki ba Abdul jiya yace na fada Miki wanan yarinyar ba komai ta iya ci ba ya roki arzikin a ringa tambayarta abinda zata ci ko a barta ta dafa abinda takeso dakanta wlh badan kin dage ba da sai na Masa rashin mutunci nida gidana azo ana min iko" "Allah sarki wlh ba damuwa ai kana ganinta kasan Yar hutu ce ba irinmu da duk abinda muka samu ci zamuyi ba Tom ba damuwa ai tunda ba laifi muna da Abubuwan Yan gayu yanzu a gidan idan ma cornflask take so ta ringa Sha gashi nan" "Ku kuka sani" Yace a daidai lokacin da ya ida fitar da machine dinsa ya tayar ya tafi Ina daga masa hannu. Ina komawa ciki na karasa mopping din na turara koina kafin na koma d'akin Ummi dan na tambayeta mai zata ci. Kwalliya na tarar tanayi a lokacin da na Shiga tana ganina ta saki murmushi tana "so nake na shirya kar nayi latti" "Kina nufin bazaki karya ba Zaki tafi nidai na soya dankali da kwai sai kayan shayi bansani ba kinaci ko bakya ci idan bakya ci sai a sama Miki wani abu dan Abdul yace Wai ba komai kike ci ba" "Eee wlh aunty duk wani abu Mai maiko ban fiye ci ba da safe nafiso nasha corn flask haka ko bakin tea" "Toh shikenan ki gama shiryawan akwai cornflask sai ki hada ki Sha" Godiya tamin na sakar mata murmushi na fito. Ban Dade da fitowa ba sai gata ta shigo da dogon hijabinta har kasa da farin glass. Tana Zama na dauko mata kofi da cokali da tuni na ajiye Mata Madara da cornflask din Cikin nutsuwa ta hada ta Sha sai satar kallona take narasa Mai yasa take San satar kallona. Tana gama Sha ta mik'e

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26