Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
Download Book

kasa sakin jikinsa yayi Kamar Mara gaskiya sai yake Jin Kamar Lubna zata iya fadowa gidan. Hadeeza kuwa ko a jikinta ta zage ta gama mopping ta fara goge kayan kallon sai ce mata yake ta barshi amma fir tak'i har sai da ta gama tsaf ta koma ta zauna tana "da akwai wuta har guga zan maka" Murmushi ya sakar mata Yana "haba dai wankin ma bayarwa nake Mai wankin ne baya gari" Tana k'ok'arin Magana wayarsa ta fara ringing gabansa ne ya Yanke ya fadi daya ga Lubna ke kiransa. Mikewa yayi da sauri yayi hanyar d'aki ya kalli Hadeeza data kura Masa Ido Yana "Ina zuwa" Yana shiga d'akin tayi sauri ta mik'e ta leka k'ofar da ta gani,ganin kitchen ne yasa ta tab'e baki ta leka daya d'akin da ke bud'e ta daga labulen nan ma ta tab'e baki tana "ko kayan kirki.ma Babu a gidan da sannu Zan shigo kifita insha Allahu" Tayi sauri ta koma ta zauna ta cigaba da karewa palon kallo,Sam palon lubnar bai wani burgeta ba kayan lubnar ma duk ba masu tsada bane da zasu daga mata hankali. Rigar jikinta ta kara gyarawa na fulaninta ya fito ta saman riga sosai,dan so take ta rikita mahfuz yayi ya fito ya aureta. Da zata samu yanda take so da lubna ma kafin ta dawo daga haihuwa zata zo ta tarar da sunyi aure da mahfuz har ta tare,sai dai ta rasa mai yasa mahfuz ya kasa motsawa duk gani take tsoron lubna yake,so take ma taga hoton lubnar amma babu ko daya data gani a palon,wayar mahfuz Kuma akwai password a wajen hotunan,da alama shegiyar matarsa ce ta kirashi ya wani shige daki,take taji ranta ya fara b'aci ta had'e rai. LUBNA Kwalliya nayi sosai na gyara d'akin kanina dan nayi kewar mijina duk da yana zuwa ganina so nake yau idan yazo mu dan keb'e dashi na faranta masa rai dan nasan halin kayana hakuri kawai yake. Da taimakon kanwata zainab na tuka Masa tuwon semo da miyar wake na jera duk a d'akin kanina. Karfe biyu muka yi dashi akan zaizo idan ya gama wankin da yake. Ganin biyu da rabi tayi baizo ba yasa na fara k'ok'arin kiransa a daidai lokacin da kiran makociyata ya shigo Mmn Iman" Ina dauka tace "Lubna kin dawone"? "Na dawo Ina"? Shine tambayar da na mata cikin mamaki "Ina nufin kin dawo gidanki ne"? "Aaa Ina gidanmu mmn imam Mai zai dawo dani nida na zo gida haihuwa lafiya kuwa" "Eee toh lafiya ba lafiya ba wata naga kamar ta Shiga gidanki sai na dauka ko kin dawone" Kirjina wani irin bugawa yayi nace "wata kika.ga ta Shiga gidana wacce" "Nima bansani ba wlh ko bakuwa kikayi batasan bakya nan ba"? "Mmn Iman da idonki Kika ga mace ta shiga gidana Dan Allah jeki dubamin wacece" Tana k'ok'arin Magana na katse wayar da sauri ko dai budurwa Mahfuz ce taje har gidana dan taga bana nan,? Yanzu mahfuz zai iya cin amanata? Mikewa nayi da sauri hankalina ma na neman barin jikina sosai zuciyata ke sak'a min kila budurwar mijina ce taje har gidana, Wayar Mahfuz na Kira jikina sai bari yake sai dube duben mayafi ko hijabi nake akwai tazara daga gidanmu zuwa gidana amma tabbas zanje gidana na indai har naga mace wlh tallahi sai na raba ta da numfashin ta,Yana daga wayar nace "Mahfuz kana Ina"? "Gani a gida na shirya yanzu zan taho" "mahfuz karya kakeyi wlh mace ka kawo min har cikin gida sabida kaga bana nan, yanzu cin fuska da cin amanar taka har ta Kai ka kawo min mace gidana Mahfuz innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" "Kanki daya kuwa wacce mace na kawo gidan kin fara ko" Mahfuz yace cikin dauriya numfashin sa na Neman daukewa "Ai gani nan a waje wlh tallahi idona idonta.mahfuz sai na rabata da numfashinta.mahfuz" Na katse wayar mahfuz yayi waje da sauri a daidai lokacin da ake buga kofar gidan Hankali a tashe ya d'auka da gaske Lubnar ce hakane yasa yayi Kan Hadeeza aguje baiyi wata wata ba ya rike hannunta ta ya fara janta ya kaita daya d'akin ya tura ta bandakin daya d'akin nasu "Mai haka mahfuz lafiya kuwa"? "Shiii kiyi shiru Lubna ce ta dawo" Cire hannunsa tayi daga bakinta tana "Toh sai me dan ta dawo ai ba wani Abu mukayi ba shine hankalinka ya tashi haka Mahfuz" "Dan Allah kiyi shiru Hadeeza Ina zuwa karkiyi magana " Yace tare da jawo kofar yayi waje da sauri Lubna Ina katse wayata Kiran makociyata na Kara shigowa wayata a daidai lokacin da na samu na tare abin hawa Ina dauka tace "gani a k'ofar gidan Ina kwankwasa wa" "Ki taimaka min mmn Iman Ina hanya yanzu dan Allah idan har Kinga mace a gidana ki rikemin ita har sai nazo Dan Allah dan annabi wata kwartuwa yarinya ce take bibiyar mijina" "Nidai Naga shigar mace banga fitowarta ba,ba lallai Kuma budurwar tasa bace kila bakuwa kikayi amma dai Ina kwankwasa k'ofar ba'a bud'e ba" Katse wayar tayi adai dai lokacin da Mahfuz ya bud'e kofar ganin mmn Iman ce dan.ya Santa yasa shi sakin ajiyar zuciya take zuciyarsa ta bashi ita ta gayawa Lubna mace tazo gidan,kila taga shigar Hadeeza gidan. Ko amsa gaisuwar da ta masa baiyi ba yace "Yanzu Mai amfanin abinda kika yi mace da cikinta kin daga mata hankali,daga gidan mu aka aiko min da abinci kanwata ce kuma tsabar munafirci shine Kika Kira lubna kika ce Mata mace tazo gidana dan Allah bakiji kunya ba da kika zo kina kwankwasa wa dan ki tabbatar toh kishigo kigani" Yace mata a dan tsawace Ja da baya mmn Iman tayi sam bataji dadin abinda lubna tayi mata ba "Wlh ba ni nace Mata mace tazo ba ni muciya nazo ara ma wlh" Tsaki Mahfuz yayi ya rufe k'ofar Mmn Iman itama ta juya da sauri ta shige gidanta bakin ciki Kamar ya kasheta banda b'atar basira da rashin hankali irin na lubna name zata kira ma mahfuz da zuwan zatayi ai bai dace ta kira mahfuz ba. Mahfuz kuwa Yana jikin kofa Yana ganin mmn Iman ta shige gida yayi sauri ya koma bandakin da Hadeeza take itama ta cika tayi fam,bata bari yayi magana ba ta fito daga bandakin ta fito palo ta d'auki Jakarta bata saurari mahfuz dake mata magana ba ta fice daga gidan tana zuba sauri mahfuz ya balain Kona Mata rai har mace yake tsoro haka Kamar wata uwarsa,har da kaita wani bandaki ya kulle wlh da ace ma tazo ba abinda zai hana ta fitowa ta ganta sai dai duk abinda zai faru ya faru,taya Mahfuz zai iya Kara aure Yana tsoron matarsa haka,yanzu Yana nufin ma yafi fifita matarsa akanta,duk wahalar nan da take sha akansa shine zai wani kaita bandaki ya b'oyeta sabida Yana tsoron kar matarsa ta ganta,shi daya Kamata ma ya fara gayawa matarsa tun yanzu akan aurenta zaiyi. Da tsanin bakin ciki ta isa gida tana zuwa ta hau watsapp ta fara zanna Masa ta WhatsApp akan ta gaji da wanan kumbiya kumbiya idan har yasan ya isa da gidansa ba tsoron matarsa yake ba ya turo manya gidansu. Mahfuz Wani

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26