Chapter 16
Chapter 16
abu da muke bukata, Girgiza masa Kai nayi dan bana Jin akwai abunda muke bukatan dan yayi Mana siyayya daidai karfinsa nama Mai yawa ya siyo aka saka min a fridge. Bakin da ake tayi yasa ya mik'e dan mahaifiyarsa ma tazo "Nidai bari na fita waje idan ana bukatar wani abu ki kirani na manta ma Abdul yace na gaisheki zai shigo Nan da jibi" Murmushi na saki dan muna shiri da abokinsa Abdul sosai Yana da matukar kirki Yana Kuma sona da Mahfuz aikine ya mayar dashi garin inyamurai. Har yaje bakin k'ofa nace "kaci abinci kuwa"? Gyada min kai yayi Yana "Na Sha kunu ama koshe nake ke kuwa na zama uba wa yake ta wani abinci. Murmushi na sakar Masa ya fice daga d'akin budurwar sa da ta fadomin yasa naji farinciki da nake ciki Yana neman gushewa,tun jiya dai banga alamar waya a hannunsa ba Addu'a nake Allah yasa maganganun da mukayi dashi jiya yasa ya canza alhamdulillah na haihu lafiya yanzu zan daura damarar kwato mijina na dawo da hankalinsa kaina da izinin Allah Mahfuz Yana fitowa daga d'akin ya Shiga daya d'akin da yawancin Yan barkan anan Suka zauna wasu Kuma a Palo,ba laifi lubna Yar dangi ce shima haka, Wajen Mahaifiyarsa Hajiya Ammi yayi dan so yake yace Mata fita zaiyi. Sai dai Yana gaya mata ta mik'e tana itama tafiyar zatayi ya sauketa a gida. Tare Suka fito daga gidan Bayan ta Kara yiwa Lubna barka. Har gida yaje ya sauketa baiyi niyyar shiga gidan ba tace ya shigo magana zasuyi. Yasan halin mahaifiyarsa da mita da kin d'auke Ido akan Abu duk kankantarsa duk tunani yake kila wani abun tagani a gidan nasa. Sai dai Yana zama tace "Dazu nan wata yar albarka tazo har gidanan ta gaisheni tace min ita budurwa ka ce yama take da suna yauwa Hadeeza yarinya tana kyau da hankali ga tarbiya wlh kaga ma abin arzikin da ta kawomin da ta tashi tafiya har dasu kyautar kudi da dukan alamu Yar baban gida ce"? Tace tana zaro turmin zani daga ledarsa har da mayafi da turare Tsananin mamaki ya hana mahfuz magana "Ammi Hadeeza ce tazo har gidanan"? "Eee fa wlh har gidanan tazo yarinya ta matukar burgeni a gaskiya Ina kaunarta kaga tsalallen atamfar da ta kawomin har da mayafinsa kaga na samu na sawa ma ranar suna" Tace tana washe baki Mahfuz kasa magana yayi dan har lokacin mamakin yanda Hadeeza tasan gidansu yake.har gidansa ma ta sani,haka kawai yaji baiji dadin zuwanta gidan su har tazo wajen Mahaifiyarsa ba wani zubin Yana ganin rawar kanta ba kad'an ba "Baka ce komai ba ka tsaya kana wani zare Ido ko bakaji dadin kyautar da ta kawomin bane ta girmamani a matsayina na mahaifiyarka yau naga yaro da yiwa uwarsa bakin ciki" "Wlh ba Haka bane Ammi ni mamakin yanda tasan gidanan nake" "Mai wani abun mamaki yarinya Yar arziki a Ina kuka hadu da ita ne"? "Ammi tsohuwar budurwa ta ce fa ita na fara nema kafin lubna Allah baiyi ita zan aura ba na auri lubna sai kuma yanzu ta dawo rayuwata,k'arfi da yaji so take muyi aure Bayan ban dade da auren ba,har ga Allah banida niyyar Kara aure yanzu amma ta dage min" "Aikuwa gwara ka daura damaran auren dan nikam tayi min haka nake san mutum mai mutunci da sanin ya Kamata,matarka tunda ka aureta sau daya ta taba bani turmin zani wanan kuwa bama ka aureta ba ta gwangwaje ni da irin zanin nan har dasu mayafi ga kudi Kuma habawa ai ka shirya Kara Aure insha Allahu" Yasan halin mahaifiyarsa Sarai wajen san abun duniya yasan kila ma ta zubar Masa da mutunci a wajen Hadeeza Sam baiji dadin zuwan da tayi gidansu ba. "Kayi mata godiya idan kaje" "Zan mata insha Allahu bari naje" Yace tare da mik'ewa yayi waje Yana k'ok'arin tayar da machine dinsa kiranta ya shigo wayarsa tun da ya baro gidansu jiya basuyi waya da ita ba dan wayarsa a kashe take bai ma kunna ba sai dazu da text dinta ya shigo bai Kirata ba dan so yake yaje inyaso ya fada mata haihuwar Lubnar daga wayar yayi Yana "Gani Nan zuwa yanzu" Ya katse wayar...... Kunsan yawancin novel dina true life ne na baya na canza na Kara daga wanan shafin zuwa na gama ya faru a gaske KAYAN MATA Assalamualaikum kina mace hadaddiya komi kincika ama kinada nakasu tawurin dadadawa miji? Shin kinkai kin isa kina gogayya d sauran mata Amma tafannin ozaroom mishkila tasamu? Shin sanyi y addabeki tayanda Baki iya gamsarda miji kullum kina makalemai yana kauda Ido? Shin minene matsalar? Kinshiga ko Ina kinnemi magani bawani chanji? Tosaurara yar uwata aminiyar arziki, ubangiji yakawo mikini har inda kike,kizo kiji qawata, Inada maganin sanyi me fatattakar kowani irin sanyi duk fitinarshi d izinin ubangiji seyabarki, Munada magungunan mata masu matuqar kyau,hadaddu gangariya kizama t gaban goshi,komi kikace oga yace don, 馃グ kikerewa sa'o'i, kizama abun riritawa abun tarairaya a kudi qalilan,karki cuci kanki kizauna kina cewa ayni nasan kaina,a inadin? Wallahi ko kanada kyau qara d wanka Kisha kiyi qattt kigigita oga, Munada tsumi nau'i nau'i Gumba ta madara,ridi,gyada,dabino,kwakwa,dasauransu Akway ruwan jaraba Ruwan Dadi Hadin minannas Hadin dafa kaza(manta uwa) Hadin yar gaban goshi, Turarukan mallaka. Duk a farashi mesauqi. Serious buyers call, WhatsApp 07046881166 Senajiku kusiya kuyi godiya Kuma kumin addua鉂わ笍nagode [6/29, 7:54 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA* *NA SADNAF* *E.W.F.* *PAID BOOK* *PAGE 8* Koda isarsa a karamin palon gidan da suke zance yayi zamansa Yana jiranta,tun kafin ta iso palon ya fara jiyo kamshin turaren ta, Hadeeza ba baya ba wajen saka turare a ransa Yana so ya nuna mata rashin Jin dadinsa da zuwa gidansu da tayi baya san garajen nan da takeyi yafisan su bi komai a hankali yasan Yana santa amma har ga Allah da san zuciyarsa ne babu bukatar wani Karin Aure,Sam baiji dadin yanda lubna duk ta dago halin da yake ciki da Hadeeza ba tun a jiyan ya daura damarar canzawa wajen iya takunsa sam bayaso ta ringa Jin kamar ya daina santa,yasan tana iya k'ok'arin ta wajen faranta Masa Sallamar da Hadeeza tayi cikin takunta najan hankali ya katse masa tunanin da yake ya dago idonsa Yana kallonta har ta samu waje ta zauna ta sakar Masa murmushi,dayasa ta kashe Masa jiki kwana biyun nan tana shigar dake dan bayyana surarta. "Sai yanzu ka tuna dani,jiya ko bacci banyi ba dan banji muryarka ba" "Lubna ta haihu fa an samu bby girl shiyasa Sam jiya ban bi ta Kan waya ba" Sai da ta dau tsawon lokaci kafin ta daure ta saki murmushi dan Addu'a tayi a ranta dama mutuwa lubnar tayi da tazo haihuwar "Masha Allah Allah ya Raya mana ita kace na samu takwara" "Sunan lubna na saka Mata zaa ringa kiranta Mimi ashe kinje gidanmu dazu"? Kamar ya watsa Mata ruwan zafi dayace sunan lubna ya sawa yarsa dan taji labarin idan har miji yasa wa yarsa sunan matarsa ba karamin kaunarta yake ba,bata so ta nuna Masa rashin Jin dadinta yak'e tayi tana "Eee dazu naje na gaida mama tunda baka tab'a cewa muje na gaisheta ba" "Dama kinsan gidanmu ne"? "Tunda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26