Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

murmushi daya shigo dashi ya kau Yana "Lubna lafiya kuwa"? "Ba komai" Kawai nace Masa na samu waje na zauna Ina Masa sannu da zuwa ya amsa Yana "Lubna ban Saba ganinki a haka ba lafiya kuwa"? "Wlh wanan yarinya ce ta bata min Rai kasan na tsani naga an shigar min daki kwatsam sai gata ta shigo min daki ni naga alamar tana da rawar Kai a gaskiya in zata cigaba da min haka bazamu shirya ba" "Oo keda kanki yau Kuma kika cewa ta bata miki rai, da da Kika kawota wancan d'akin fa" "Gaskiya badan kusancinka da Abdul ba wlh gobe zata barmin gidanan bana San munafirci kaga kwalliyar da tayi sai kace wata matar gidan" Daga hannuwansa sama yayi Yana "Ni ba abinda nagani mallama muje ki hada.min ruwan wanka tunda zu ma nake kiranki baki dauka ba" Mik'ewa nayi na nufi d'akin ya biyoni a baya. Koda na zuba Mata abincin a bakin k'ofa na ajiye Mata "Ina ummi ga abincin ki ban tsaya jiran ta fito ba na koma Palo mukaci abinci da mahfuz . Muka tab'a hira lokacin baccina nayi na mike dan nasan sai yayi kallonsa na masifa daya tsiro dashi. Washegari ban bari ta wani tayani aiki ba kafin ta fito na gama komai yau Kam bata Isa na Mata wani abin karyawar va abinda nayi zata ci. Doya da kwai da tea. Har mahfuz ya fita bata fito ba. Ban Kuma damu na dubata ba bansani ba yau ko ba inda zataje,nidai yau fita zanyi zanje kunshi da kitso. Mmn Iman tun jiya tana unguwarsu. Idan ba inda zataje sai ta zauna tayi gadin gida na kulle palona. Na shirya kenan,na fito Palo sai gata ta shigo palon sanye da hijabinta har kasa a Raina nace munafika Gaisheni tayi.murya na rawa na amsa Mata Ina k'ok'arin goya mimi tace " Aunty ko dai akwai abinda na miki ne bansani ba"? "Mai zakimin kuwa ummi"? "Wlh sai Naga kamar na Bata Miki Rai bansani ba Dan Allah kiyi hakuri" Tuni naji ta bani tausayi nace "ba komai wlh ummi jiyan ne raina a bace,ga abincin ki nan fita zanyi kinsan saura kwana biyu sallah zanje kitso da kunshi" "A koshe nake Aunty bana Jin yunwa yau nima ba inda zanje Dan Allah ko zan iya binki kunshi bana so na zauna ni.kadai" "Ba damuwa ki zo mu tafi. Mik'ewa tayi da sauri ta fita waje ba dadewa sai gata ta fito da hijabinta har kasa. Na kulle ko'ina muka nufi gidan kunshin..... [6/29, 7:54 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA* *NA SADNAF* *E.W.F.* *PAID BOOK* *PAGE 9* Koda muka koma ciki,a kasan kafet ta zauna ta miko min hannu tana na bata mimi. Mik'a mata Mimi nayi Ina "Mai Kika zauna a kasa ki koma ki zauna mana akan kujerar" "Nan ma yyi Aunty ngd" "Kai Kai sunana Lubna ba Aunty ba" Murmushi kawai tayi ta cigaba da Wasa da mimi tana ta zuba mata kiss a fuska ni.kuwa take ta sake burgeni ni nasan Zainab gajiya tayi ta gudu toh tayi a banza tunda na samu Yar tayin hira. Hira na fara janta dashi Ina dan jefa Mata tambayoyi duk dan ta saki jikinta,anan take fadamin ta kamalla degree dinta tana neman aiki, shine kafin su dauketa suka turota nan ta danyi wani programme a shiyarsu ta nan. Ina da saurin sabo da mutum kamar na dade da saninta haka na hau janta da hira bamu tashi ba sai da aka Kira sallahr laasar. Na nuna Mata d'akin bakin akan ta Shiga ciki tayi sallarta. Nima na shige d'akina dan na canzawa Mimi Pampers dan bansamu tsarki ba tukunna Ina cikin sawa Mimi Pampers Kiran Mahfuz ya shigo wayata Ina dagawa yace "Ashe har Abdul ya tafi yanzu nan ya kirani Kuma kinsan dan wulakanci bai biyo ta office dina ba wlh sai na Masa rashin mutunci" Murmushi na saki Ina "kunfi kusa kaima kasan bazai tafi batare da ya ganka ba kila anjima kaga ya dawo,tare yazo da wata bakuwa Wai zata yi wani program Yar yayarsa ta Lagos bansan bai fada ma ba sai daya zo tafiya Wai Idan ka dawo na fada maka" "Wlh Abdul ya Raina ni yanzu nida gidana zai kawo min wata bai nemi izini a wajena ba" "Kai Kam da rigima kake wlh yanzu dan Yar yayarsa zata zo tayi kwana biyu a gidanan shine sai ya nemi izininka"? Tsaki yayi Yana "Zan Masa rashin mutunci ai sai mun hadu dashi tukunna" Murmushi na sake yi nace "ba ruwana Ina daga gefe" "Ina Mimi"? Gata nan yanzu nan na canza Mata Pampers goyata zanyi na Shiga kitchen Hira Muka dan Kara tabawa kad'an kafin ya kashe wayar na goya mimi na fito nayi kitchen banga ummi a palon ba nasan tana cikin d'akin kila hutawa take tunda Lagos ba nan ba duk da banga alamar gajiya a tare da ita ba kila jirgi suka hau dan su Abdul din nada rufin asiri. Ina cikin kitchen din na jiyo muryar Mmn iman tana kwankwasa k'ofa. Ajiye muciyar hannuna nayi naje na bud'e Mata k'ofar ta shigo da ledoji a hannunta ko bata fadamin ba nasan na menene kayan gyara ta kawo min dana bata sautinsa dan so nake na tsantsame kafin na samu tsarki. "Ke Kaya masu zafi ta kawo wlh sai kinyo ciko" Gefenta na zauna na fara duba kayan a daidai lokacin da ummi ta fito daga d'akin motsinta yasa muka dago muna kallonta nace "kinfito kenan da zan shigo nace ban sani ba ko baccin gajiya kike" Murmushi tayi a daidai lokacin da ta karaso wajenmu ta zauna a kasan kafet tana "Aa idona biyu ai ba wani gajiya da nayi tunda jirgi muka biyo Ina wuni" Ta gaida mmn iman ta amsa cikin sakin fuska tana "kice bakuwa kikayi"? "Eee wlh tun daga Lagos tazo" Na bawa mmn Iman amsa na cigaba da duba jarkokin tsumin data shigo dasu da dan bokitin da aka dafa min ciccibi a ciki. Kice Abban Mimi zai Sha Dadi na kashewa mmn Iman Ido data dafe baki tana "lah bakida kunya fa agaban bakuwar kike badala ko dai matar aure ce"? Sunkuyar da kai tayi da muka hada ido da ita dan ni banma San kallona take ba Murmushi nayi Ina "ba matar Aure bace wlh Mai dan nayi wanan hirar a gabanta ai Yan matan suma yanzu sun San komai" Na karashe Ina dariya a daidai lokacin da nake dandana wani zuma Nan ma na sake hada Ido da ita ta sunkuyar da Kai da sauri Mmn Iman tace "nidai mallama ki bani cikon kudin dana ranta Miki" "Har nawa Kika ranta min"? "Dubu bakwai na cika Miki wlh" "Kai dubu ashirin na baki fa" "Kwarai kuwa ai kayanta masu kyau ne da tsada wlh tamkar budurwa Zaki koma duk Inda Kika saka kafarki bbn mimi na biye dake" Washe baki nayi Ina "Zan baki kudinki idan na Kai shi duniyar can kila na baki fiye da Dubu bakwai din" Tafawa muka yi da ita ta mik'e tana "naji ma kamar abincin da kika Dora na kauri bari naje Nima na dora nawa girkin na biye miki ba abinda zan zanyi. Tayi hanyar waje

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26