Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

wajen aiki awa biyu a tsakani sai ga Hadeeza a office dinsa. Rabonsa da ita shekara biyar kenan taci kwaliyya ta Kuma yi kyau kamar ba ita ba ta canza akan sanin daya mata a baya ta Kara gogewa sai kamshin turare take. Ledar da ta shigo dashi ta ajiye masa agabansa ta langabar da kai ta hau matsawar kwalla. Mahfuz kuwa kau da kansa yayi yana "Hadeeza dan Allah mai kike nema a wajena" "Ba abinda nake nema a wajenka so nake kawai komai ya wuce mu cigaba da soyayyar mu" "Shekara daya da Aurena Hadeeza idan ba yaudararki kikeso nayi ba banida ra'ayin yin soyayya ko na Kara aure matata ta isheni rayuwa Dan Allah kije ki nemi wani" Bai idda magana ba ta fara hawaye har da sheshek'a mahfuz ya shareta ya cigaba da danne danne a laptop din gabansa sunansa data Kira yasa ya dago ya kalleta "Allah ya jarrabceni da kaunarka mahfuz bansan ya akayi na wayi gari cikin tsananin sanka ba amma tunda kace haka dan Allah Ina neman alfarma mu cigaba da zumunci ka zama abokina" "Ana abota tsakanin namiji da mace ne Hadeeza cigaba da muamalla dake kamar dai muna soyayyar kenan Mai amfanin haka" "Dan Allah Mahfuz iya alfarmar da zaka min kenan ko ba kullum ba muringa waya ko chatt har Allah ya yaye min" Burinsa kawai ta tafi daga mata Kai kawai yayi yace jeki naji" Washe baki tayi ta mike tana "Nagode mahfuz ga wanan ba yawa sai na kiraka anjima" "Hadeeza karki kirani kinsan inada mata kidaina kirana anyhow" "Bakada matsala" tace tare da sakar.masa murmushi ta juya tana wani irin takun daya sa Mahfuz kasa d'auke idonsa akanta har ta fice. Sai da ya gama abinda yake ya bude ledar da ta kawo turare ne.masu kamshi sai snacks da akayi wrapping a foil paper har zai mayar da snacks din ya gutsiri meatpie din yaji ya masa dadi a haka ya gyara Zama yaci iya Wanda zai iya ci dan ta hutashe shi siyan abincin Rana, lubna taso ta ringa aika Masa da abincin rana ya hanata dan baya san ya wahalar da ita. Tunda ga lokacin Hadeeza da zage wajen zuwa office d'insa tun bai wani bata fuska ba har ya fara bata fuska duk zuwan da zatayi da kalar abinda zata kawo Masa, text kuwa haka take tura masa. Bai tab'a d'aukar wayarsa ya kirata ba sai dai ita ta Kira shi. Yau da gobe a hankali ya fara damuwa da lamuranta har idan bata zo wajen aikinsa ba bayajin dadi, yayi balain sabo da snacks masu Dadi da take kawo Masa. A irin wanan yanayin ta daina aiko Masa da text din da ta sabar.masa dashi,ta bar zuwa office d'insa haka.kawai.yaji ya damu tun Yana ganin zai iya daurewa har yaga bazai iya ba aranar da aka samu sati daya baiji daga wajenta ba ya kirata a waya sai daya mata.miscall ya kusa goma Kafin ta daga murya can kasa da Sunan bata da lafiya shiyasa yaji shiru Nan kuwa karya takeyi so take ta gwada shi taga ko ya damu da ita. Ana tashi daga wajen aikin ya kirata ta mishi kwatancen gidan da suka koma bai Sha wahala ba dan ba wani nisa tsakanin gidan nasu da wajen aikinsa. Sai gashi har da kayan dubiya. Har dan karamin palon gidan aka masa iso da alama ba kowa a gidan sai kannenta da suka kasance yaran kanin mahaifinta. A kwance ya sameta a doguwar kujera ta Sha kitson attach da tayi parking,sai riga yar kanti armless da taje mata har kasa duk da batayi kwalliya ba bata yafa komai ba tayi wa mahfuz kyau. Nanarkewa kawai take tana shagwaba Kamar bazai tafi ba lubna dake ta kiransa a waya yasa ya Mik'e ya Mata sallama ya ajiye Mata kayan dubiya ya fito. Wani ikon Allah Koda ya dawo gida suna Hira da lubna Yana tuno Hadeeza da yanda ta ringa Masa shagwaba tunda ga wanan lokacin ya dawo da Hadeeza rayuwarsa ta samu matsayi a zuciyarsa dan ta Kai yanzu har breakfast take Masa idan zai wuce ya karba da Rana ma abincin take aika Masa. Dak'yar yake yakice cin abincin dare a wajenta gudun kar Lubna ta zarge shi. Zuwa yanzu baya iya kwana biyu bai ga Hadeeza ba duk da ba abinda Lubnarsa ta rage shi dashi wanan kenan. LUBNA Jan kunshi mai kunshina ta rangada min a hannu da kafa. Tana ciremin na sallameta ta tafi na hada Abubuwan da nake dan gyaran jiki dashi na hada na mulka a jikina dashi sabida fatata ta Kara laushi. Iya kokarina zanyi dan na dawo da hankalin Mahfuz kaina bazai yu wata Yar iska can ta kwace min shi ba,nima sai a yanzu naga wautata da na hau fushi da shi,waya sani ma ko kwana ma yayi jiya yana waya da yar iskar SR. Sai da na goge ko'ina na jikina na Shiga wanka har wani iska naji Yana Kara Shigana. Mahfuz na san shinkafa da wake da salad hakane yasa na dafa shinkafa da wake na hada masa zobo sai da na gama na koma d'akina Ina duba kayan da Zan saka yau nayi Masa kwalliya yasan har yanzu da saurana ciki ne kawai yasa bana kwalliya duk kayana sun min kad'an dak'yar na samu wani kamfala da nayi wa dinkin bubu mai kalar dorawa da bak'i ya shigeni ya kuwa min kyau dan na cika kayan bansa breziya ba dan mahfuz bai fiye San na saka breziya ba, Hoda da Jan baki na shafa Nima kaina nasan nayi kyau na mulka jikina da turare na fito daga d'akin na koma Palo na zauna. Wayata na dauko na kira shi a waya Yana fara ringing ya dauka na sauke ajiyar zuciya da naji muryarsa "Matata ta kaina kin sauko kenan"? "Hmm dama ni ba fushi nayi ba kishin mijina kawai nake aka nuna nayi laifi" "Mijinki nakine ke kadai bai Kamata ki dagawa kanki hankali ba" "Tom mijina ya Kamata ka dawo yanzu matarka nasan ganinka" "Mai Kika ajiyemin"? "Kaima kasani" nace Ina sakin murmushi kamar Ina gabansa Murmushi yayi yace gashi nan ya kashe wayarsa yana kashe wayar Kiran Hadeeza na shigowa wayarsa. Bayaso ya d'auka tace Masa yazo tunda har ya samu lubna ta sauko da kanta Kamata yayi shima ya faranta Mata. Kashe wayarsa yayi gabad'aya dan yasan Kira zatayi tayi Ana kiraye kirayen sallah magriba naji tsayuwar machine d'in mahfuz ido na zubawa kofar har ya shigo idonsa kyam a kaina Nima idon na zuba Masa ina dan sakin murmushi dan har dan sakin baki yayi nasan mai hakan ke nufi "Iyye wai duk wanan kwalliyar ni akayiwa Kinga yanda kikayi kyau kuwa aikuwa ya Kamata na biya kudin kwalliyar nan daga haka ya nufo wajen da nake baiyi wata wata ba ya daukeni dak'yar Yana nishin nayi nauyi Nasan Mai yake nufi ce Masa nake ya bari muyi sallah fir yak'i har sai da muka samu nutsuwa da juna na gamsu da mahfuz nawane ni kadai ba wata Yar iska da ta Isa ta rabani dashi sannu a hankali zan rabashi da wata SR. Tare muka yi wanka muka yi sallah mu kaci abinci tamkar

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26