Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Abar So Book One Complete Hausa Novel 1,186 words 0 views Progress saved
Download Book

iyayen yafi kowa sonshi tin shariff bai ganewa har yazo yagane . Lokacin da suka tafi kasar waje karo ilimi alokacin neh gobara tacinye gidansu bb Wanda ya tsiradaga Wanda suke ciki aka suka kone kurmus. Lokacinda mutuwan iyayen ya riske su bakaramin tashin hankali suka shiga bah , Sun girgiza da mutuwan Amma bb yadda suka iya tunda Allah yafisu sonsu a haka suka yi yakana. Akwana atashi sai gashi Allah yayi Sun gama school inda suka karanci course daya wato Business Admin Suna dawowa aka raba gado inda Isah yadinga almubaxaranci Danashi kason Kuma yayi aure . Shi kuwa shariff yahada hannun jari dawani company a China *Two years later*......... Kullum arzikin shariff bunkasa yakeyi Shi Isah yana neman aiki cos yaga yanashirin talaucewa matarshi Hauwa mutumiyar kirki kullum cikin yimai wa'azi take mai cos talura da irin kiyayyar da mijin ta kemawa Dan uwanshi. Alokacin kuwa sunada yarsu Fatima dakuma sabon ciki . Lokacin da HAUWA taga talaucin yakusan musu kamun kazar kuku ,saitabada shawarar yaje wajen Shariff tunda yanada shi ,aikuwa anan yake gwada mata babu abinda zaisa shi neman taimako awajen kaninshi ,babu yadda ta iya ,haka tabarshi. Lokacin na tafiya arzikin shariff kara bunkasa yaketayi ,yanxu Kuma Shirin aure yakeyi , sai wata mumunar labari yariske shi wai Fatima da kannuwata (kasancewan mamansu takara haifan wata maiSuna Maryam )Suna wasa da candle bisa ganganci wutaya diga a curtain, ahankali yake kamawada wuta ,dakyar aka samu aka fitardasu daga cikin gida ,ko kwandala ba'a fitar daga cikin gidan bah kasansewan night neh . Daman ISAH Kuma da certificate yake takama gashi yanxu ya kone,dolenshi ya amsa tayin matarshi nazuwa wajen Shariff, batareda bata lokaci bah Shariff yabashi kyautar Wani katon gida daga cikin gidajenshi na anguwar GIDA DUBU ,dakuma babbar shago wanda shida kanshi yake supplying dinkayan shop din kasancewan ISAH baxaiya aikin office bah . Aganin Shariff kiyayyar da Isah yakemai zai rabu . Shariff yayi aurenshi inda lokacinda yatafi India ya hadu dah CHANDRAMUKHI soyayya mai tsabta yashiga tsakanin su . Chandra ita kadai iyayenta suka Haifa Kuma talakawa neh sosai amma dukda hakan suna samun na daily bread . Iyayen sunyi iya kokarinsu naganin Chandra bata auri Shariff bah amman hakan ya gagara cos Chandra cemusu tayi in basu barta ta auri Wanda takeso bah she will elope with him ,babu yadda suka iya aka suka barta. Anyi aure da wata daya ,Chandra ta musulunta inda tazabi Suna NARGIS cos a India ta musulunta Kuma wai sunan kakanta nawajen amminta neh .NANU (kaka) taji Dadi sosai inda Kuma iyayenta suka yi fushi da ita, dakyar dai suka sauko kasancewan bakin alkalami ya riga ya bushe. Aurensu da wata biyu suka koma Nigeria sunyi kukan rabuwa barinma Nargis da amminta ,dakyar dai suka hakura inda shikuma yamusu alkawarin zasu nah zuwa lokaci zuwa lokaci. Gidan yayanshi yafara sauka donya gabatarda matarshi ga yayanshi , gigicewa neh kawai Isah baiyi bah sanda yakalle irin kyan Nargis atake kuwa yakara tsananta tsanan dayamawa kaninshi Kuma ya kudurta Wani aniya akansu. Sun tare awani big mansion nagani nafada a G.R.A cikin garin Bauchi. Kwanci tashi babu wiya inda na Hango Nargis da bukekiyar ciki wanda haihuwa yau ko gobe. Cikin dare Nargis tafara naquda inda Shariff ya garzaya da ita NI'IMA Consultant Hospital . Bata Dade dafara naquda bah Allah ya sauke ta lafiya inda ta haife yarinya dagabaya kuma aka gane ba ita kadai bace ,after one hour takara haifo wata ,kuma a haihuwan nabiyun neh tasha wahala. Yanbiyun ta kyawawan gaske kasancewan Nargis mah ba'a baya bah wajen kyau. Ranar Suna yanbiyu sukaci suna HASANA ( NAFHIRA) dakuma HUSAINA(NADHIRA), alokacin Kuma ya'ya Isah wato Fatima da maryam Sun girme su .Daganan Kuma haihuwa yatsayawa Nargis sbd mahaifan ta bashida kwari. *12years later*....... Abubuwa dayawa sunfaru ciki kuwa shine alfarmanda Nargis (momma)taroki mijinta daya Kara aure ,soboda yanda ta lura mijinta (dady)Mai son ya'ya ,dakyar da sudin goshi ya yarda, inda Kuma yace tanema Mai Mata cos Shi babu wanda yake SO batayi kasa a guiwa bah tazaba mai yar ajikinta maiSuna Amatullah . SU Amatullah talakawane sosai ,lokacin da aka mata maganar auren mijin uwar gidanta taso taki ,saida aka hada da roko kafin ta amince dayake Kuma tana mugun ganin mutuncin Momma. Aisha irin mutanen nan neh masu saukin kai ,nutsuwa dakuma rike addini ,ita ta raini NAFHI da ABAR SO tana mugun son yaran Kuma suma Suna son ta ,acikin halayen Momma da antynsu babu wanda basu dauko bah . Anyi aure lafiya inda bayan yan watanni ciki yabayyana ajikinta ,murna awajen familyn ba'a magana alokacin neh suka jeh kasa mai tsarki sauke farilla dukda bawannan bane zuwansu nafarko bah Kuma alokacin suka hadu dah Amin. Sun dawo da wata daya aka nemi dadynsu aka rasa , sunyi kuka harsun godewa Allah ,bayan yan watanni antynsu ta haife baby boy inda yaci sunan Salim wanda daman kafin bacewar dadynsu yace sunan yake SO. Nafhi (haka akecemata) da Nadhira ( ABAR SO KOKUMA BABY,haka sukecemata ) sunje gari ruka da dama Wanda ba'acikin Nigeria bah. NAFHI tafi ABAR SO hakuri nesa ba kusa bah while ita ABAR SO tanada saurin fushi ga shegen zuciya Kuma duk sunada ilimi sosai ,babu abinda basu iya bah . *2 years later*. ....... Cikin shekaru biyun da sukawuce anyi zaman Dadi dakuma bah Dadi a familyn. Saikuma labari tariskesu wai ansamu gawan dadynsu,basu yarda da abinda aka fada bah sanda aka kawo gawar dadynsu nan kuwa tashin hankali yadawo Sabuwa a familyn . Sun fito takaba kenan wata Sabuwa alamari ya bullo wai dadynsu yayi signing din duk will nashi wa yayanshi Isah wannan batu ya girgiza su ainun ace wai duk propertyn su basuda kaso aciki sai gidan da suke zaune ,ai atake jini......... πŸ’‹πŸ’‹ wurarh πŸ’‹πŸ’‹ πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *ABAR SO* πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ WRITTEN BY:NAFISAT MA'ARUF SHEHU πŸ’‹πŸ’‹ WURARHπŸ’‹πŸ’‹ 🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟 🌟G.W.F🌟 HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST Page 40-42 Jini yafara fitowa antynsu ta baki Sakamakon tarinda ya caske tah,rushing nata sukayi zuwa nearest hospital domin ceto ranta ,kuka kam awajensu ba'a magana. Suna isa hospital din aka wuce da antyn emergency, bayan minti talatin aka fito da antyn zuwa resting room sannan doctor yamusu bayani akan cewa heart nata neh yaso bugawa ,Sun tsorata sosai dajin bayanin doctorn. Sannan yakara dacewan mutum dayaneh xata kwana daita . Dakyar suka bari NADHIRA tazauna cos bb Wanda yakeson barin antyn ai kuwa Salim cewa yayi baisan zancen bah haka suka barshi cos bb yanda suka iya cos yaron akwai naci.Bayan sun tafine suka lura ko flask basu xoh dashi bah ,haka NADHIRA tanace saita dauko ........ Suna isa gida suka samu babu Baba gateman akofar gidan ,akadai suka garzaya cikin gidan cikeda rashin damuwa Kuma yayi daidai da isowar Nadhira kofar gidan . Abinda suka tarar cikin gidan neh yasasu mutuwar tsaye, wato wasu mutane neh suka gani wanda daga yanayin faces nasu mutum xaigane basu da imani sai Kuma guda daya Wanda yake da face mask ,itakuma Nadhira lokacin take karasowa cikin sanyin tafiyanta kawai saitayi Gamdatakar da abinda ya tsoratata ,aikuwa atake tafasa Wani ihun daya sa su Momma farfadowa daga suman tsayen dasukayi,itakuwa bata Hankara bah taji

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27