Chapter 23
Chapter 23
yanda kace haka za'ayi" "Toh InshaAllah ranar da za'ayi nasu Abdulkadir Sai ahada danasu, Sai afara shirye shirye" Dady yafada… Wani irin farinciki yakeji acikin ranshi cos tindazu a labe yake ajikin kofa yanajin abinda suke fadi… *********** *3 days later…* Yen kwanaki ukun datayi acikin gidan ta kara Lura da abubuwa dayawa acikin gidan,daita ake kowani abinci agidan yanz u inda kuma yanzu Maimuna ce target dinta dan haka yau tayi niyyar fara aiwatar da kudurinta akan Maimuna din. Maimuna mah bata fasa bibiyarta bah cos itama kowani motsin Nadhira akan idonta yake amma har yanzu bata samo komai gameda ita bah, Data fadawa Big Dady Sai yace kawai su shareta , yanxu dai zance Maimuna ta share batun sawa Nadhira ido… Tindazu take kitchen tana taya Maimuna aiyuka inda Maimuna ta Lura Maimuna ta fiye shan coke,abu kadan Sai adan kurbi coke dinnan, Fakan idon Maimuna tayi tazuba mata codeine acikin coke dinta ,inda tsantsan mugunta irin na Nadhira babban kwalba tazuba mata aciki, su Maimuna kam banda waka babu abinda takeyi, kuma dayake tabawa coke din baya amma tsantsan rashin Kula irin na Maimuna ko jijigawan datake yi bata ji bah, "Nikam Maimuna wannan coke din daya rage dinnan zaki iya shan duka alokaci daya"Nadhira tafada tana nuna coke dinda ko rabi bai kawo bah, Sanda Maimuna tayi wani irin dariya kafin tace" ke bakisan nayi course a iya shan coke bah??" "Toh taya za'ayi nasani inba gwada min kikayi bah??" "Tsaya kisha mamaki" Maimuna tafada tana kafa goran abakin ta , tsantsan hadama ko irin kwarewan nan batayi bah,gyatsan da Maimuna tayi bayan ta ajiye gora neh ya katse mata mamakin ta. "Ya Kika gani??"tafada tana dage mata gira Dariyan jin dadi Nadhira tayi sannan tace " wlhy nadauka bazaki iya bah, barina dauko miki nawa kisake sha mugani" Dadi kaman ya kashe Maimuna cos daman kullum guda biyu take sha arana amma gashi yau garabasa tasamu zatasha guda 3, Fita Nadhira tayi straight dakinta ta nufa sanda taboye kwalban codeine dinda ta juye mata dafarko abayan gado sannan tasake fitowa dawani again sanda tadan zubar da kadan kafin tasake zubawa aciki(nace kaii Nadhira ke muguwar karshe ceh…) sanda Tajijiga dakyau sannan tayi takoma wajen uwar kwadayi "Gashi harna bude miki"tafada tareda mika mata,karba tayi sannan tace "Kin kyauta wlhy" aranta kuwa fadi take ashe Nadhira akwai mutunci(nace Maimuna kenan hhh), Kafa goran tayi abaki amma ko rabi batayi bah tafara ganin Zion,wani irin zumm zumm take jin kanta na mata, Ajiye goran tayi tafara ganin Nadhira shida shida, dagudu Nadhira tashige dakinta takwaso kwalaben codeine taje tazube su acikin sif din Maimuna, Lokacin datakoma kitchen din ta tarar da Maimuna cikin maye,cikin muryan Masha ya tace "Miye Kika samin a coke??dayake bata gama loosing sense dinta bah Dariya mara sauti Nadhira tayi sannan tace" duk abinda naga zai zamemin matsala a harkan dana sa agaba toh lah shakka kawar dashi daga hanya nakeyi" Wani irin sarawan da kanta yayi yasata sakin wani irin dariya amadadin kuka, Jin dariyar da akeyi yayi yawa yasa mumy dakuma su Fatima saukowa daga sama cikin sauri,hanyan kitchen din da suke jin dariya suka nufa, Turus sukaja suka tsaya SAKAMAKOn ganin Maimuna akasa,itakuwa Nadhira takurewa tayi jikin garu,tana ganin mumy tayi wajen ta gudu sannan tace "Mumy bansan miye ke damunta Sai fadin maganganu maras a dadi takeyi akan itada big dady" "Wlhy son Alhaji nakeyi irin sosai dinnan…"suka tsinkayo muryan ta tana fada,tana tashi tayi tana layi … Mumy kam notin kanta taji yana neman kwancewa cikin dauriya mumy tace "Wani Alhajin kikeso??" Wani irin dariya tayi sannan tace "wani Alhajin kuwa baya… *Comment,* *Vote&* *Share* *💋💋 wurarh💋💋* 💝💝💝💝💝 *ABAR SO* 💝💝💝💝💝 *WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU* WATTPAD: MHIZZPHYDO 🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟 🌟G.W.F🌟 HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST *Page 96* Wani irin dariya tayi sannan tace "wani Alhajin kuwa bayan mijinki?,wlhy Ina mugun son sh...." Marin da mummy takife ta dashi neh ya katse ta, cikin bacin rai mumy tace "Abinda zaki saka min dashi kenan Maimuna??" Wani dariya tayi dukda marin mumy bakaramin shigan ta yayi bah sai tace"toh an fada miki don ke kadai akayi shi neh?, Kindai San yana da damar yakara auren ire irenki guda 3, toh miye abin daga hankali anan? Kuma bari Kiji har kwana dani yakeyi" Haba kan kace kabo su mumy harsun sun mata taron dangi, mumy sai cewa take wlhy yarinya karya kikeyi, mijina babu abinda zaiyi dake(Niko nace daga baya kenan). Dukan ta sukeyi kaman ba gobe har sanda sukaga tadaina motsi sannan suka kyaleta,sheka mata ruwa akayi amma ko gizau Maimuna batayi bah "Kun kasheta!!!,kunyi kisa" shine abinda Nadhira ke fadi afirgice cos tinda suka fara dukanta taja gefe ta tsaya. "Suma tayi" Fatima tafada in assuring tune, "Bagashi ankwara mata ruwa bata tashi bah" Nadhira takara fada tana mai tsugunawa akasa. Kanta tasa atsakiyar cinyarta tasaki kuka mara sauti,she can't imagine yanzu ace ita tayi sanadin barin Maimuna duniya. "Yah Salam"shine abinda mumy tafada sannan tace "Ku kamata mukaita asibiti" mumy tafada cikin sanyin murya cos gabadaya tsoro neh yadarsu acikin ranta. Cicibarta sukayi suka sata amota Sai asibiti,suna isa asibiti aka karbe ta aka wuce daita direct emergency. Ansamu numfashinta yadawo amma gabadaya bata cikin hanyacinta, doctor ne yasa aka Kira mai wa'inda suka kawo ta… "Miye kuke kallon yarku tayi shaye shayen dayasa ta bugu dayawa?" Doctor ya gefawa mumy tambaya "Yar aiki nace" mumy tabada amsa atakaice "Yar aiki kuma??"yatambaya cikin mamaki "Erh" "Toh aina tasamu cocaine??" "Cocaine" dukkansu suka fada cikin tsoro amma banda Nadhira "Erh acikin aman datayi munsamu ashe tahada mixture biyu alokaci daya Wato da cocaine dakuma codeine which is not proper,gashi kuma dayawa tasha shiyasa condition dinta yazamo critical, ahalin yanxu kam Allah yasoku da akwai wani visiting doctor available dole shi zamu gayyato" Kallon kallo akeyi acikin office din wajen cikeda jimami kafin suka tashi suka fita. Wayar big dady mumy takira inda ta shaida mai halin da ake ciki. Banda salati babu abinda big dady keyi, inda ya ce mata su hadu agida. Komawa gida sukayi suna jiran big dady yadawo, chan saigashi da uwarsu babban riga, hula ma ahannu yariko Sai huci yakeyi kaman wani namijin zaki. Shigowar shi yasa dukkansu suka tashi tsaye Cikin bacin rai yake fadin" ina yar iskan yarinyar nan take??" "Bata farfado bah" mumy tabashi amsa "Yarinyar nan taci mutunci na dayawa harni zata mawa sharri don batasan hallaci bah??"Alhaji yafada cikin dacin rai kaman da gaske, Nadhira kam babu abinda take yi Sai binsu da ido "Nima abin yabani mamaki,ai tanuna mana halinta kuma daga yau aikinta yakare agidanan" mumy tafada "Abinda yasha minkai shine ina tasamo cocaine??"dady yafada "Allah masani" "Gaskiya ban yarda bah??"big dady yafada "Toh aje a bincika dakinta mana I'm sure zamu samu wasu clue" Fatima tafada "Kin kawo point sisto"daga nan suka dunguma zuwa dakinta, birkita koina sukeyi daga karshe suka samu kwalaben codeine manya manya guda biyu. Salati suka hau yi sam basu taba kawowa aransu Maimuna zata iya shaye shaye bah cos ta fiye shuru shuru, ayyerh daman ance duk masu shuru shurun nan basuda dadi. "Taya akayi tasamu cocaine??" Shine abinda Amin Yafada bayan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27