Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Abar So Book One Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

agaban mirror acikin daki banda murmushi babu abinda yake fitowa daga Samar labbanta. Daman tin randa taje tasiyi Condom ta lura wasu na binta amma dayake shu'umace saitayi kaman bata gansu bah. Abin mamaki kuma saitaga abokin Amin neh yashiga nan tasan tareda Amin sukazo kuma sawunta suka biyo. Washe gari takoma chemist din tareda tambayansu wanda yazo immediately lokacin da tafita ,basu tsaya bata lokaci bah suka zayyana mata abinda ya tambaya dayake bakin su baida rufi. Nan tamusu godiya tareda ficewa, tana komawa gida tadinga sakawa da warware akan yanda zatayi da Amin cos tasan yanzu yadaura Ayar shakku akanta kuma mai yiyuwa mah yafara zarginta. Daman tinda taga doctors sunyi confirming substance din Cocaine acikin abin da tasha tasan dole Sai anzo yin bincike shiyasa tinda wuri tasan inda dare yamata. Amma agarin kwashewa Sai akayi rashin sa'a Condom yafadi,amma batasan takamen men abinda yafadi bah irin bari tagama saita dauka Sai Allah yasa tamanta shi awajen. Sai alokacin da akace za'a duba dakinta ta tina ashe bata dauki abinda ya fadi bah shiyasa tsoro ya shigata. Tana ganin Condom neh ranta yayi fari fatt tsantsan murna cos tasan in akan Condom neh zata iya kare kanta... Numfawa tayi tareda sakin wani murmushi tinawa datayi yanda tayi da cocaine. Jan drawern jikin dressing mirror din tayi tareda daukan hands glove sannan ta tashi, dayake dare neh kuma anriga da an rufe kofa kuma tana kyautata zaton kowa yayi bacci. Ahankali tayi jikin window tayaye labule, sliding glass din tahau cirewa ahankali gudun karyayi kara. Tana gama cirewa tasauke ajiyar zuciya mai karfi, zura kafafun ta tayi sannan ta dira ahankali. Wajen bolan gidan tanufa sannan ta sanya gloves din ahannunta, sanda ta daddaga wasu abubuwa kafin tazura hannunta chan kasa. Torch din wayan ta tukunna daidai tafito da wani bakin leda. Tsince leathern farko tayi wanda yariga da yayi datti sannan ta yasar kafin tabar wajen cikin tsantsan murna...(nace master planner bah...) *Vote,comment&share* *Mhizzphydo* πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *ABAR SO* πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU* WATTPAD: MHIZZPHYDO 🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟 🌟G.W.F🌟 HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST *Page 98* Tsince leathern farko tayi wanda yariga da yayi datti sannan ta yasar kafin tabar wajen cikin tsantsan murna...(nace master planner bah...). Straight kitchen tanufa sannan ta dauko container din gishiri tazazzage gishiri acikin buhun gishirin cikin store kafin ta zuba cocaine din acikin container din. Ajiyar zuciya tasauke sannan tasake wannan murmushin muguntan ta kafin ta koma dakinta... Washe gari ita tafara tashi tashiga kitchen ta dafa musu lafiya yiyar breakfast. Kafin su fito ma har tagama komai ta feso wankan ta as usual cikin short gown yau kam ko dankwali batasa bah. Ta zauna da 10mins yen gidan suka fara fitowa, sosai suka sha mamakin ganin abinci asamar dining table. "Babynmu kece kika bawa kanki wahala haka??"mumy tafada cikin farinciki cos Nadhira bakaramin burge ta tayi bah "Ai bawani wahala bane" tafada cikin sune kai kaman da gasket "Madalla Allah ya biya" "Ameen mumy" Tashi tayi tareda karasawa wajen dining table din cos su kam har sun zauna sun fara serving Kansu. Lura datayi Nadhira batacin abinci yasa mumy cewan" ya naga baki cin abinci" "Inajiran Big dady tinda naga baku jira shi bah" Tafada cikin murmushin daya zame mata jiki "Kin kyauta Babynmu "suka ji muryan Big dady daga bayansu. Tashi tayi taje ta taroshi tareda mai Ina kwana amsawa yayi cikin Jin dadi tareda kawar da duka zargin dayake mata acikin zuciyarshi. Zaunar dashi tayi tareda serving dinshi nashi abincin, lokacin har su Fatima sun gama cin abinci. Gaishe shi sukayi sannan ya amsa cos in suna cin abinci ya hana su magana tashi sukayi suka bar wajen... "In hado maka coffee neh??"tayi requesting "Gyada mata kai yayi tareda sakar mata murmushi Itama murmushin tamiyar mishi tareda wucewa kitchen. Tea cup tadauko tareda fara zuba cocaine din akasa sannan tasa garin coffee din. Ruwan zafi tadauko ta sheka akai sannan ta dauka spoon ta gauraya su hasaida aka daina ganin garin cocaine din sannan ta fice. Ta kaiwa ta dauki cube din sugar sannan tasa aciki.. "Allah yamiki Albarka" dady yafada cikin mouthful "Ameen" tafada tareda Zama akan kujera tukun tayi serving din kanta mah. Ganin yakai cup din bakinshi neh yasata cikin boyayyen murmushi... Dayake baiyi changing taste bah shiyasa Big dady bai fahimce komai bah. Tass ya shanye coffee din harda gyatsa. Ya na mikewa itama ta Mike dayake tagama cos bata cin abinci dayawa. Car key dinshi ya dauka sannan ya mawa mumy magana wacce taje shirin zuwa asibiti. Chan saigata ta sauko daga sama cikin takunta na matan attajirai... Da murmushi ta tareta itama tareda taka musu zuwa waje "Ke bazaki zoh dubiyan bane??"mumy ta tambaye ta cikin kulawa. Murmushi tasake sannan tace" ni bana zuwa dubiya hannu zalla ma'ana so nake na hada koda kunu neh in case inta tashi tasamu abin sawa abaki" Sosai suka sha mamaki cos ko kadan wannan tunanin baizo musu bah. "Madalla Babynmu Allah ya biya ki in kin tashi tahowa driver yakawo ki" dady yafada. Toh tafada still akwai wannan murmushin afuskarta, bye bye tayi musu sannan ta shige cikin gida. Straight kitchen takara nufa agagauce ta daura ruwan akan gas tareda kara sa cocaine acikin ruwan.. Sharp sharp tagama hada kunun sannan ta juye acikin flask.. Dakinta tawuce ta Kira wani number,dagawa akayi daga dayan bangaren akace "Ranki shi dade baki da sauki fah" yafada cikin muryanshi irin na mashaya Wata karamar tsaki taja sannan tace"ya ake ciki??" "Gaskiya aikan ki yanzu ya kara kudi soboda da kyar ake samu amma dai Alhmdllh ansama miki " "Nawa neh ??"ta tambaya atakaice "Dubu goma zaki ciko" "Toh inason mu hadu nan da minti 10 zan taho maka da cikon kudin" "Toh Hajiya muhadu a inda kika ce zamu hadu??" Sanda tayi Jim sannan tace "tsari ya chanza" "Toh yanzu miye tsarin" yatambayeta "Akwai wani mai shago a anguwan danake ta bakin titi, inkaje saika bashi kace za'a zo akarba nikuma kafin ka karaso zan bashi aika ya ajiye maka, yanajin kace aika kazo karba zai baka kudin amma kayi wrapping dinshi yanda babu wanda zai gane wani Abu neh aciki" tana gama magana ta katse kiran tareda deleting din numbern" Dariya yayi yana jinjina irin kwakwalwar Hajiyan( bai taba ganinta bah daman) afili yace"komin kwakwalwar ki yau kam saina san wace ce ke" Tana ajiye wayar tasauke wata ajiyar zuciya kafin tabar cikin dakin da leather a hannunta. Waje tafita dashi sannan ta gaisar da baba mai gadi. Yana ganinta yafara wangale baki musamman mah daya hangota da leather. "Wa'inan yaran fah??"ta tambaye shi "Ai basu nan amma sun kusa dawowa daga makaranta" "Ohk in sun dawo amin magana" tafada tareda juyawa" Yace"toh" yana mai yin adduan Allah yabashi y'a kaman ta. '''5mins later...''' Fitowa tayi amma yanzu leathers biyu neh a hannunta. Yaran suna ganinta suka fara murna cos sosai suke sonta. Wanda tasan tana da nutsuwa kuma wanda bata fiye magana bah takira acikin su sannan ta jata gefe daya. Bata leather daya tayi sannan tace "ki kaiwa mai shagon bakin hanyan nan,kina bashi kice za'a zo akarba sannan kijuyo" Gyada kai yarinyar tayi sannan ta wuce

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27