Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Abar So Book One Complete Hausa Novel 1,226 words 0 views Progress saved
Download Book

wajen mai shago din. Kaman yanda tace haka yarinyar tayi, tana dawowa tabawa yarinyar nata alawan cos daman kullum saita raba musu shi sadaka '''5mins later...''' Hango wani huge guy nayi wanda kallo daya xaka mai kagane bashida mutunci shagon ya shiga tareda bashi aikan sannan aka bashi kudin. "Waye neh yakawo kudin??"ya tambaye mai shago Mai shago kuwa ganin babu rahama afuskarshi yasa shi fada mishi wata ce ta kawo, "Ya take??" Nan kuwa ya zayyana mai kallan kayan yarinyar dayake akwai niqab afuskarta(daga islamiya suka taso amma babu uniform ajikinta) Gyada kai yayi tareda ficewa daga shagon, yaje ya zauna a inuwa yana jiran dawowarta. Hango shi tayi tacikin mota awajen inuwa,wata murmushi tasake ganin zaton ta yazama gaskiya. Sanda suka danyi nisa tace mai ya tsaya sannan tace"in bazaka damu bah aika zaka karbo min??" "Haba miye kuma abin damuwa anan,kifadi komiye ni mai iya miki neh"yafada cikin sanyin murya Murmushi tasake akaro na biyu sannan tace "shagon bakin titi dinnan zakaje kasiyo min flour mudu 5, sai kaga yafara auna flour din ma'ana in yajuya baya saika dan duba min karamin leathern da aka mai kyakyawan package. Wannan leathern zaka dauko amma fah karka bari yagani. Ga wannan saika ijiye shi awajen da kadauki leathern" Yace toh tareda karban kudi da wata farar envelope daga hannun ta. Fita yayi daga cikin motan tareda wucewa shagon ,kaman yanda tace haka yayi ,yana karba ya faki idon mai shago sannan ya tusa leathern acikin flour din kafin yafito. Yana komawa ya Mika mata leathern flour din karba tayi tareda ajiye wa cos batason ya bata mata hannunta. "Wajen matan ka zaka fara kaini kafin muwuce asibiti din"tafada mai "Toh"amsa tareda nufar daita anguwan Mahaukata(karku ce fah Mahaukata neh a anguwan a'a sunan anguwa neh kawai) Anguwan talakawa neh sosai wanda kowa harkan gabanshi yakeyi ga yen talla sai fitowa sukeyi yasu wajen cin kasuwan su. Adaidai wani gida mai labulen buhu yayi parking itama fitowa tayi tana jinjina ma masu Zama a anguwan. Iso yamata zuwa cikin gidan inda ya tayata rike leathers din flour din samun matarshi sukayi inda take cilla dan wake acikin ruwa. Gaisheta takeyi amma abin mamaki Maimakon matar ta miyarda hankalin ta kan bakuwa sai takara miyarwa kan danwaken ta. Duban agogon hannunta takeyi inda yanzu taci minti uku azaune cos tintini driver yafita. Gyaran muryan da tayi neh yasa matar Dan juyowa"gashi ni natafi"tafada tana tashi tsaye Cikin dan Jin kunyan abinda tayi matan tashi tsaye tareda gaishar da Nadhira. "Gashi akwai wani leather acikin wannan kidan cire min sai ki karkada min flourn jiki"tafada cikin nutsuwa Cikin rawan jiki matan tasa hannu ta cire sannan ta karkada harda gogewa da zanin jikinta. Karba tayi sannan tace"ni natafi sai watarana in Allah yayi zamu sake haduwa tinda na Lura kinfi bawa kasuwan cin ki muhimanci fiye da mutane" tana gama fadin hakan tayi gaba tareda boye leathern acikin side bag dinta. Sosai matar driver taji kunyan abinda ta aikata cikin sanyin jiki takarasa gurin tukunyan sana'arta... Suna Isa asibiti tabar side bag nata acikin jaka sannan tafito da flask din kunu. Shiganta dakin yayi daidai da farfadowan Maimuna kuma alokacin akwai doctors aciki, ciki kuwa harda Amin. Gaishe su tayi cikin sanyin murya sannan ta karasa wajen gadon Maimuna din. "Ya jikin ki??" Tafada a hankali,itakuwa Maimuna banda binta da ido babu abinda takeyi. In akwai liquid abinci abata soboda taji karfin jikin ta"Amin yafada Mumy neh ta dauki flask din tareda zuba kunun ciki acikin cup. Nadhira neh dakanta ta sawa Maimuna cup din abaki, ita kuma banda kallon Nadhira din babu abinda takeyi. So take tayi magana amma saitaji kaman an rike mata makogaron ta. No tausayi haka Nadhira tabata kunun nan Tass... '''3hours later...''' Fita tayi don komawa gida soboda babu kowa, drivern neh dakanshi ya bude mata kofan motan. Da murmushi tace "ai da baka wahalar da kanka bah" "Girman ki neh" yafada shima... Daidai gurin mai shagon takara ganin shi wata murmushi tasake sakewa dayake motan tinted ni shiyasa ba wanda yaganta. Suna Isa gida tawuce daki, numbern shi tasaka awayan tareda danna mai Kira... Ganin mai kiranshi yasa shi saurin dauka(private number)... Dariyan dayaji anyi neh yasashi kallon fuskar wayan cos ko murmushi bayajin tayi in har takira. Cikin nutsuwa tace... *Vote,comment&share* *Mhizzphydo* πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *ABAR SO* πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU* WATTPAD: MHIZZPHYDO 🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟 🌟G.W.F🌟 HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST *Page 99* Cikin nutsuwa tace " I thought you're a smart guy but unfortunately you're not, You thought zaka iya min wayo koh??"Wani dariya takarayi tace" I trust no one in fact I don't even trust myself cos tunani nah na iya chanza wa akowani lokaci so.... Katse ta yayi fadin"miye faru neh ranki shi dade??" Dariya takuma yi tace" all pretence aside, daman shawara zan baka" Sanda yayi Jim yana dan juyawa ko taganshi neh amma baiga alaman ana kallon shi bah. "Miye sa kakeson sanin waye ni??" Tambaye shi batareda tajira cewar shi taci gaba" nagane sokake in polisawa suke kama ka kafito dani koh?? Dariyan rainin hankalin yayi yace"kina tunanin in suka kamani bazan binciko ki bane??" "Toh ka sani ni nan inuwa ce baza'a iya kamani bah ko ka taba jin inda aka kama inuwa neh??" "Kaman dagaske yafada in amusement, bayan zaki fito daukan aikan ki??" "Aika?? Nawa yaushe kenan fah??" "Nadazu mana" "Kama daina bata lokacin fah soboda nariga dana dauki kayana!!" A saba'in yamike daga inda yake yace"wannan mah karya neh" Dariya tayi tace" go and check nabar maka aika awajen mah" Baijira cewar ta bah ya katse wayar tareda nufar shagon, ko sallama babu yace"ina abinda nakawo dazu??" Duba inda ya ajiye yayi yakalli farar takarda instead of bakin leather. Hannu na rawa ya dauki takardan tareda warwarewa wata kyakyawan rubutu neh ya bayyana(irin na 3sweet besties dinaπŸ’‹πŸ’‹) "FOOL!!!" Harya cakumo wuyar rigan mai shago kawai sai wayan sa ya dau kara dasauri yasake shi hade da picking din wayan. "Karka mawa mai shagon komai cos shima baisan lokacin da aka dauka bah" "Ke waye ceh??" "Someone who is seeking for revenge on the death of her mom and sister!!!" Tana gama fadin hakan ta Kaste wayan. "Hello! Hello!! Hello!!!" Ganin batayi magana bane yasashi duba screen din wayan "Holy shit" yafada tareda nausar gini sannan yasa kai ya fice... Zama tayi agefen gado ta bude ledar ganin abinda yake ciki yasata fashewa da kuka mai tsuma zuciya, sanda tayi mai isarta sannan ta share hawayen ta tareda shigawa toilet domin yin wanka. Tana gama wanka tashige kitchen domin dafa musu abincin rana soboda 1 tayi.. Tana cikin hadan abinci mumy tadawo.. "Sannu da dawowa mumy" "Sannu da aciki Babynmu" "Ina big dady yake" "Wai zai shiga ganin likitanshi cos baidan jin dadin jikinshi" Wani irin faduwa gaban ta yayi amma ta waske tace"shine bakuje ganin likitan tareda shi bah??" "Ai banma san kin fara abinci bah cos shi nazo dafawa". "Ohk, ya jikin Maimuna din??" "Hmm, jikinta sai sake rikicewa yakeyi gabadaya tafice hanyacin ta" mumy tafada cikeda jimami "Ayyerh Allah yabata lafiya" "Ameen" mumy tafada tareda ficewa Ajiyar zuciya tasauke sannan tayi wannan dariyan muguntan

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27