Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Abar So Book One Complete Hausa Novel 1,184 words 0 views Progress saved
Download Book

tafada lokacinda take bata juice baaket din "Antymu yanxu korata kikeyi koh?, kenan harkin gaji da ganina koh, babu damuwa" tafada hade da ficewa azuciye . "Babynmu wlhy kitsaya bakorar ki nakeyi bah" antyn tafada tana mai bin bayanta , itakam ko sauraron antyn batayi bah tatari keke napeep, shikuma Amin ganin ta tare napeep yasashi komawa cikin gidan dasauri domin dauko car key dinshi, haka yagama duba gurinda ya dan zauna amma babu key babu alamunshi , zuwa lokacin kuma yasan sunyi nisa, sai asannan yatina ashe key din na kan car dinshi yamanta......(lol.....πŸ˜†) "Yanzu yazamuyi" Hasana ta tambaye antyn cikeda damuwa "Karki damu daman haka take da saurin fushi ko da abin baikai ayi fushi bah. "Toh ki gwada kiran numbern ta mana" inji Amin da fada "Ai kona kira badagawa zatayi bah" Antyn tabashi amsa "Toh kiban numbern nayi trying luck" yakara fada, haka antyn ta karanto mai numbern, kira yayi amma har yatsinke batayi receiving bah, sallama yayi musu akan zai cigaba dakira , cike da damuwa yakoma gida ranar. Su antyn kuwa jigum suka zauna har Hasana takoma gida, tana isa kofar gidansu tasami Husain wajan "Ya dai twinee?" Yatambayeta "Wlhy wai Nadhira neh ta tafi cikin fushi" tabashi amsa "Miye akamata haka?"yakara tambaya......nan dai ta labarta mai abinda yafaru " kut.. Wannan wace irin zuciya ce daita , gaskiya za'asha fama"yafada "Gaskiya kam cos ko yafiya batadashi" Hasana tafada "Hmmm, ya akayi kika sani madam Hasana?"zama tayi na musamman ta bashj labarinsu wanda tasani gabadaya , wani tausayinsu yaji shima " shiyasa ai yanayinsu baiyi kamada na talakawa bah"haka dai suka dinga hira har aka tada sallah sannan Hasana tashige cikin gida. Abangaren Nadhira kuwa tinani takeyi akan abinda yasata fushi kuma bayan tayi alkawarin bazata sake bah gabadaya saiyaji bata kyauta bah. Gaishe da baba maigadi tayi sannan ta ajiye basket din akofar side dinsu kafin tashiga side dinsu mumy tana shiga tasame su harda wani bakon fuskanda bata sani bah amma kamanninshi yanuna cewan shi dan gidan neh "Sannu da gida" tagaishesu hadeda risinawa cikeda girmamawa "Saiyanxu baby" "Eh" "Yamutanen gida?, hope suna lfy" Abba yatambayeta "Alhmdllh , wai inji Antynmu tana gaishe ku" ta bada amsa "Muna amsawa" mumy tafada "Toh saida safe " tafada musu "Bazakizo muyi dinner bah?" Mumy ta tambaya "A'a wlhy cikina a koshe nake " tafada murmushi kwance akan face dinta.... "Waini mumy miye kike gayyatar wannan kazamar kan dining dinmu, ko sokike Love dina yaganta yakasa cin food neh cos kinsan ba kowace cleaner yake kulawa bah balle kuma tazauna a inda yake for the matter of fact cleanern wannan kazami gurgun !!!" Afirgice suke kallonta , kaman wata walkiya ta iso gabanta "One more bad word from you and i promise to keep you mute"Nadhira tafada cikeda bacin rai cos har jah idonta yayi "Miye kike nufinda zaki keeping dinna mute, yar yarinya ma dake yar matsiyata , doluwa mah irinki, tukunna mah wai kare wannan gurgun zakiyi don rashin hankali , wanda ko gata baida akanshi zaki nema gayamin magana tukunna mah waye ubanki a fadin Nigerian nan miye kika taka arayuwa nasan familyn ki dake suka dogara soboda ke ne mai nema musu na daily bread kuma a haka kike neman wasting opportunityn ki" "Kursum" Abba yakirata cikin kausashiyar murya "Karka kirani mijin mumy kayi shiru cos bada kai nake yi bah, ka adana duk abinda xlzai fito daga wannan mushen bakin..." Ai bata karasa bah taji saukar mari a kumatunta..........tirkash Guess waye mareta? πŸ’‹πŸ’‹wurarhπŸ’‹πŸ’‹ πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *ABAR SO* πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *WRITTEN by: NAFISAT MA'ARUF SHEHU* *πŸ’‹πŸ’‹wurarhπŸ’‹πŸ’‹* Wattpad:Nafisatma'arufshehu 🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟 🌟G.W.F🌟 HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST Page 75-76 Ai bata karasa maganan bah taji mari a kumatunta "Ke wace irin mara hankali ceh, kinfini sanin abinda wannan bawan Allahn yamiki arayuwa amma tsantsan rashin hankali irin naki kike zaginsa kuma fah dukda hakan yana suriki awajenki, wai tsaya mah tukunna harke dinnan kin isa ki zageni , kinsan wace ni kuwa, kinsan waye mah ubana kuwa, babu shakka kinsanshi bama ke kadai bah dukkanku kunsanshi , muba matsiyata bane cos daga kaina har 7th generation dinmu masu zuwa bazasu taba sanin miye talauci bah, kuma mijinki dakike ikrarin baisom kaza da kaza toh i bet you ni zan aureshi kuma kindai ganni babu namijin daya isa yayin resisting dina cos ni ABAR SO ceh!!!, babu magani babu tsafi zan siye zuciyar mijinki dukda nima inada wanda nake so amma haka zan hakura na aure mijinki, zan nuna mai tsantsan soyayyar da babu algus acikinta , sannan abinda zan gargadi ki guda daya neh kawai shine ki boye mijinki cos haduwata dashi will be the beginning of your downfall, lastly wanda kike kira da kazami gurgu shin kinada masaniya akan abinda ya mayardashi hakane?, ko kuma kina da masaniyar akan matsayinda yakedashi kafin yadawo wannan condition din?, ko kinada masaniya akan asalinshi, kokuma abinda yakeda kafin yadawo haka? ko kuma kina nufin Allah baya jarabtan bawanshi?, bakya tunanin shidin mah yanada gata kaman yadda kowa yakeda?"numfasa tayi sannan tajuya wajen wannan saurayin "Kaikuma kawani tsaya sokoko ka wangale baki hangam kaman wani maloho , shasha kawai agaban idonka wata kanwar bayanka take zagin babanka wanda inada yakinin cewan bazaka wuce 28 bah itakuma nasan babu tantama 25 amma shine bazaka dauko tsumagiya ka chachauda mata bah, wlhy you are a disgrace to manhood"tana gama fadin hakan ta fice daga palourn hartana bangaje a bakin kofa shigowa. Shikuwa dawowarshi kenan daga gidansu Nadhira , mamaki neh yakamashi jin yadda aka bangaje shi amma ko arzikin sannu baisamu bah, girgiza kai yayi hade da kutsawa ciki , abinda ya tarar neh yasashi jan birki yana dada bin gidan da kallo cos tunaninshi shine gidan wasu yashiga soboda ganin da yayi an tsatsaya while Kursum na durkushe tana kuka ga idon yakumbura , shahada yayi sannan ya matsa kusa dasu " lafiya naganku haka?, miye faru?"ya jera musu questions trying to figure out what the problem is. Mumyne tafara haurawa sama, cike da rashin nutsuwa ta mike tabi mumyn tana fadin "Wlhy bazan yadda bah , i swear to make the hell out of that small girl , tinda nake ba'a taba cimin mutunci irin na yau bah , look at my face i can feel how it got swollen" tafada daidai lokacinda tarike hannun mumy dayan hannun kuma akan cheek dinta. Mumy kam babu baki magana cos bazata taji dadin marin da aka mawa daughtern ta bah kuma bazata ceh ta ji dadin zaginda Kursum tamawa mijinta bah amma kuma yazatayi, batareda tace komai bah ta zame hannu Kursum sannan takarasa hayewa, cikin kuka Kursum tamara mata baya "My son inkagama kasameni a room dina" Abba yafada tareda barin palourn "Kai miye faru?" Amin yatambaye kaninshi "Infada maka yau ankoyawa Kursum hankali " nan dai yakwashe komai yafada mishi, shikuwa abangaren shi haka kawai yaji yarinya ta burgeshi kuma zaiso ganinta "Barinaje wajen Abba " yafada hade da barin wajen. Da sallama yashiga cikin bedroom din Abbanshi , amsawa yayi hade da nuna mai gefenshi alaman yazauna batareda ya musa bah yaneme mazauni agefen nashi "Ka kalle ikon Allah koh abinda baby tayi naji dadinshi sosai cos taburge

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27