Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

Abar So Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

sati dayan dasuka wuce abubuwa dayawa sun faru irin shakuwan da Amin da Nadhira sukayi dukda awaya neh, amma har Amin ya gayawa Nadhira sirrin azuciyar shi,itakuwa cemai tayi zatayi tunani akai...... Ga kuma Abdul yayi nisa akogin son Hasana batareda yashirya bah ,gashi kullum saiya mata 100 missed calls amma bata taba dauka bah abin sosai yake mishi ciwo,harya kaiga zuwa gidansu,anan aka fada mai tayi tafiya,daganan yanemi ganin Babanta sannan ya fadamai bukatunshi,Babanta kuwa cewa yayi idan yashirya yaturo iyayen shi,sosai Abdul yaji dadi while dayan bangaren azuciyar shi kuwa cike yake da fargaban kallan masifan da zaisha Hasana yakeyi. Akwana nabiyu akaje tambaya mishi aurenta kuma anbayar,dayake tinda yatafi akayi bincike akansu kuma aka samu basuda wani aibu. Su Abba sunso abasu auren Nadhira ma aranar ,amma gudun magana yasa tace zataje tafada wa big Dady cos bazaiyiyu tayanke hukunci dakanta bah,kuma su Abba sunyi na'am da barin . Hasana kuwa gadan gadan tafara aikin da yakaita ,inda masu gidan kuma suka amince da ita ,duk movement din mutanen gidan babu na wanda ba tayi monitoring bah,atakaice dai aikinta yana tafiya smooth Back to labari.... "Baby"..... "Na'am Abba".... "Why not ki fito da dadynki yasha iska"Abba yafada wa Nadhira dayake yaje wajen Antynsu kuma ta bashi LABARINSU kuma har mumy yafada wa kuma itama ta tausayi musu kuma tabada goyon bayan a aurawa Amin Nadhiran "Gaskiya Kam baby yakamata kifito dashi"inji mumy dafada "Toh"ta amsa cikeda jin dadi cos itama taso ace yana fitowa shan iska amma Kuma babu yanda zatayi.... Shiga tayi tareda fitowa dashi akan wheelchair dinshi daidai bakin kofa ta tsayar dashi tareda komawa cikin gida dan dauka ruwa,dadynsu kuwa sake hannunshi yayi daga kan handle din wheelchair din SAKAMAKOn gyangyadin dayafara,aikuwa nan wheelchair yafara tafiya dakanshi,kuma daman gangare ne, wheelchair Kam Sai tafiya yakeyi abinshi,daidai kuma lokacin Nadhira tafito dauke da goran ruwa a hannunta,mamakine yakamata ganin bata ganshi bah, jefar da goran hannunta tayi SAKAMAKOn ihun da taji anyi,aguje tayi inda taji ihun "Innalillahi..... Vote Comment& Share πŸ’‹πŸ’‹wurarhπŸ’‹πŸ’‹ πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *ABAR SO* πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *WRITTEN by: NAFISAT MA'ARUF SHEHU* *πŸ’‹πŸ’‹wurarhπŸ’‹πŸ’‹* *Wattpad: mhizzphydo 🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟 🌟G.W.F🌟 HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST Page 85-86 Barkanmu da sallah,Allah ya maimaita mana. Ameen "Innalillahi"shine abinda su mumy da Abba ke furtawa sanda suka karasa inda dadynsu yafadi "Dadynmu kabude idonka babynku ce,wayyo Allah kuyi wani abu mana ga kanshi yafashe "haka tadinga magana ita kadai lokacin da ta isa awajenshi,Abba kuwa phone yadauka yakira doctor,kamin yakira Amin akan yayi gaggawan dawowa gida, baima jira jin abinda Amin ke Shirin fada bah ya yanke wayan. Bada dadewa bah doctor ya iso ko gama parking baigama yi bah Keke napep yashigo da Amin cos daman alokacin da aka kirashi yana cikin Keke napep din dasauri yakarasa wajen, Abba yasha mamakin ganinshi amma yanzu ba lokacin magana bane "Akawo ruwa" shine abinda doctor yace,dasauri mumy tadauko bottle water, yayyafa mai akayi inda shikuma ya sauke nauyayiyar ajiyar zuciya "Yaya kataimake ni kabarni,karka cutar da families dina yanda kake ikrarin cewa,duk abinda kakeso Zan baka"Shine sambatun da yakeyi ,dasuka ga sambatun bamai karewa bane yasa su danna mai Allura,nan da nan bacci yakwashe shi. Carpet aka shimfida daidai wajen da yake sannan suka mirgina shi. Alokacin kuma Baby na rungume ajikin mumy tana sharban kuka. "Abbana garin yaya akan tafaru??" Amin ya tambaya yana mai miye da kallonshi wajen Abba, muryan dataji ne yasata dago kanta domin ganin mai magana amma Kuma bayanshi tagani, sake sunkuryar da kanta tayi yayinda Abba yabashi rahoton abinda yafaru...... Sallaman da akayi neh yasa su miyar da dubansu inda suka jiyo sallaman "Antynmu!!!" Tafada cikin kuka tareda barin jikin mumy, dagudu takarasa wajen Antynsu tareda rungumeta ta kuka, itama Antyn kuka takeyi sosai..... Mamaki ne yakama Amin dalilin ganin wanda baiyi expecting ba "Miye sukeyi anan??"Amin yatambaya "Kasansu neh??" Mumy ta tambayeshi batareda ta amsa mishi bah " Erh mana ABAR SO na da Antynsu" yabawa mumy amsa "Allahu Akbar, daman itace ABAR SO din?? ai itace mukace zamu aura maka"mumy tafada mai "Tsuntsu daga sama gashasshe"yafada azuciyar shi amma afili cewa yayi " Amma kince bazan kara aure bah??" " Yanzu ba lokacin magana bane" tabashi amsa Some hours later... Ahankali yake bude idonshi ,dishi dishi yafara gani kafin idon yabudu tas... Nadhira neh tafara lura dashi ,aikuwa dasauri suka matsa wajenshi " Dadynmu!!!" Tafada cikeda jindadi, muryan wanda yajine yasashi runtsa idonshi abubuwan da suka faru yafara dawowa mai..... " Nakashe duka iyalanka , kaida su kuma yanxu Sai amafarki kokuma a lahira" yayanshi yafada " Innalillahi wa'inna illahir rajioun....." Dadynsu yafada dakarfi hade da bude idanunshi,still bata bace ba juyar da kanshi yayi wajensu Abba yana sake fadin " Ya kashe su, he killed those innocent souls , he killed all of my happiness , why didn't he killed me too?? He knows that I lived for them, they are my second half..... "Dadynmu!!!" Nadhira ta Katse shi cikin cracking voice, dasauri ya juya jin ankira shi tareda taba shi " DanAllah ku mintsi ne ni ko zantashi da mafarkin danake yi " yafada yana me kallon kwayar idonta "Dadynsu!!! Antyn takira shi tana me taba fuskarshi ( cos haka take kiranshi) Ahankali yake juya fuskanshi gabadaya awajenta sannan ya sauke ajiyar zuciya mai karfin " Daman nasan yayana bazai iya kashe min iyali bah , nasan wasa yakeyi amma those jokes where so expensive, amaryata ina habibity na take sannan kuma ina Nafhira dakuma cikin jikinki??" Yafada yana mai taba cikin ta " Dadynmu!!!" Nadhira takira shi , miyarda duban shi yayi wajen ta " Babynmu!!! Ina yar uwarki dakuma Mommanku ??" Yatambaye ta tareda riko hannunta " That monster killed them, he gave them the worst death ever" ba bata lokaci ta zayyano mishi abinda yamusu saidai abu daya bata fada mishi ba shine alluran da aka mata " Ya Salam!!!" Dadynsu yafada hawaye na zuba daga idonshi likewise kowa na wajen " How could he be so cruel?? Hmmm Nayafe mishi duniya da lahira!!!" Arazane Nadhira tadago ga eyes nata sun gama rinewa tsantsan tashin hankali, su Abba kuwa mamaki ne Yakama su " Bangane ka yafe mishi bah??" Abba yatambaya " In ban yafe mishi bah kuma miye zanyi mishi?? Ku Tina fah sakkayya a wajen Allah yake,kuma Allah yanason masu yafiya muma fah muna mawa Allah laifi kuma yana yafe mana nikuma asuwaye da bazan yafe wa wanda ya mana laifi bah?karku manta fah ciki daya muka fito dashi dan'uwa na ne najini in shi ya kini wlhy ni haryanzu inason shi , tinkan ayi daran akayi kwandi, kunga babu abinda Zan iyayi akai" Dadynsu yafada cikeda da kwarin gwiwa " Tabbas haka yake, Allah ya yafe mana gabadaya" Abba yafada "Ameen" aka amsa in chorus amma banda Nadhira cos ance na ciki na ciki " Nagode sosai Allah yabiya ku" dadynsu yafada wa su Abba cikin hawaye " Babu komai ai yiwa kaine" Abba yafada " Zaku iya dawowa nan da zama tinda akwai parts dayawa cos nasan zai iya zamowa matsala idan yaganka da rai" Abba yafada " Gaskiya neh wannan shawaran yayi" mumy tayi adding " Bazamu daina yimuku godiya bah" Antynsu tafada " Ai babu

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27