Chapter 24
Chapter 24
yagama duba ta Iska Amin ya furzar sannan yace"Toh gaskiya nikam banyin wannan aikin in har ba'ayi involving din police bah" "Erh gaskiya nima haka nakeson cewa, bari nakira police din Sai suzo"doctor yafada Isowar police yayi daidai da isowar su big dady da duka yen gida amma banda yen matan gidan Statement yen sanda suka karba sannan sukace dole Sai anje an bincike gidan su big dady. Batareda bata lokaci bah suka dunguma zuwa gidan gabaki dayansu harda Amin. Ganin gidan da motansu yayi horn yasa Amin sauke boyeyyar ajiyar zuciya. Zaune suke akan sofa suna kallo while ita Nadhira na kitchen tana girki, muryan su big dadyn dataji yasata fitowa dasauri tana goge hannunta da hand towel. Runguman shi tayi irin na sannu da dawowa sannan tace"ya naga harkun dawo?" Sam bata Lura da yen sanda dakuma Amin dinda takafe ta da ido bah,ji yake dama shi ta runguma bah wannan mugun mutumin daya nakasar da sirkinsa bah. Kuma gaskiya yasha mamakin ta amma daya tina dadynsu yace ya yafe mishi saiya basar da zancen azatonshi itama Nadhira ta yafe mishi neh, dadi sosai yaji wai ABAR SOnshi tana da kyakyawar zuciya(nace Allah yasa) "Muna tareda police neh sunzo duba gidan"wani irin rass taji gabanta yabada kafin tamiyar da dubanta kansu daya bayan daya take binsu da ido har ta tsaya cakk da idonta akanshi. Wata uwar harara ta jefe shi dashi tareda hade fuska kaman bata taba dariya bah ganin yana mata murmushi, jikinshi neh yaji yayi sanyi sosai. Banda kallon shi babu abinda takeyi dukda yanzu tafara mantawa dashi cos dakanshi ya hadata da abokin shi amma kuma abu mai wuya neh ta manta dashi gabadaya a babin rayuwarta.(First love) Maganar yen sandan neh yakatse su ,inda aka musu gajora zuwa dakin Maimuna din, duk bincike anyi amma ba'a samu komai bah banda kwalaben codeine. Daki daki suka shiga amma ba'a samu komai bah, saukowa kasa yace aje aduba kitchen. Duk iya binciken su ba'a ga komai bah, fita suka yi daniyar tafiya, har sun kai bakin kofa wanda yamusu jagora ya tsaya cak tareda facing dakin Nadhira yayi sannan yace "Bamu duba wancan dakin bah" wani irin dum dum taji gabanta ya bada, Adduan datake karanta wa azuciyar ta yasa halin da tashiga boyuwa kadan. "Amana jagora" taji anfada cikin in in na tace toh,gawani zufan dayafara karyowa takowani gaba najikinta. Amin neh ya Lura da halin da tashiga, "Akwai matsala neh??" Yatambaye ta Wani hararan takuma banka mai ahasale tace"ina ruwanka dani" "Muje" tafada hade da yin gaba, big dady mah alokacin ya daura ayan shakku akanta. Bincikan dakinta akeyi abinda suka ganine yasa dukkansu miyar da dubansu gareta cikeda mama.... *Nace toww miye suka gani?ππ* *Vote,comment&share* *Mhizzphydo* πππππ *ABAR SO* πππππ *WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU* WATTPAD: MHIZZPHYDO πGEORGEOUS WRITERS FORUMπ πG.W.Fπ HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST *Page 97* Bincikan dakinta akeyi abinda suka ganine yasa dukkansu miyar da dubansu gareta cikeda mamaki. Amin neh yakarasa wajen tareda tsungunawa zuciyar shi na zafi sosai har ga Allah baiyi tsammanin haka daga gareta bah kuma zarginsu ya tabbata akanta . Runtsa idonshi yayi sannan yabude su so yake ya karyata abinda yake gani. Daya daga cikin police din neh yake karewa Nadhira kallo nan kuwa yayi harba da kafanta cos as usual short gown neh ajikinta. Dawowa sama da idanunshi nan kuma yakara harbawa da kirjin ta wanda ko bra bata sanya musu bah, wani irin yawu ya hadiye tareda lashe kasar labban shi. Ganin kallon da suke mata neh yasata tattara duk nutsuwar ta waje daya takuma aza murmushi asamar fuskarta tareda karasawa wajen Amin cos ita kam mah tadauka wani abin daban zasu gani shiyasa tsoro shiganta . Karban kwallin Condom din tayi hannunshi, tareda lura da yanayin bakincikin dayake ciki kafin tace "Akan wannan abin kuke kallo na kaman wata sabuwar hallita,nikam mah har kunsa naji kunya" Ganin yanda take magana naneh yasashi tsura mata ido for some seconds gani yayi duk wannan tsoron dakuma rashin gaskiyan daya bayyana a fuskarta dazu babu su. Cikin sanyin murya yace"miye kikeyi dashi??" "Toh miye zatayi dashi ai kowa yasan amfanin wannan abun guda daya neh tal" wannan police din yafada cos bakaramin bata mai rai Amin yayi da wannan tambayan bah. "Lahπ¨π¨ waye cemuku amfanin shi daya neh??" Ta tambaye su cikeda mamaki. Shuru dakin yadauka suka sake Baki da hanci suna mai neman dayan amfanin Condom cause gabadaya ta jefa su aduhu. "Ke karki raina mana hankali fah" wannan police din yasake fada a kaushashe cos gabadaya tafara bashi haushi ,shidayake son neman hanyan daza su hadu soboda gaskiya ran shi yabiya(Niko nace kwalelenka) "Yadai kana min magana saikace yar ka??" Tafada tareda maka mai harara. Zaro ido yayi ganin abinda tayi mishi amma ba damuwa zaijira insun hadu yafada mata shi baya daukan raini( lallai kam) "Just say what kikeyi da wannan" yafada cikeda zakuwa "Packing din gashi na nakeyi dashi" tafada sounding relieved "What a bullshit" Amin yafada afusace cos gani yake raina musu hankali kawai takeson yi Itadin mah bai tsira bah sanda ta banka mai nashi hararan, rolling eyes dinta tayi sannan tacire dankawalin kanta. Nan kuwa doguwar gashin ta ya bayyana wanda aka tufke atsakiya. Zaro abinda ta tufke gashin tayi tareda mika mishi abin wanda shi bah roba Lin bahγ Karba yayi yana juyawa ahannu shi amma har lokacin bai dago miye bah, shima police din karba(inaga shi yayi leading dinsu) yayi yana dubawa. Duka dakin sanda suka rike abin suna kallo daga karshe suka miyarda duban su gareta. "Baku gane miye bah koh??" Batareda ta bari sun yi magana bah ta ciro Condom daya daga cikin kwali. Fatima kam harda rufe ido wai batason gani, dariya kawai tayi sannan tayi wajen drawer. Razor blade tadauko sannan ta ijiye Condom din akan dressing mirror. Yanka daidai wajen band din rike ...ππ tayi Sannan ta dago shi. Toilet tashiga ta wanke yanda maikon zai bar jikin abin bayan nan tafito. Na mujiya suka zuba mata suna kallon ikon Allah. Mika musu tayi suna kallo Sai sukaga iri daya neh da wanda tacire akanta. Murmushi tasakar musu tareda fadin" akan nayi amfani da roba Lin ya tsinka min gashi toh gwanda nasa wannan, in takaice muku nafi jin dadin amfani da '''CONDOM BAND''' akan kowani band" Mamaki neh yacika su jin abinda takeyi da Condom cos basu taba zargin haka abin yakeba sun dai San ana amfani da Condom neh wajen kariya while Amin ya dinga blaming kanshi akan zarginta dayake yi, sosai zuciyan shi yasamu relief jin ba abinda yake tunani bane Dariya da ita kadai tasan ma'anar shi tafashe dashi sannan tace" I knew you will all be shocked, shiyasa ma dafari tsoro tashigeni dana tina da na fito da kwallin kuma dafari I thought bazaku tsaya ku fahimce ni bah" Ta karashe maganar da murmushi, dukkansu mah murmushi sukayi amma banda wannan police din cos gabadaya shirin shi ya wargaje. Fita sukayi daga dakin, cewa sukayi zasu duba compound din ba bata lokaci aka musu izinin dubawa. Har suka gama dube duben basu ga komai bah, haka suka koma akan in Maimuna tafarfado zasuji komai... Zaune take
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27