Chapter 8
Chapter 8
ta fito daga kitchen, ganin Hadiza yau nade cikin kujera sai ta fashe da kuka, Sulaiman ya yi saurin ficewa a falon ya dau mota ya fita don dauko yara a makaranta. Hadiza ta dubi Alti ta yi dan murmushi, “Alti wane ne ya halicce mu?” Ta ce, “Allah (S.W.A)”. Ta ce, “To kinga in haka ne ke nan bamu da iko da kanmu sai abin da ya ga damar hukuntawa a gare mu, mu kuma dole ne mu zamto masu godiya idan har muna so imanin mu ya cika”. Alti ta jinjina kai tana mai jinjina karfin imani irin na uwargijiyarta. Hadiza ta juya ga Fati ta ce ta kal kayanta dakin ta, kasancewar a tsarin gidan likitocin babu wani edtra room, ita za ta yi amfani da na Sulaiman. Fati ta ce atafau ita dakin su Muniba za ta zauna tare dasu, ta kada ta raya amma ta ki, ta ciccibi jakarta ta yi dakin su Muniba. Fitar ta daga falon ke nan su Munib suka dira a falon, Baban su na biye dasu yana rike da jakunkunan su da food flasks din su. Suka tafi da gudu suka rungume Mamarsu, Munib da yake shine mai wayo ya ce, “Mummy yaya jikin ki? Daddy ya gaya mana kin yi accident kin ji ciwo kina asibiti ana yi miki allura?” Ya kai hannu ga tabon ciwon goshinta, “Sannu Mummy, kin ji?”. Ta shafa kansa ta yi masa murmushi bata ce komai ba. Ita kuwa Muniba bin jikin Mummyn ta yi ta lafe kamar mage, dama ita ba ta fiya magana ba. Zuciyarta kal da ganin mahaifiyarta da ta jima ba ta gani ba. Munib ya soma jan hannunta wai ta taso suje su yi kwallo (ball) kamar yadda suka saba, Sulaiman ya kau da kai, bai son ganin wannan abin tausayi, ya mai da hankali ga lallatsa wayar sa, baya son su ga hawayen sa. To ita ma Hadizar duk dauriyar ta sai da hawayen suka tsatstsafo, ta sa yatsun ta biyu ta dauke su, ta kama dukkan ‘ya’yan biyu ta rungume a kirjinta. Kukan zuci take wanda ya fi na fili soya zuciya. Ta ce, “Ku tafi wurin Anti Fati tana dakinku ku yi kwallon tare, har yanzu bani da lafiya”. Da gudu suka mike daga jikinta suka nufi dakin su suna murnar zuwan Antin su da suke tsananin so. Alti ta yi sallama dauke da tray kanta a sunkuye ta ce da Hadiza, “Na ce sai na daina daura abinci a tebir?’ Hadiza ta yi murmushi mai hade da wani irin huci mai zafi, ta ce, “Idan maigidan yana son hawa tebir din fa?” Ta fada tana kallon Sulaiman. Bai dago ya kalle su ba, haka bai tofa musu ba, duk da ya lura ta bakinsa suke son ji. Alti ta ajiye katon tray a gaban Hadiza ta juya ta fita. Tana ba da baya ya suri Hadiza a kafadar shi sai dakin barcin su. A hankali ya sauke ta a makeken ‘family bed’ din su, ya koma toilet ya cika baf da ruwa mai dumi, ya zuba dettol kadan ya dawo ya soma warwarewa Hadiza kayan jikinta, ya nade ta cikin towel ya sake sungumar ta ya yi toilet ya sanya ta cikin ruwan da ya hada. Ita karfin Sulaiman mamaki yake bata. Ya yi mata kyakkyawan wanka da kamsassan sabulun Zest, ya nado ta ya fito da ita. Yawancin kayanta a dakin suke, don haka ya shirya ta cikin riga da wandon pakistan ruwan goro (orange), ya dauki (kumb) ya soma sharce mata gashin kanta wanda rashin gyara kwana biyu ya sa shi duk ya cukurkude. Ta ce, “Da ka bari Sulaiman Fati za ta yi min”. Bai saurare ta ba ya ci gaba da abin da yake, amma da a ce ta kalli fuskarshi a lokacin, data lura da yadda ya dan hada rai, saboda ambatar Fati da ta yi, wato ta fi son Fati ta kula da ita fiye da shi. Ta yi murmushi ta ce, “Amma tunda ka hada ruwan wanka ka yi mai wuyar, zan iya wanka da kaina,sai Fati ta shirya ni koda yake ma zan iya shiryawa da kaina……. ” “Is o.k Hadiza, ba tun yau ba na san kin fi son kanwar ki fiye dani. In ba haka ba ni amfanin me ke gare ni? Da ba zan kula dake ba a lokacin da kike cikin lalura?” Ta kama baki, don ba ta ji dadin maganar shi ta farko ba, amma sai ta share ta ce, “Yau da gobe ne sai Allah Sulaiman……. “. Can kuma ta yi rau-rau da ido kamar hawaye za su zubo, “Me ya kawo maganar na fi son Fati a kanka? Ban ji dadin nagetive response din ka ba”. Ya ce, “To ai ke ce Hadiza da wani irin batu, amma ina so ki yarda da cewa, idan zan gaji da hidimar ki Hadiza, to zan gaji da_ hidimar Kaina…… ” Ta ce, “Amma Sulaiman…… Ya kai hannu ya toshe mata baki, “Kina shakka da abin da na ce miki?” Ba ta son jan zancen da nisa, har ya yi tsayin da zai zamo bacin rai, sai ta ce, “Bana shakka Sulaiman, Allah ya bamu rai da lafiya”. Ya turo ta cikin kujerar ta suka dawo falon don cin abinci. Munib da Muniba suka shigo, fes dasu cikin kaya ‘yan kanti (pink colour) har Fati tayi musu wanka ta shirya su ta feshe su da turare. Suka saki baki cikin mamaki, ganin Daddy yana tura Mummy cikin kujera, abin ki da yaro, sai ba su kawo ma ransu komai ba, ko wani abu ne ya faru da Maman nasu, sun dauka haka nan dai yake tura ta don bata da lafiya. Sai suka sa rigimar ta tashi suma Daddy ya tura su. Haka Sulaiman ya sauke Hadiza a seater, ya dauke su su duka biyun ya aza a kujerar, ya yi ta zagaya falon dasu suna jin dadi, sai kyalkyatar dariya suke. Hadiza ta juya ta dube su, ganin abin nasu ba na kare bane ta ce, “Oya! Food is ready, maza ku zo ku ci kafin malamin lesson ya zo, ko kuna so ku yi latti ya yi muku bulala?” Suka diro daga kujerar suka nufo abincin, Sulaiman ya zauna tsakanin Hadiza da Muniba, kafadun su na gugar na juna. Ta sa murya ta ce, “Fati!” Ta fito sanye da hijab, da alama sallah ta idar, kallo daya Sulaiman ya yi mata ya dauke kansa, ya ci gaba da cin abincinsa. Daga can bakin kofa ta tsaya ba ta karaso cikin falon ba, son addini irin na Fati yana matukar burge Hadiza ba kadan ba. Ta ce, “Taho mu ci abinci in kin idar da sallar”. Ta yatsina fuska ta ce, “Na ci tun dazu, Alti ta zuba mini”. Don jikinta ya yi sanyi da hararar da Sulaiman ke zabga mata, bayan ita ko da gida da mota aka hada ta dama ba za ta ci abinci da shi ba, don ta ki jinin mutum mai halin GIRMAN KAI. To a ganin ta halin Sulaiman kenan, babu wanda ke ganin walwalar shi sai ‘ya’yan shi da matarshi, duk ilimin da ya ke takama da shi a ganin ta girman kai ba hali
Table of Contents