Chapter 5
Chapter 5
ta da sedy eyes din sa, masu kassara ta, ba shiri ta sunkuyar da kai, don ba ta iya jure kallon idanuwan nan na Sulaiman din ta, masu rikirkita kowacce lafiyayyar diya mace, balle ita matarshi ta sunnah, data fi kowa sanin sirrinsa na zahiri da badini. A raunane ta ce, “Ban so ka yi min wannan fahimtar ba”. “Sai wacce kike so in miki?” “Irin wadda ka saba, understandable (ta fahimta)”. Ya yi murmushi ya mike daga kujerar ya koma mazaunin shi, duk ya shafa mata mayataccen kamshinsa na _ turaren ‘Chris Adams’. Nutsuwar matarshi da haibarta na burge shi, magana take cikin nutsuwa da haiba, kamar ba daga bakinta furucin ke fitowa ba, dauke da matsananciyar kauna a cikin kwayar idanun ta. Son ta da kaunar ta na kara kwarara a zuciyarsa, ya rasa inda zai sa kansa. Ya kama kanshi da hannuwan shi biyu. Ya ce, “Hadiza bana so ki tafi ne, sai in ji ni lonely kamar maraya…….. !” Ta ce, “Alfarma za ka yi min Sulaiman, muna tare muddin rayuwar mu”. Ya mika mata hannu ta kama, ta isa gare shi. Ya miko mata kumatun shi yace, “Kiss me plzzzz……772”. Ta ji kunya sosai, ta boye kanta a kafadun shi, ita ba ta iya wannan keke-da-keken ba. Ta ce, “Kudin da zan kai mata za ka bani Su laiman, ba kudi a waje na”. Ji yake in zai iya ba ta ranshi, to zai ba ta. Balle duniyar da abin da ke cikinta. Bai tambaye ta me za ta yi dasu ba, ko adadin da take so, ya kwaso duk abin da ke cikin aljihun shi ya zuba a jakar ta. Allah sarki! Kamar ba za su rabu ba, a lokacin har duhun dare ya shigo, likitoci uku ne da ke karkashin sa suka kwankwasa suka turo kofar suka shigo. Dole Hadiza ta dau jakarta da lab-coat hadi da gilashinta ta fita, yana kara jaddada mata ta yi tuki da kula. Dan banzan go slow ne ya tare ta a titi, ba ta isa gidansu ba sai tara da rabi, Maman su da suke kira Yaya, tana zaune a tsakar gida da rediyo a hannun ta tana sauraron Jakar Magori. Autan su Abdulyassar yana gefe yana hada motar kara. Yaya Babar su Hadiza ba wata tsohuwa ba ce cancan, don irin auren wurin nan aka yi mata, shekarun ta arba’in kenan. Hadiza ta yi sallama Yaya ta amsa, Abdulyassar ya watsar da _ kayan wasan shi da gudun shi ya kwaso ya rungume ‘yar uwar shi, kasancewar ta mai jan su a jiki tare da nuna musu kauna. Yana tambayar ta ina Munib? Daga can dakinta na ‘yammatanci, wanda a yanzu ya zan mallakin Fati, sautin Abdurrahaman Sudais ke tashi a hankali cikin suratul Al-Imran, wannan ya tabbatar mata Hafiza Fati Ja‘afar na gida. Ta samu gefen Yaya ta zauna, Yaya ta mike daga kwanciyar da ta yi bisa tabarma. Kai da ganin kyakkyawar fuskarta ka san ta ji dadin ganin diyar tata, ta ce, “Da daddaren nan Hadiza?’ Ta ce, “Wallahi Yaya, Dr. ne ya tare ni, na kawo ma Fati kudin ne”. Ta ce, “Amma kin kyauta, don da ta yi ma Yayan ku maganar ta waya ya ce ba zai samu zuwa Kano wannan satin ba, ga shi baban ku kwanan nan kasuwar ta ja baya, kuma ta ce daga wannan satin za a rufe”. Ta ce, “Baba bai dawo bane?” Yaya ta ce, “Ya dawo tun yamma, ya tafi dubiyar dan gidan Malam Abdu ne babur ya buge shi dazu”. Ta ce, “Allah ya sauwake, Fati na ciki ko”. Yaya ta ce, “Yanzu ta gama cin abinci ta shige ciki tana rehearsal, jibi za su yi musabakar jiha kuma ita za ta wakilci jihar Kano, kin san Fati ba daga nan ba”. Cikin alfahari da kanwar tata a zuciyarta, Hadiza ta tura kofar dakin cikin sallama, Fati ta diro daga gado ta rungume ‘yar uwarta tana yi mata oyoyo. Hadiza ta dubi Fati sama da kasa, ta zama cikakkiyar budurwa sosai. Ta kama baki “Fati girma haka?” Fati ta yi murmushi, kumatunta duka suka lotsa gwanin sha’awa, wushiryarta ta fito siririya da ita. Hadiza ta ce, “Wane course aka samu?” Ta ce, “Course din da na nema ne (Islamic Studies)”. Ta ce, “Masha Allah, da an je kuma sai a Samo saurayi, irin wannan girma haka Fati?” Ta ji kunya ta boye fuskarta cikin tafukanta, ta ce, “Ai hijabi zan ke zumbulawa irin mai hannun nan, kada ace ana so na”. Hadiza ta ce me za ta yi ba dariya ba, duk girman Fati baka raba ta da wauta. Ta kirgo kudi a jakarta naira dubu ishirin ta ba ta, Fati ta yi godiya ta ce, “Allah Yaya Hadiza kwana biyu ba’a kawo su Munib ba”. Ta ce, “Makaranta ta boye su, amma da anyi hutu suna nan tafe insha-Allah”. Sai sannan ne ta ga hakoran Fati. Ta ce, “Ashe kuma musabaka za a yi Fati ba labari? To Allah Ya ba da sa’a”. Ta yi murmushi ta ce, “Ameen”, Tana shirin fita Baban su na shigowa, ya ce, “A’ah, manyan likitoci ne yau a gidan namu? Ina matas da abokin?” Ta yi murmushi ta tsuguna har kasa ta gaida tsohon ta, ta ce, “Suna nan lafiya basu samu hutu bane, da sun samu za su ZO”. Yace, “Kinga kafar nan tawa kwanan nan bana jin dadin ta, har na gaji da hadiyar magani”. Ta ce, “Wane magani ne Baba? Likita ne ya rubuta?” Ya ce, “A‘a, maganin ciwon kashi ne kawai nake saya a wajen masu talla”. Ta kama baki, “Baba irin wadannan magungunan ba masu kyau bane, yawanci ma sun yi edpiry don Allah ka daina sha. Yanzu bari in rubuta maganin Fati ko Hamza su je su siyo”. Yace, “To na gode”. Ta baro Karkasara karfe goma daidai na dare, dauke da tazbihi a bakinta domin ba abu ne da ta ke so ko ta saba ba, wato (night dribing) tukin dare. Ta biyo ta titin Court Road ta hawo titin Gandu, ta yi kwana ta hau titin B.U.K Road. Ta iso Kabuga ta dau titin New-site wanda zai sadata da Janbulo. Babu wadatar motoci a titin. Daga gefen ta wayarta ta yi kara, sunan Sweetypie ya soma yawo a screen din. Ta yi murmushi ta mika hannun damanta ta dauka, ta rike sitiyari da hannun hagu cikin sanyin sauti ya ce, “Ya ya? Hope for now kina gida?” Ta yi ajiyar zuciya cikin karyayyar murya ta ce, “Na kusa dai, ina kan Iya abin da ya ji ke nan sai wata irin kara da ta fi kama da fashewar taya, ya yi kira “Hello!…..Hello….Hadizah!” Amma ba amsa. Motar ta hantsila ta shige karkashin wata trailer da ke cike da buhunhunan abinci, duk da kokarin da direban ya yi wajen kauce mata hakan bai samu ba, motocin da ke gabansu da bayan su duk suka yi birki cikin salati, tsirarun mutanen da ke gefen titi suka runtumo don kawo agaji. T a hanyar katin shaida (ID Card) jami’an tsaro suka gano ko wace ce Hadiza. Don haka ba su sha wahalar samun nombar wayar mijinta ba, wanda ke can cikin gigicewa. Nan asibitin aka taho da ita cikin
Table of Contents