Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Yakanah Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

iya hada ido da surukansa ba. Malam Ja’afar ya karasa jikin gadon Hadiza ya kama hannun ta inda babu ciwo, ya ce, “Ki yi tawakkali Hadiza, ki zamo mai YAKANAH a dukkanin al’amuran ki, ki zamo mai godiya ga Allah a duk yanayin da kika tsinci kanki. Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba, yarda da kaddara dole ne ga duk musulmin kwarai”. Cikin kuka mai tsanani ta ce, “Na ji Baba, amma don Allah ku fada min me ke faruwa dani? Sulaiman bai gaya min komi ba, sai kuka yake yi, kukan shi ya daga min hankali, ku fidda ni a duhu. Wani abu ne ya faru dani?” Malam ya sa habar babbar rigar sa ya share hawayen da suka ciko mishi ido cikin dabara wai kada Hadiza ta ga shi ma kukan yake, amma ta ganin. Hadiza ta musamman ce ko a cikin ‘ya’yansa, yana son ta son da bal yiwa su Mukhtar, ganin Babanta yana kuka sai ta kara tsananta kukan ta. Cikin tausasawa Mukhtar ya ce, “Cool down Hadiza, take it easy……. Ya shiga rattabo mata al’amarin da ya samu rayuwarta, ya kare da cewa, ““Wannan shi ne ya dagawa Sulaiman hankali, amma kamar yadda Baba ya ce ne, ki yi tawakkali, ki zamo mai YAKANAH! Wannan ba shi _ ne karshen rayuwar ba!” A matsayinta na cikakkiyar likita, tuni ta gano mummunan nakasun da ya samu rayuwarta wanda babu wani likitan duniya da zai iya maganin shi. Ta nemi hawaye a kwayar idonta ta rasa, ta nemi miyau don ta hadiya a kan harshen ta ya kafe karaf! Kamar Fati a gaba, Yaya, Malam, Hamza da babban Yayan su Mukhtar suka shigo, daga Hadiza har Sulaiman babu wanda ya san da shigowar su, shessehekar kukan Fati ne ya ankarar da Sulaiman cewa akwai mutane a dakin. A hankali ya zare jikinsa daga na Hadiza ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya iya hada ido da surukansa ba. Malam Ja’afar ya karasa jikin gadon Hadiza ya kama hannun ta inda babu ciwo, ya ce, “Ki yi tawakkali Hadiza, ki zamo mai YAKANAH a dukkanin al’amuran ki, ki zamo mai godiya ga Allah a duk yanayin da kika tsinci kanki. Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba, yarda da kaddara dole ne ga duk musulmin kwarai”. Cikin kuka mai tsanani ta ce, “Na ji Baba, amma don Allah ku fada min me ke faruwa dani? Sulaiman bai gaya min komi ba, sai kuka yake yi, kukan shi ya daga min hankali, ku fidda ni a duhu. Wani abu ne ya faru dani?” Malam ya sa habar babbar rigar sa ya share hawayen da suka ciko mishi ido cikin dabara wai kada Hadiza ta ga shi ma kukan yake, amma ta ganin. Hadiza ta musamman ce ko a cikin ‘ya’yansa, yana son ta son da bal yiwa su Mukhtar, ganin Babanta yana kuka sai ta kara tsananta kukan ta. Cikin tausasawa Mukhtar ya ce, “Cool down Hadiza, take it easy……. Ya shiga rattabo mata al’amarin da ya samu rayuwarta, ya kare da cewa, ““Wannan shi ne ya dagawa Sulaiman hankali, amma kamar yadda Baba ya ce ne, ki yi tawakkali, ki zamo mai YAKANAH! Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba!” A matsayinta na cikakkiyar likita, tuni ta gano mummunan nakasun da ya samu rayuwarta wanda babu wani likitan duniya da zai iya maganin shi. Ta nemi hawaye a kwayar idonta ta rasa, ta nemi miyau don ta hadiya a kan harshen ta ya kafe karaf! Kamar bai taba gudana a cikin bakinta ba. Ta runtse idonta da karfi, tsawon mintuna biyar ba ta bude ba. Ita kadai ta san radadin da take ji a zuciyarta, ita kadai ta san azabtuwar da ruhinta ke yi, al’amarin ya shallake tunanin ta. Ba ta yi tsammanin al’amarin ya yi kamarin haka ba, lallai dan adam ba a bakin komai yake ba. Yau ne kake mai rai, gobe ne kake gawa. Yau ne kake da amfani, idan Ubangiji ya so, gobe ne ka zama tarihi. A rayuwar Hadiza ba ta taba tsammanin wata kaddara makamanciyar wannan za ta taba shafar rayuwar ta ba. To ina ruwan Allah! Ta bude idon a hankali tana kallon iyayen ta da ‘yan uwanta wadanda dukkanin su ke sharar hawaye, sai ta soma lallashin su cikin muryar ban mamaki, tamkar ba ita ba. Ta fi su karfin zuciya, ta fi su tawakkali, ta fi su YAKANAH. Ta karbi kaddarar ta da hannu bibbiyu, tana fatan Allah ya sa hakan ya zamo kaffara a gare ta, in kuma jarrabawa ce ya sa ta cinye jarrabawar ta. 36 KOK Dole kanwar naki, Sulaiman ya sayo ma Hadiza wheel chair ana i gobe za a sallame su daga asibiti. Don duk raunin dake jikinta ya kame sai karfin jiki da dan abin da ba a rasa ba. Yaya ta so Sulaiman ya ba ta Hadiza ta wuce da ita gida inda za ta fi samun kulawar iyaye da ‘yan uwa, amma sai ya sa musu kuka. Da me zai ji ne? Da lalurar da ta kashe masa rayuwa, ko da rashin Hadiza a cikin gidan, wadda ta zamo wani bangare na rayuwar sa, kundin farin cikin sa, sannan barin jikinsa? Dole suka kyale shi da matar shi, amma sun ce Fati ta koma gidan ta zauna tare dasu, don ta dinga taimaka masa kula da Hadiza, musamman kasancewar sa ba mazauni ba. Sulaiman bai so ba, don shi tun fil’azal Allah bai sa mishi son Fati ba, saboda son da Hadiza ke mata. Yana kishin Fati, a ganin sa Hadiza ta fi son Fati a kanshi. Sannan zubin ta na zuhudu (gudun duniya) ya yi yawa, bai fiya son mutane irin ta ba, kasancewar shi (sociable). A tsarin halittar dan adam (personality), tana cikin rukunin al’ummar da ake kira (introbert). Ba ta iya hada ido da shi, kai da kowa ma, saboda kunya. Da wuya ka ga hakoranta, sai dai in guri ya kure ta yi murmushi, ‘dimple’ din da ‘cleft’ su lotsa, wanda shi ne muhimmin al’amarin da ke daukar hankalin dubban maza a kanta, sai dai kuma bai isa ya tsallake hukuncin da Yaya ta yanke ba. Haka Fati ta hado kayan ta tsaf, ta dawo gidan ‘yar uwarta da zuciyar ‘yan uwantaka. Zuciyarta cike fal da so da kaunar ‘yar’uwar ta, karatun da ta taso shekara da shekaru da burin yin sa, gashi ta samu, amma ta jingine shi ta sadaukar da rayuwarta kacokam da lokacinta ga rayuwar, ‘yar uwarta. Sulaiman ya ciccibo Hadiza ya fito da ita daga mota, Fati ta bude (boot) ta fiddo wheel chair a nade, cikin sauri ta warware, Sulaiman ya sanya ta a ciki ya tura a hankali zuwa cikin gida. Fati ta fiddo kayansu daga cikin motar ta rufe motar, ta soma diban kayan daya bayan daya tana shiga dasu cikin gida. Malam Ilu maigadi, ya yi sallama a falon, a lokacin Sulaiman na kici-kicin aza Hadiza a daya daga cikin kujerun falon, ba tare da ya juyo ba ya amsa masa. Ya zube har kasa yana jajantawa iyayen gidansa kaddarar da ta same su. Yana magana yana sharar hawaye, saboda yadda yake matukar kaunar Hadiza, saboda karamci da kyautatawar ta gare shi. Haka Goggo Allti

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18