Chapter 3
Chapter 3
san shi ba. Ya fahimci dalibar (obstetric and gynaecology) ce, daga (ID Card) din ta. Yadda ya ga rana haka ya ga dare, ko na second daya bai runtsa ba. So da kaunar student (daliba) Hadiza na narkar mai da zuciya. Abin kamar sihiri, daga ranar bai kara ganin Hadiza ba, bai kuma san ya zai yi ya tambaya ba, tunda ko sunanta bai sani ba. A matsayinsa na babban likita, mai juya sauran likitocin bangaren su, ba karamin zub da kima bane a ji shi yana tambayar wata yarinya cikin masu daukar darasi a wurin su. Duk da haka bai fidda rai ba, yana da yakinin watarana Allah zai sake hada shi da yarinyar ko da a mafarki ne. Ita kuwa Hadiza ba ta dawo TH ba sai bayan sati uku, tana gida tana Jinyar Maman su da suke kira Yaya, da ke fama da ciwon hanta. Tana ganin likita a Murtala, har suka kwantar da ita sati guda. Kawarta Surayya ke daukar musu Jacca tana kuma sanar da ita duk abin da ke faruwa ta waya. Ranar monday Maman su ta ji sauki sosai, don haka ta shirya ta dawo. Ba zato babu tsammanin shi, yana ganawa da wata patient din suka shigo ita da Surayyah, ya zare gilashin idonsa a hankali, ya saki wata sassanyar ajiyar zuciya irin ta wanda ke neman abu, ya wahala ya dade, kamin ya samu. Duk hankalin sa da attention din sa sai ya koma kanta, ya manta abin da ke gabansa, ya samu kansa da rudewa. Abin da bai taba yi ba a kan diya mace, akwai wani sassanyan kallo cikin kwayar idon Hadizah, da ba duk mata Allah ya mallakawa ba. Suka gaishe shi cike da girmamawa, sannan suka samu kujeru suka zauna. Hadiza dai a darare take, ko kanta ba ta dago ba. Daga gefe-gefen idon ta take satar kallon likitan da ya hargitsa mata tunani ‘yan kwanakin nan. Tunda ya kore ta ba ta kara samun nutsuwar zuciyarta ba, har zuwa yau da ta sake tozali da shi a karo na biyu. Ta tambayi kanta, shin ko mutane nawa ne a duniya irin Dr. Bakori? Yana da wasu ilhamomi na musamman a tare da shi da ba ta taba ganin su a da namiji ba, ko yadda yake duban mutane daban ne da na sauran likitocin da ta sani. Tsarin maganar sa cikin seriousness shi ne babban abinda ke burge ta da shi, ga kamun kai da sanin mutuncin kai, hadi da rashin son wasa ta ko’ina. Dr. Sulayman Bakori, ya shiga cikin rukunin wasu mutane da take ganin matukar kima da mutuncin su, sannan kuma ya bi ya manne a zuciyarta, ta yadda dai-dai da minti daya ta kasa manta shi cikin satittikan da ta yi tana jinyar Mamanta. A gurguje ya basu laccar ya kuma sallami mara lafiyar da suke tare da ita. Suka mike da nufin su tafi, baya fatan wannan damar da kubuce masa, don haka bai yi kwauron baki ba, ya yi ta maza (in ji mata) ya ce da Hadiza cikin wata irin lallausar murya da ya kasa yarda cewa tashi ce. “Wato fushi kika yi? Kika daina halartar karatun ki sabida na kore ki a kan kin yi min laifi?” Ta yi ajiyar zuciya a hankali ba tare da ta juyo ba, ta ce, “A haba Doctor! Wane ni in yi fushi? Mum dina aka kwantar a_ hospital kuma ni nake jinyar ta sai jiya aka sallame mu”. Ya nuna tausayi tsantsa a_ kan kyakkyawar fuskarsa, ya ce, “Ayya! Ta juyo ta yi mishi murmushi, suka yi ido hudu da dan Inna Halima, wani chemistry yayi aiki cikin ‘yan dakikai, ya kimsa wani al’amari mai GIRMA a zuciyoyinsu mai wuyar bayyanawa. Gwiwoyinta suka yi sanyi, zuciyarta ta karye, duk wata soyayya da Allah ya halitta a zuciyarta ta hadu ta tattare waje daya. To haka shi ma. Jikin shi ya ba shi wannan ita ce matar auren shi, wadda za ta samar mishi da ‘ya’yan da zai yi alfaharin fitowar su daga tsatson ta. Ya ce “A bani address zan zo in duba Mamar mu”. Daga ita har Surayyah sai suka yi mutuwar tsaye, domin abune da ko da wasa basu taba kawowa ba. Kowa ya san shi da halin ko in kula da yake nunawa a kan mata, wanda ke burge kowa. Don haka sun sha mamaki. Ita Hadiza ta kasa magana, sai Surayyah ce ta rairayo mishi adireshin Hadiza. Ya ce, “Idan na zo wa zan ce?” Ta ce, “Hadizah!””. Ya ce, “Hadizahh, am I welcome?” Ta yi murmushi ta ce, ” You are welcome!!”. Tun daga ranar kakkarfar soyayya ta kullu, kullum suna tare, a gida ne ko a ofis. Abin ya soma bayyana ga abokan aikin shi da abokan karatun ta, da manyan likitoci mata da ke yi mishi asirtacciyar soyayya. Wannan ya janyo ma Hadiza hassada karara a wajen mafi yawan abokan karatun ta, to ita ma sai ta share su, saboda ta san Surayyah kadai ke kaunar ta saboda Allah. A uren su, wani abu ne da ya bar dimbin tarihi a asibitin Malam Aminu Kano, domin mafi akasarin likitocin cardiology kabilu da Hausawa sun halarta. Ba a taba ganin daurin auren da ya tara ‘yan boko tsantsa, likitoci ziryan a unguwar Karkasara irin na Hadiza ba. Suka tare a gidan Sulaiman da ke cikin asibiti, cikin wata irin soyayya mai wuyar fassarawa. Aure ne auren soyayya mai tsabta, wanda babu ha’inci, yaudara ko karya a cikin ta. Ya sha mamakin samun Hadizah a cikakkiyar mace (birgin) musamman in aka yi la’akari da matakin karatun ta. Ba gaskiya bane zargin da ake yiwa ‘yammatan (medicine), kawai dan iska dan iskan kansa ne, amma da yawa abin da ya kai su shi ne a gabansu. Cikin shekaru uku da auren su ta yi mishi tukuicin kauna da Munib da Muniba, wannan ya kara sayowa Hadiza matsiyaciyar kauna a zuciyar Sulaiman. Daga baya ne da ya kammala ginin da yake yi a Janbulo suka koma, daga nan ne likitocin aka rufe bakin mahaifa ruf, aka _ fuskanci cigaba. Hadiza ta kare karatun ta cikin nasara, da taimakon mijinta. Ita ce (oberall) a year din su. Da gudu aka rike ta a (labour room) wato dakin haihuwa. Sannan ba ta tsaya a nan ba, ta ci gaba da halartar kwasai-kwasai a akan bangaren ta. Har kawo matakin da ta ke kai a yau, na cikakkiyar likitar mata. 2K 2K OK Karfe hudu na yammacin ranar litinin aiki ya tsagaitawa Dr. Hadiza, babu yawan marasa lafiya, don haka ta soma hada ‘yan komatsanta don barin asibitin. Tun safe yau kanta ke damun ta da ciwo, gida kawai take so ta Je ta huta. Amma dole sai ta fara ganin Sulaiman tukunna, akwai wasu kudi da take son karba a wajen sa za ta biya ta kai ma Fati tayi (registration). Ta bude motar ta kenan ta zuba shirgin hannun ta, wata Nurse ta karaso da gudu tana haki tana kiran ta, “Dr. Hadizah!” Ta juya tana kallon ta har ta karaso. ” leeees Don Allah ki taimaka, wata ce aka kawo yanzun nan da alama ba za ta iya haihuwa da kanta ba, sai bleeding (zubar jini) take”. Ta
Table of Contents