Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Yakanah Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

ya dafe kai, Hadiza na kuka a hankali tana kara hargitsa shi, ya ce a fusace, “Enough…….is enough Hadizah! Ki gaya min fisabilillahi mene ne babbar matsalar ki?” Ta ce, A mamakance ya maimaita “Panadol?” “Eh”. Ya ce, “You are silly ko in ce you are nonsense Doctor! I did not beliebe YOU… “(kina shirme, ke shashashar likita ce, ban yarda dake ba). Ya tashi a fusace ya fizgi waya ya kira Dr. Bashir, ‘consultant’ na ‘psychiatrist’, Surayya ce ta dauka, bai ko amsa gaisuwar da take mishi ba ya ce, “Ina mijin ki?’ Ta amsa “An kira shi a ‘emergency’ kuma ‘he is on call’ yanzu ya fita, ya manta wayar”. Ya kashe wayar ya cillar ya zauna a gefen gado ya dafe kai, Hadiza na kuka a hankali tana kara hargitsa shi, ya ce a fusace, “Enough…….is enough Hadizah! Ki gaya min fisabilillahi mene ne babbar matsalar ki?” Ta ce, “Nifa na gaya maka laulayin ciki ne, Sai migraine wanda ba yau na fara ba, kuma ka san shi dama ina da magungunan da nake sha a kan shi, wannan zazzabin da haraswa laulayin ciki ne irin wanda na saba, zan gaya maka karya ne? Yau da bakin ka Sulaiman kake cewa baka yarda dani ba?” Jikinsa ya dan yi sanyi, ya rage sauti ya ce, “To ta ya ya zan ce zan kira likita da ya san matsalar ki ya duba ki ki ce a’a? Sai in dauka wani abu ne daban kike boye mini”. Ya yi mata wani irin murmushi da har abada ba zai gushe daga zuciyarta ba, ta dauke kai alamar ta yi fushi. Ya bi bayan ta a hankali ya kwanta, suna raba zazzabin tare. Akwai wani abu wai shi ‘hot kiss’ da Hadiza ba ta sani ba daga Sulaiman sai a yau, ya mantar da ita rashin lafiyar ta, ya dauke ta ya jefa a duniyar soyayya, ta manta cewa ita nakasasshiya ce, ta manta damuwar ta na cewa lafiyarta na hannun Allah, ta dauka cewa, tana a Dr. Hadiza ne ta baya. Ba za ta mance da wannan ranar da Sulaiman ya zubar da hawayen shi a karo na biyu a kanta ba. Na farko saboda ta nakasa, na biyu na dimbin soyayyar da yake yi mata. To wanne ne zai kasance na uku??? 2K KK OK I nna ba ta koma Bakori ba sai bayan watanni biyu, lokacin laulayin Hadiza ya ragu, tana yi mata dabaru irin na manya har ta samu sauki. A lokacin cikin ya shiga wata hudu, sannan ne laulayin ya tsaya. Sannan ciwon kanta ya jima bai tashi ba, saboda Dr. Bunza ya sauya mata magani, Fati ce ke zuwa ta karbo ba tare da sanin Sulaiman ba. Ganin ciwon ya dade bai tashi ba sai Hadiza ta watsar da shawarar Fati ba ta gayawa Yaya ba, shi dama SuJaiman tuni ta binne shi ya kuma yarda cewa migraine take. Cikin Hadiza wata bakwai, ya fito ya yi tororo kamar watanni tara. Haka za ka ganta fus! A cikin wheel chair tasa cikin a gaba tana kallo tana mamakin sarautar Allah, wanda ya ga damar ta haihu a cikin halin da take ciki. So da kulawa wurin Sulaiman kamar ya yi mata nakuda. Watan Aprilu ya kama, wanda ya yi dai-dai da EDD din ta, cikin dare wani azababben ciwon kai ya tashe ta, ta soma bubbuga kanta a jikin gado, kafin a yi haka ta yi dogo suma jini ya kece kamar da bakin kwarya. Duk wani kokari da zai iya shi ne kiran Dr. Abdullahi ko Dr. Surayyah a waya, amma hannun shi ya kasa kama wayar saboda dimaucewa. Sannan shi ya manta kansa balle ya yi tunanin wane irin taimako zai ba ta a matsayin shi na cardiologist wanda kuma ke da general knowledge a kan komai. Sai ya sunkuto ta ya nufo harabar gidan, ya shimfidar a bayan mota. Malam Ilu ya wangale mishi ‘gate’ ya fita, cikin ranshi yana cewa kai wan nan yarinya kina cikin jarrabawa kalakala, Allah ya baki lafiya. Da taimakon innalillahi…….. da yake ta ambato ya samu nutsuwar da har ya iso AKTH, aka karbe ta a bangaren ta wato dakin haihuwa, su Dr. Surayyah, Dr. Abdullahi suka rufu a kanta, ba ta san inda kanta yake ba. Suka soma ba ta duk wani taimako da ya dace don ta haihu da kanta kamin su yi bincike a kan wata matsala daban da suka hango wadda da alama dadaddiya ce. Amma duk iya kokarin su sun tabbatar da ba za ta iya haihuwa da kanta ba, don haka suka miko mishi takardu don ya sanya hannu a shiga da ita tiyata. Da kyar yake iya sarrafa ‘yan yatsun shi a lokacin da yake rattaba hannun, zuciyar shi ta riga ta bushe da tashin hankali. Yana tsaye aka turo ta a kan gadon daukar marassa lafiya zuwa dakin tiyata, bai yi tunanin gayawa kowa ba sai da safe, kasancewar ba shi da nutsuwar yin hakan. Da ya ga wannan ba za ta yi mishi ba, sai ya nufi ofishinsa ya murda kofar ya shiga, ya jingina da kofar ya soma tunanin wasu al’amura da ya lura Hadiza na boye mishi, da yawan waya da take yi da Dr. Bunza na mene ne? Sannan da kwayoyin maganin da ya gani a leda babu suna babu takardar su a karkashin gadon su. Ya yi wani irin huci mai zafi, “Akwai wata matsala wadda da alama dadaddiya ce”. Ya tuno furucin Dr. Abdullahi. A sukwane ya bude kofar ya fita ya nufi ofishin Dr. Bunza a psychiatry. Dr. Bunza na rubuce-rdubuce a file suna hira da Dr. Karaye, Dr. Sulaiman ya bankada kofar ofishin ba tare da ya yi sallama ko neman izinin shigowa ba, ya kai wa Dr. Bunza shaka ya ce, “Gara in kashe ka, kafin ka kashe ni….”. Dr. Karaye ya soma kokarin kwatar Dr. Bunza wanda ya sha_ shaka matuka, duk idanun sun yo waje. Ya ce, “Ba zan cika shi ba, sai ya gaya min abin da ke damun matata, da magungunan mene ne yake dirka mata?” Dr. Bunza ya ce, “Ka yi hakuri Dr. Sulaiman mu yi maganar cikin nutsuwa”. Ya samu ya sake shi da kyar ya koma kujerar sa yana gyara wuyan rigarshi, yayin da Sulaiman ya yi mishi kerere a kai, idanun shi a jujjuye, shi dai kawai so yake ya ji mene ne matsalar Hadiza? Dr. Karaye ya ce, “Ka yi hakuri ka zauna Dr. Bakori, Dr. Bashir ba zai cuce ka ba…… – Ya juyar da juyayyun idanunsa a kan Karaye, “Akwai wata cuta wadda ta wuce wadda ya yi min? Matata na dauke da cuta shekara guda amma bai taba gaya min ba? Ya biye mata suke yi min rainin hankali, na yi kama da wanda bai je makaranta bane Dr. Karaye?” Dr. Bunza ya ce, “Ba haka bane Dr. Bakori, ina bisa aikina ne, akwai sirri tsakanin likita da petient din sa, wannan shi ne hujja ta. Sannan Dr. Hadiza na da tata huyar, ta boye maka cewa tana da (brain cancer) don samar maka da kwanciyar hankali, ta ce idan ka ji babu kai babu sauran kwanciyar hankali, kuma nima na yarda you are not taking things

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18