Chapter 16
Chapter 16
ciki har da madarar SMA da Nana ke sha, ya kwalawa Fati kira ta fito ya bata. Sai a sannan ya lura da bakin takalma har da na namiji a kofar dakin Yaya, ya ce da Fati, “Waccan madarar ta kare ne?” Ta ce, “Eh, saura kadan”. Ya ce, “To ki dinga gaya min kafin ta kare ba sai ta kare kaf a barta tana kuka ba”. Ta ce, “Ai masassara take shi ne take kuka, amma dama gobe zan kaita asibiti”. Ya ce, “To Allah ya sauwake, ke kuma Allah ya ba ki ladan hidimar da kike yi da ‘ya’yan ki, ya sa suji kan ki kamar yadda kika ji kan su, ya kai rahama kabarin mahaifiyar su”. Ta ce, “Amin Baba”. Shi ma Sulaiman da ke can daki yana jin su ya ce “Amin”. A zuciyar shi. Malam ya daga labulen ya ce, “A’a! Ashe Inna ce, barka da zuwa kin sha hanya, ya ya aka baro Malam?” Ta amsa, suka ci gaba da gaisawa suna hirar ‘yan jikokin su, tare da kara yiwa juna ta’aziyya. Malam Ja’afar ya dubi Sulaiman sosai ya ce, “Ina maganar aiki ta kwana?” Ya yi shiru kanshi a sunkuye, can kuma ya ce, “Zan koma gobe insha Allahu”. Malam ya ji dadi, ya kara mishi da nasiha mai sanyaya zuciya. Ba su baro gidan ba sai karfe biyar na yamma, bayan Inna da Yaya sun yanke shawarar yaran za su ci gaba da zama a nan saboda ya fi kusa da makarantar su. Har za su tafi ya dubi Yaya ya ce, “Duk abin da ake bukata Yaya, don Allah a gaya min”. Yaya ta yi murmushi ta ce, “Me ake bukata ban da madara? Bayan ita babu abin da zai gagara da izinin Allah”. Ya ce, “Duk da haka ina son sanin sauran abubuwan da ake bukata, ai ragi-ragi ne”. Ta ce, “To ka tambayi Fati”. Ba don ranshi ya so ba ya nufi kofar dakin nata. hijabin a jikinta, kwayar idanun su ta hadu, ya yi saurin dauke kansa don gani ya yi kamar Hadiza, hatta digon tauwadar Allah da ke kan tsinin hancin Hadiza akwai shi a tsinin hancin Fati. Zuciyar shi ta yi wani irin mummunan bugu, don gani ya yi tana rikide mishi Hadiza sak, kasancewar bai taba ganin ta babu hijabi ba. Ya tsaya daga bakin kofar hannun shi duka biyu zube cikin aljihu. Da kyar yake magana kamar an tilasta mishi, ba tare da ya kara kallon ta ba. “Na tambayi Yaya abubuwan da yara suke bukata, ta ce in tambaye ki?” Kanta a kasa ta ce, “Sai ko pampers da madara”. Yace, “Bayan su ba wani abu?” Ta ce, “Eh, amma malamar su ta ce akwai prize gibing day ranar asabar kuma ana son iyayen yara su je”. Sannan ta dauko report card na yaran na wannan zangon ta mika masa. Garin karba hannayen su suka gogi juna, sannan suka kara hada ido a lokaci daya babu wanda bai jia jikin sa ba. Ita tsoro ta ji, shi kuma ji ya yi kamar hannun Hadiza. Bai ce komi ba ya karba ya sanya a aljihun shi ba tare da ya duba ba, bai kuma ba ta amsar zai je ko ba zai je ba ya fita. Ya tadda Inna har ta fito suka tafi, ya bar Fati cikin tunani. Ta zauna a gefen gadon ta, ta sauko Nanah wadda ta samu barci ta rungume cikin hannayen ta, tana tunanin me Hadiza ke nufi da ta ce ta kula da Baban Munib? “….Munib kulawar Uwa yake nema, Sulaiman kulawar MATA yake nema….”. Ta tuno kalaman Hadiza. To ai ita ba matar shi ba ce, ba gidansu daya ba, ta ina za ta kula da shin kada rashin Hadiza ya tagayyara shi? Wannan baudadden mijin nata dake yi mata kiyayya maras dalili? In har Hadiza na nufin ta auri mijinta ne wanda ba ta fito baro-baro ta fada ba, sai hannunka mai sanda da ta yi mata, ta hada ta da wani al’amari da ba zai taba yiwuwa ba. Ba ta fata, kuma kada Allah ya tabbatar ta yi tarayya da Hadiza a kan abin da take so, ta tafi ta bari ba don ba ta so ba, sai don hukuncin Allah wanda ya fi karfin dan adam ya yi jayayya da shi. Hakika ta dauki alkawarin da ba ta san yadda za ta yi ta sauke shi ba. kK WwW ashegari da yamma sai ga Inna ta kara dawowa, Dr. Sulaiman ya kawo ta, Hamza da Abdulyassar suka shigowa Fati da katon na madarar SMA, katon na diapers da himilin shopping na kayan masarufi da kayan biskit da choculate da su Indomie wanda su Munib ke zuwa makaranta da su. Ta adana kowanne a inda ya dace, Inna ta ce ya je sai dare ya zo ya dauke ta. A lokacin Malam Ja’afar ya iso da shi da Inna da Yaya suka kule a daki, suka sakayo kofa, me suka ce me suka ce oho, sun dai dade suna magana kafin ya dawo ya dauki Inna su wuce, kasancewar a gobe zata koma Bakonri, ya biya ta Jifatu ya yi mata sayayya mai yawa kamar yadda ya saba, ita da Malam da sauran kannen shi, suka wuce gidan sa. Inna ta tuka mishi tuwon semobita da miyar ganye ya ci, ta takura mishi ya bude wayoyinsa. Yana budewa sakonnin ta’aziyya daga |ikitoci ‘yan uwansa da sauran abokan arziki ya soma tittidowa cikin wayar. Sannan ana neman shi a ofishin (Chief Medical Director) na AKTH ranar litinin. Don haka yana kai Inna Bakori suka gaisa da mahaifin shi bai tsaya ba. Da zai tafi Inna ta ce, “Ni kuwa akwai wata magana muhimmiya da nake so mu yi, ga shi na ga alamar kana sauri”. Yace, “Gaskiya kam ina cikin sauri, sai ko idan na dawo”. Ta ce, “Shi ke nan Allah ya kiyaye hanya, ya kara maka hakuri da YAKANAH, ya shige maka gaba a kan al’amuran ka, ya yi maka musayan alheri”. Har ransa ya ji dadin addu’o’in Inna, wata nutsuwa ta kara shigar shi, son mahaifiyar shi ya kara shigar shi. Ta ce, “Ina so zuwa sanda za ka dawo in ga canji, kamar yadda ka yi min alkawari, in ganka a likitanka ba mai sunan Malam ba”. Murmushi ya yi, wanda rabon shi da yin shi tun wani karni can da ya shude. RR KK L itinin, ya isa ofishin CMD, sun dade suna tattunawa a kan wani aiki na dashen zuciya da za a yiwa ministan lafiya. Yana daya daga cikin likitocin da zasu gabatar da aikin. Ya koma office dinsa ya daidaita komai ya ci gaba da aikin sa, cikin karfin zuciya da neman rinjaye a kanta. Sai ya zamto yana jin dadin aikin sosai, don yana debe mishi kewa, yana hana shi zama shiru har maraicin matarsa ya gallabe shi. Ya tarar da tulin ayyuka da yawa, don haka ya zamo busy a satin gaba daya. Ranar alhamis ya saci jiki ya je yayowa ‘ya’yan shi siyayya ya biya ta makarantar su ya gansu, lokacin da aka fito cin abinci, a karkashin wani benci ya zauna ya rungume su suna ta labari, ya bude ‘kit-kat’ yana basu suna ci
Table of Contents