Chapter 15
Chapter 15
amma bai fasa kwana yana yiwa Hadiza addu’a ba. Uwa, mahaifiya, duk ta rasa sukuni, tana can Bakori, hankalinta na Kano, ta san cikin kowanne hali Sulaiman yake yana cikin halin da yake neman matallafi. Kuma cikin halin da yake bukatar mai tausar sa, nuna masa kauna da kulawa. Don haka yau ta tambayi Malam Sulaiman cewa za ta taho Kano wajen Sulaiman. Ya ce hakan ya yi. Yana zaune a falo, daga shi sai wata dukunkunanniyar jallabiya ruwan makuba, da kofin ‘tea’ a hannun shi da ‘remote’ yana_ = kallon _tashar Saudiyyah, inda suke gabatar da sallar magariba. Aka danna kararrawa wajen sau biyar kamin ya yunkura ya aje kofin a kan side table ya bude kofar. Inna Halima ce tsaye cikin atamfa holland ta sha lullubi da koren mayafi kalar atamfar ta, har ranshi ya ji dadin ganin ta, ya ba ta hanya ta wuce cikin falon, ya tsuguna ya gaishe ta. Ba ta amsa ba sai kallon shi take cikin al’ajabi, “Haka ka lalata kanka Sulaimanu saboda Allah? To wannan rashin tawakkalin da kake shi zai dawo da Hadiza duniya ko me? Ka sani Hadiza ta riga ta koma ga mahaliccin ta, ba za ta taba dawowa ba, ka fuskanci rayuwar da take jiran ka a gaba, ka zamo mai YAKANAH cikin duk halin da ka tsinci kanka. Tsakanin ka da Hadiza yanzu addu’a ce, ba wannan lalata rayuwar ba. Idan Hadiza tana raye, ba za ta so ganin ka haka ba, ka yi hakuri mai sunan Malam. Shin yaushe rabon ka da cin abinci?’ Ya sunkuyar da kai bai yi magana ba. Ta jawo ledar da ta shigo da ita ta fiddo ma’adanan abinci guda biyu, ta bude ta tura masa, tuwon shinkafa ne lafiyayye da miyar taushe ta ji nama zuku-zuku, ta ce, “Cinye maza ka bani kwanon”. Ba musu ya dauka ya soma ci kamar Allah ya aiko shi. Inna ta mike ta soma tattare bolar falon, ta share shi tsaf, ta shiga dakunan ta gyare ko ina, ta wanke masa toilet. Sanda ta gama ya dade da yin barci a carpet, ta zauna a gefen kansa tana tofa masa addu’a. Yana tashi ta ba shi rubutun da ta zo da shi cikin jarka ya sha, ya mai da kai kan tuntun ya koma barci. Bai tashi ba sai la’asar, ta je bandaki ta hada mishi ruwan wanka cikin kwami, ta dawo falon ta same shi ya idar da sallar la’asar, ya mike kafa yana kallon ceiling, ta tsuguna a gabansa ta ce, “Tashi ka je ka yi wanka, ka shirya muje mu ga mai sunan Hadiza”. Wannan karon ma bai yi musu ba, ya mike ya je ya yi wankan, ya zubo farar shadda dinkin Mohammed, ya dora hula fara sol amma bai fesa turare ba, ya fito ya tadda Inna ta idar da sallah tana lazimi. Ta yi addu’a ta shafa, ta mike suka fito harabar adana motoci, duk motocin sun yi kura futuk! Alamar an dade ba a taba su ba. Ya sa key ya fiddo motar dai-dai inda Inna take, Malam Ilu ya karaso da sauri ya gaida Inna, ya sa ‘duster’ ya karkade motar cike da jin dadin ganin yau Ubangidansa ya fito, wanda yake kwana cikin wannan gida shi kadai ransa, sai dai yana tausaya masa, don ya san rashin matar kwarai kamar Dr. Hadiza ba karamin abu bane. Inna na baya shi kuma yana tukin suka nufi unguwar Karkasara. A dai-dai titin asibitin AKTH kamar an ce da Inna ta juya, ta hango Fati rike da hannun Munib da Muniba cikin kayan makaranta tana tare tasi, da alama ta dauko su ne daga makaranta. Da sauri Inna ta ce, “Ka ga Fati can tana tare mota, yi kwana mu dauke su”. Ya yi kamar bai ji ba, ya karawa motar shi gudu. Inna ta yi salati ta ce, “Baka ji ni bane? ‘Ya’yan ka fa ta dauko daga makaranta!”. Sai a sannan ya juya, tuni ta tare tasi suna kokarin shiga. Ya ce, “Ai sun shiga mota ma hadu a can”. Inna ta yi shiru tana mamaki, har suka iso gidan su Fati ba su shigo ba, don ba za ka hada motar gida da ta haya da ke yin tsaye-tsaye ba. Tun daga soron gidan yake jiyo kukan Baby Nana Khadijah. Ya rintse ido tsigar jikinshi na tashi. Inna ce ta yi sallama ya biyo bayan ta. Yaya suka tarar tana ta fama da Baby Nana, wadda ke ta tsandara kuka kamar ta tsaga gidan ta ki karbar madarar da take bata. Ta amsa musu sallama cikin sakin fuska da walwala, ta shimfida musu sabuwar tabarma, sannan ta mikawa Inna Baby Nana. Yaya ta dubi Sulaiman ganin yadda ya rame ya yi kasumba, sai ta ji hawaye sun ciko idon ta. Ta ce, “Me nake gani haka ni Sa’adatu? Su Da sauri Inna ta ce, “Ka ga Fati can tana tare mota, yi kwana mu dauke su”. Ya yi kamar bai ji ba, ya karawa motar shi gudu. Inna ta yi salati ta ce, “Baka ji ni bane? ‘Ya’yan ka fa ta dauko daga makaranta!”. Sai a sannan ya juya, tuni ta tare tasi suna kokarin shiga. Ya ce, “Ai sun shiga mota ma hadu a can”. Inna ta yi shiru tana mamaki, har suka iso gidan su Fati ba su shigo ba, don ba za ka hada motar gida da ta haya da ke yin tsaye-tsaye ba. Tun daga soron gidan yake jiyo kukan Baby Nana Khadijah. Ya rintse ido tsigar jikinshi na tashi. Inna ce ta yi sallama ya biyo bayan ta. Yaya suka tarar tana ta fama da Baby Nana, wadda ke ta tsandara kuka kamar ta tsaga gidan ta ki karbar madarar da take bata. Ta amsa musu sallama cikin sakin fuska da walwala, ta shimfida musu sabuwar tabarma, sannan ta mikawa Inna Baby Nana. Yaya ta dubi Sulaiman ganin yadda ya rame ya yi kasumba, sai ta ji hawaye sun ciko idon ta. Ta ce, “Me nake gani haka ni Sa’adatu? Sulaiman me ya yi zafi? Hadiza ba ta yi gaggawa ba, muma jiran namu wa’adin muke. Karbi ‘yarka tunda ta zo duniya baka taba daukar ta ba, ita kuma laifin me ta yi? Ka zamo mai YAKANAH, wannan ba shi ne karshen rayuwar ka ba!!”. Inna ta mika mishi yarinyar, ya fi karafin mintuna uku kamin ya karbe ta, ya kura mata ido yana mamakin kamannin shi da ita har sun fi nashi da Munib. Dai-dai sanda Fati da yaran suka shigo cikin sallama, tana sanye da katon hijabin ta har kasa mai hannaye, rike da lunch bod din yara da jakunkunan su. Cikin nutsuwa ta tsuguna har kasa ta gaida Inna, ba tare da ta kalli Sulaiman ba ta ce, “Ina wuni?’ Bai amsa ba, ita ma ba ta tsaya sauraron ya amsa ba ta wuce ciki. Ai Munib da Muniba suna ganin Baban su suka fada mishi suna ta tsallen murna, ya mikawa Inna Baby ya zaunar dasu duka a cinyoyin sa, suka soma ba shi labari iri-iri, duka rabi ‘AUNTY FATI’ ta yi mana kaza, ta yi mana kaza. Yana jinsu bai ce komi ba. Malam Ja’afar ya shigo hannayen shi rike da manyan ledoji yayo cefane
Table of Contents