Chapter 1
Chapter 1
YAKANAH!- Agogon ‘alarm’ da ke gefen makeken gadon ya buga karfe shidda dai-dai na safe, Dr. Hadizah wadda ke kwance a gadon doguwa ce ba can ba, irin tsayin nan gare ta mai tsari da ban sha’awa. Tana sanye cikin rigar barci mai santsi fara sol. Ta yi mika a hankali tare da koro addu’ar (Alhamdulillahil lazee ahyana, ba’ada ma amatana wa ilaihin nushour). Ta mika hannu side din da maigidanta ke kwance, wayam! Tayi hanzarin mikewa daga kwanciyar don a zatonta, ta makara. Daga can kitchen ta jiyo motsin mai aikinsu Goggo Alti tana karakaina da kwanuka. Tana shirin mikewa ta ji motsin maigidanta Sulayman a shower, don haka ta yi ajiyar zuciya mai sanyi, a kalla ko ta makara kadan ne. Ita ma ta fada bandakin don ta taimaka mishi wajen wanka. Suka fito kowane daure da towell, shi iya kugun shi ita iya cinyoyin ta. Jiki ne da ita lukui-lukui kamar atafa. Jiki ne da shi na MANYA, kuma kasaitattun maza, wadanda suka dama, suka kutsa cikin ilimummuka daban-daban. Yana da duhu, amma duhun mazan Marocco ne. Dogo ne sosai ma’abocin karfi da kyawun sura ta ko’ina. Idan baka san asalin shi ba, za ka yi tsammanin ya fito ne daga Sirreleone, amma a zahiri Bakatsine ne dan asalin garin Bakori. Wadda Bakorin ta bi sunan shi, ta boye Sulayman-Sulayman din, ake kiran shi Dr. Bakori. Ta bude wardrove ta dauko mishi bakaken Spanish-Suit mai hade da farin tie mai santsi. Ita kuma ta fiddo wata atamfa super shudiya mai ratsin rowan hoda da_ hasken – sararin samaniya, riga, zane da kallabin su, ta dora da farar rigar su ta likitoci. Tuni ta fito a Dr. Hadizarta. Tana tsuke mishi tie ya ja zankalelen dogon karan hancinta in appreciation din (cike da jin dadin) irin kulawar da take mishi. Yace “Allah ya bar min ke Dr. D.Z”. Ta ce “‘…Ya bar min kai nima, likitan zuciyata…..”.. Ta manna mishi kyakkyawar sumba a kirji, kasancewar ya kere ta a tsaho, ita iya kirjin shi ce. Ta dauko tashi rigar likitocin ta zagaya ta bayan shi ta rufa mishi, ya zura hannun shi kana a hankali ya janyo ta ya rungume ta. Sun dau tsawon lokaci a hakan, suna sakin ajiyar zuciya mai sanyi cike da matsananciyar kauna wadda biro ba zai iya rubutawa ba, kamin su saki juna ba don sun so ba, sai don tunanin dimbin al’umma masu larura da suka yi sammako suke jiran su. Sai da suka gama kammalawa tsaf sannan suka fito, tana rike da gilashin idonta a hannu, ya yin da shi yake rike da jakarta da brief case din shi. Kai tsaye dakin yaransu suka nufa, inda suka tarar tuni Alti ta shirya su tsaf, kasancewar yau garin an tashi da lullumin sanyi mai tsanani ya sanya ta sanya musu rigar sanyi mai kauri a ciki, ta sanya musu fararen socks ta rufe musu kafafu cikin farin cambas. Yaran su biyu ne mace da namiji, namijin dan kimanin shekaru hudu, macen ‘yar kimanin shekaru biyu da kadan. Dole in ka gansu sai ka sake marmarin kallon su, sun kuma baka sha’awa. Munib sak Babansa, yayin da Muniba komi nata na Dr, Hadiza ne. To ba Mamin ba, ba Daddyn ba, kowanne ji yake da kyau tamkar shi ya yi kansa. Akwai shakuwa, fahimta da soyayya mai yawa a tsakanin wannan family. Hadiza ta rage tsawo ta russuna ta rungume Muniba, “Gud morning my dear……. “Morning Mummyy….”. Munib ma ya ce “Gud morning Daddy…..”. Ya amsa da “Morning my Munib, an tashi lafiya?” Su dukka suka nufi tebir domin yin kalaci. Goggo Allti ta fito daga kitchen za ta wuce bangaren ta, daga Hadiza har Sulayman suka gaishe ta, kamin ita ta gaida su. Wannan dabi’arsu ce da ke karawa dattijuwar jin dadin zama dasu, saboda yadda suke ba ta girma kamar ba a karkashin su take ci ba. Hakan ne yake kara mata himmar kula musu da yaransu saboda Allah. Hadiza ta bude ma’adanan abincin ta soma serbing kowannen su da abinda yake so. Sinasir ne da miyar ganye, sai farfesun kayan ciki, sai kuma soyayyen dankali da kwai domin su Munib da bazasu iya cin mai nauyin ba. Ga al’adarsu sun fi cin abinci mai nauyi da safe, don ba za su kara ci ba sai dare in sun dawo aiki, sai ‘yan ciye-ciye da ba a rasa ba a office. Hankalin Dr. Sulaiman yana kan ‘ya’yan shi, sai da ya tabbatar sun koshi sannan ya ci nasa. Zuwa bakwai da rabi sun gama komai sun fito, suka yiwa Goggo Alti sallama suka wuce rumfar adana motocin su. Akwai motoci har guda uku, daya ta Sulaiman, daya ta Hadiza, daya ta amfanin gida. Sai da suka aje yaran a makarantar su (Maitama Sule) da ke dab da asibitin da suke, wato (AKTH) sannan suka karasa cikin asibiti, kowanne ya nufi bangaren sa. Dr. Sulaiman-Sulaiman Bakori shi ne consultant na (cardiology), yayin da Dr. Hadiza Ja’afar Mai-Yadi take likitar mata wato (gynaec) a labour ward take. Sai da ya fara sauke ta sannan ya wuce ofishinsa, ya soma attending dimbin cases din da ke gabansa. Karfe sha biyu na rana ya zame ya je ya debo yara ya kai ma Goggo Allti, sannan ya dawo. Wannan shi ne tsarin rayuwar su a kullum. AK S hekarun su biyar kenan da aure, amma har zuwa inda yau ke motsi, babu abinda ya canza na daga soyayyar da suke yiwa juna, sai ma abin da ya karu. Hadiza dalibar shi ce irin yaran likitocin nan da ake koyarwa a (teaching hospital). Ya fahimce ta yarinya ce mai matukar kwazo a tsakanin tsararrakin ta. Wani abin mamaki da ya fara bincike a kanta ‘yar talakawa ce likis, amma iyayenta sun tsaya tsayin daka wajen daukar nauyin karatun ta, duk da tsadar shi kuwa, da dukkan iyawarsu. Soyayya ce mai tsabta irin ta wadanda suka wadata da ilimi suka gudanar kamin aure. Ga Hadizah ba karamar sa’a ba ce, kuma ba karamin abin alfahari bane samun mutun kaman Sulayman (as a husband). To haka shi ma. Hadiza ta tara duk wasu kualities da yake nema ga diya mace, ga dai kyau ga kyan hali, ga addini da kyakkyawar zuciya, sannan uwa uba ta samu ingantacciyar tarbiyya daga_ iyayen kwarai. Iyayenta suna nan a_ unguwar Karkasara dake cikin birnin Kano, sana’ar mahaifinta shi ne yadiddika yake sayarwa, yana da shago a nan kantin Kwari. Hadiza ita ce ta biyu a cikin ‘ya’yan gidansu, akwai Yayanta Mukhtar wanda ke aiki da (Zenith Bank) a Kaduna, kusan da tallafin shi ne Hadiza ta samu ta kammala karatun ta. Duk da haka shi ma mahaifinsu a tsaye yake a kan karatun su, don yaga amfanin da karatun yayiwa Mukhtar. Sai kanwar ta Fati, budurwa ce ‘yar ki manin shekaru sha bakwai, a bana ne ta kammala karatun sakandire. Sai Hamza da Yusuf, da dan autan su Abdulyassar. Duk cikin kannenta Hadiza ta fi son Fati, wata irin yarinya ce mai sanyin hali, sanyin kyau da sassanyar zuciya. Akwai wata irin shakuwa ta musamman tsakanin Hadiza da ‘yar uwarta Fati. Jininsu ya hadu sosai ta yadda Hadiza ba ta iya shawara da kowa kan al’amuranta kamar Fati saboda hankalin ta. Fati
Table of Contents