Chapter 17
Chapter 17
suna yi mishi hira. Tun suna damuwa da rashin Momin su har sun hakura sun dangana sun daina tambayar ta. Munib ya ce, “Daddy ba ka zo (prize gibing) din mu ba, kowa Baban shi ya zo banda mu”. Ya kama kunnen shi cikin nunawa yaron amsa laifin sa, ya ce, “I am bery-bery sorry….. aiki ne ya yi min yawa. To wa ya kawo ku?” Suka ce, “Aunty Fati, ta yi mana kwalliya ta kawo mu”. Ya ce, “Aunty Fati ta kyauta!”. Suka yi murmushi. Ya ce, “Nedt year ba zan sake ba”. Aka kada kararrawar komawa aji, suka fella da gudu suka nufi ajinsu, ya bisu da kallo yana murmushi cike da kewar su. Hakan yake yi duk sanda ya samu sararin aiki, ya daina zuwa gidan don kar ya ga Fati, tana tuno mishi da wasu al’amura msu yawa a kan Hadiza. Sannan ba ya son wata alaka take shiga tsakanin su, shi ma kuma bai san mai ya sa ba, ya danganta hakan da rashin haduwar jini. Ita kuma ta danganta hakan da wulakanci da raina mata wayo, yana ganin ta kamar ba ta san abin da take yi ba, bayan in da wanda ya san ciwon kansa a duniya to ita ce. Sai dai tsarin rayuwar su da ya banbanta, kowa da irin nashi tsarin rayuwar, don haka ita ma ta yi kamar ba ta san yana zuwa makarantar yaran ba, bayan kuma suna gaya mata. Ana i gobe sadakar arba’in din Hadizah, Malam Sulaiman, Inna Halima da Baffanin Sulaiman guda biyu, Malam Surajo da Alhaji Umar suka iso gidan Sulaiman a Kano, a daren suka bukaci ya kai su Karkasara. In da ya ajiye su da daddare ya wuce asibiti, da cewar zai dawo ya dauke su. Manya sun kule a falon Baban Hadiza, wato Malam Ja’afar suna magana ta hankali har da Yaya da Inna. Yaya ta ce, “Ni bana jin Fati sai shi Sulaiman, anya zai yi na’am da al’amarin nan?” Malam Sulaiman ya yi murmushi ya ce, “Kune baku san Sule ba har yanzu, yana da wani hali tun yana yaro, abin da zai so sai ya fara kin shi tukunna. Ga yadda mahaifiyar shi take bani labari, babu jituwa ko ya ya tsakanin sa da Fati, ita kuma ta kama kanta ba ta shiga shirgin shi. Mu dai burin mu ku bamu hadin kai, Allah ya gani muna son zuri’ar gidan nan, muna son zumunci ya ci gaba da gudana kamar yadda aka faro. Fati ita ta fi cancanta da ta rike ‘ya’yan ‘yar uwar ta, don a wannan zamanin da wuya a samu macen da za ta rike maka ‘ya’ya har uku duk son da take maka. Sannan mun yaba da hankali da tsarin rayuwar Fati, muna sa ran yara za su tashi da kyakkyawar tarbiyya har zuwa girman su. Fati ba za ta dauwama a gida tana bautar ‘ya’yan ‘yar uwarta ba, dole watarana za ta yi aure. Ranar da hakan ta faru ya ya Sulaiman zai yi da yaran nan? Ga shi suna karatun su mai kyau a nan balle mu tafi dasu Bakori. Fati ita ta fi cancanta da ta maye gurbin ‘yar uwarta a zuciyar Sulaiman. Don haka muna neman hadin kanku, yardar ku da amincewar ku Malam Ja’afar. Shin an bamu Fati? Da karfin mu muka zo, gobe muke so bayan an shafa addu’ar Hadiza a daura auren Sulaiman da Fatima”. Malam Ja’afar ya ce, “Tun kafin ku yi wannan tunanin na riga ku yin sa, kun dai riga ni furtawa ne. Tabbas duk matar da Sule zai aura nan gaba ta rike mishi marayun shi ba kamar Fati ba, wadda ta san ciwon su, tasan ciwon ‘yar uwarta. Sannan Hadizah ta yi wani abu a ranar da za ta koma ga mahaliccinta, wanda ya tsaya min a rai kwarai, ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, sai dai ban ji me suke cewa ba. Fati yarinya ce mai biyayya, ba za ta tsallake umarnin mu ba, amma kamar yadda Sa’adatu ta ce ne, da kyar idan shi Sulaiman din zai amince. Sannan ya wuce matsayin da za ace za a yi mishi aure ba tare da sanin shi ba”. Alhaji Umar ya ce, “Kubar wannan a hannun mu, kamar yadda Fati take mai biyayya, shi ma Sulaiman mai biyayya ne, iyayen shi basu taba saka mishi kara ya tsallake ba. Ina da yakinin zai yi biyayya ga mahaifin shi, kuma a daren nan zamu sanar da shi ba sai gobe ba. Ga sadaki naira dubu ishirin ga goro, daga aljihuna ni waliyyin sa. Jikina ya bani alheri ne zamu kulla, don irin wannan auren na son zuciyar iyaye ba karamar falala ake samu a cikin shi ba”. Kowa ya jinjina kai. Yaya ta ce, “Nima a daren nan zan sanar da ita insha Allahu””, Da haka taron ya tashi, ya yi dai-dai da sallamar Sulaiman a falon, dukkanin su suka amsa fuskar kowannen su cike da walwala da annuri. Malam ya ce, “Faduwa ta zo dai-dai da zama kenan, ita ma Fatiman a kirawo ta”. Yaya ta tashi ta fita don kiran Fati. Tana yiwa su Munib shimfidar kwanciya goye da Nana, Yaya ta yane labulen dakin ta ce, “Fati kin kwanta ne?” “A‘a, ina harama dai”. “To biyo ni dakin Malam yana son magana da ke”. Ta sauke goyon ta zurma hijabin ta, ta bi bayan Yaya har dakin Malam. Ta sha mamakin ganin taron dakin har da Baban Munib, wanda ke can sunkuye da kai a gefe. Ta yi sallama cikin sassanyar muryar ta dukkan su suka amsa, ban da Sulaiman wanda ya fara shan jinin jikinsa kan wannan taron domin shi aka yi. Jikinsa ya yi sanyi, gaban shi ya soma faduwa, haka nan gwiwoyinsa ya jisu kamar an rarrade su da murfin kwano. Ta samu gefen Inna ta zauna, ita ma jikinta ya soma kyarma don ba ta son a tirke ta a cikin mutane. Iyayen dai na duban su suna nazarin kowannen su, sun fahimci dukkan su a firgice suke, amma firgitar ta fi karfi ga Sulaiman. Wannan taro na mene ne? Malam Sulaiman baya _shiga kankanuwar magana. Sai da suka tabbatar sun dan samu nutsuwa sannan Malam Sulaiman ya dubi dansa ya ce, “Mai sunana wani abin alheri ne za mu yi maka, da fatan za ka karba hannu bibbiyu”. Bai yi magana ba, amma ya dago ya dubi mahaifin sa. Ya ci gaba da cewa, “Muna kara yi muku ta’aziyya, sannan muna so ku sani cewa, duk abin da Allah ya tsara akwai hikimar yin hakan a cikin sa. Mun zauna mun yi tunani, mun yi shawara mun yanke cewa, Fati za ta maye gurbin ‘yar uwarta a gare ka, ku ci gaba da raino da_tarbiyyar ‘ya’yanku kamar yadda mahaifiyar su ta fara yi musu, kuma ‘yar uwarta ta karbe ta. Allah ya riga ya hada mu, zuri’a ta hada mu. Don haka Sulaiman bana son ka da wani aure in dai ba jinin gidan nan ne ya kare ba. Za mu yi alfahari daku idan kuka taushi zuciyoyin ku kuka yi mana biyayya. Allah zai nunawa Hadiza har cikin kabarin ta cewa, ke Fati kin rungumi iyalinta, kin rungumi mijinta baki bar rashin
Table of Contents