Chapter 6
Chapter 6
jinni, rai a hannun Allah. Likitoci biyar ne a kan Hadiza, sai Sulaiman cikon na shida, wanda ya manta wani abu wai shi karatun likita, komawa ya yi tamkar bai taba halarta aji ba. Shi da Hadiza da ke kwance babu maraba, illa shi a tsaye yake, sai dai jingine da garu (bango), wanda ya taimaka masa wajen daukar nauyin gangar jikinsa. A lokacin da za ka tsaga ba za ka samu ko digon jini a cikin jikinsa ba. Tashin hankali ba a sa maka rana! Haka wannan mummunan labari ya iske iyayen Hadiza da ‘yan uwanta ta hanyar Dr. Surayyah. A daren Mukhtar ya baro Kaduna zuwa Kano, a daren suka dungumo baki dayan su suka taho, sai dai basu samu ganin Hadiza ba. Har zuwa lokacin likitoci na tsananta bincike a kanta, haka suka kwana a barandar asibiti cikin tsananin sanyi. Fati sai kuka take kamar ranta zai fita tunda suka taho, Yaya na lallashin ta. Sai washegari da safe result din Hadiza ya iske Sulaiman da iyayen ta, bayan raunuka da ba za su kirgu ba, babu karaya ko daya a jikinta. Babban tashin hankalin wanda ya _ girgiza kowa shi ne, jijiyar bayanta wadda ta hada daga wuya zuwa bayan ta (spinal cord) ta tsinke, wanda ke nufin Hadiza ba za ta kara iya mikewa ba, ba za ta kara iya tafiya ba a gaba daya sauran rayuwar ta. Dr. Sulaiman ya mike tsaye ya nuna Dr. Samson da dan yatsa, “Ka san abin da kake fada, ban san cewa baka san aikin ka ba sai yau. Kuma shi ke nan daga yin accident sai ka nakasta min mata? Uwarka ce ba za ta kara iya mikewa ba, amma ba Hadiza ba……” Kai da ganin yadda yake maganar, kwayar idanun shi a juye, ka san ba a hayyacin sa yake wannan furucin ba. Samson ya sunkuyar da kai, duka likitocin babu wanda ya kara magana. Tausayi ne fal a zukatan su. Dr. Hadiza abar so ce ga kowa, suna jin dadin tarayya da ita, marasa lafiyan ta na yaba kokarin ta. Wannan accident da ya yi mata karan tsaye da kuruciyar ta, ya zamo nakasu ga dimbin taimakon da take bai ma al’umma. Malam Ja’afar mahaifin Hadiza da ke gefe shi ya soma tausar Sulaiman da kalami masu dadi da sanya imani, yana tuna masa muhimmancin yarda da kaddara. Sulaiman ya yi shiru, ya koma ya zauna a kujerar sa. Ya kifa kai cikin cinyoyin sa, amma har yanzu ya kasa yarda da abin da kunnuwan sa suka jiye masa. Wai Hadiza ta zama sai dai a kwantar a tayar ba za ta kara amfanuwa ba, ba za ta kara moruwa ba. Balle ta amfanawa kanta komai. Ita da ‘ya’yanta da mijinta sai dai gani da ido. Abin da suke gani kullum yana faruwa da al’umma yau Allah As-Samadu ya juyo da shi kansu. Dimbin ilimin su, karfin aljihunsu da tunanin su babu abin da zai iya a kai, domin ita wannan jijiya ba ta doruwa. Sai ya fashe da kuka. Malam Ja’afar ya mike daga kujerar sa ya isa ga Sulaiman, ya mikar da shi tsaye ya rungume. “Haba Sule! Kamar ba namiji ba? Namijin ma, likitan likitoci. Ba ka yi kuka a kan sauran al’umma da kuke kwana da yini kuna fama dasu ba sai a kan matar ka kadai? Su Allah ba ya son su ne yake dora musu lalura? Allah da ya halicci Hadiza ya fi mu son ta, shi kadai ya san dalilin sa na hukunta hakan a gare ta. Yau in Hadiza mutuwa ta yi me zamu iya ban da mu yi mata addu’a? Amma tana raye, a kalla muna ganin ta muna jin dadi, ka yi tawakkali ka barwa AIlah, ka zamo mai YAKANAH, sai ya yi maka tukuici da abin da baka zata ba. Kai za ka ba ta kwarin gwiwa, ta rungumi kaddarar da Allah ya dora mata. Amma idan ka fita karaya, wane ne zai karfafa wani?” Ya mika hannu yana share masa hawayen da suka kasa daina ambaliya daga kyawawan idanun sa. Dr. Ruth ta yi gyaran murya, ta dubi Dr. Sulaiman ta sunkuyar da kanta, kana ta dago ta ce, “Ina ganin idan Dr. Hadiza ta ji sauki, za ta iya ci gaba da aikinta ta hanyar amfani da wheel chair, idan har za’a samu wanda zai juri kawo ta da mai da ita”. Kiris! Ya rage ya lailayo ashar ya antaya mata, amma da ya tuna Malam na wajen Sai ya balla mata harara, a zuciyar shi ya ce, “Uwar ki za a sa a wheel chair ba uwar Munib ba”. Samson ya ce, “Shawarar Ruth abar dubawa ce, hakan zai debe mata kewa fiye da ta zauna a gida ba abin da take yi. Ko ba don zuwa aiki ba dole za a nema mata wheel chair ko da a gida ne”. Ba shi da abin cewa, don duk likitocin abin da suke cewa kenan. Malam dai baya ji saboda cikin harshen turanci suke maganar. Sulaiman ya tashi ya fita ya nufi ICU inda aka kwantar da Hadizah. A bayan kofa ya tsaya ya rabe, yana leken ta, ya kasa karasawa, ya kura mata ido yana ta’ajjibin yadda kwana daya rak! Allah ya_ jirkitar da kyakkyawar fuskar Hadiza, ko ina a jikinta rauni ne, nan plasta can plasta. Barci take sadidan, sai dai da gani ba na Allah da Annabi bane (na karfin allurai ne). Rabin fuskarta nade cikin bandeji, wadda ta kumbura ta yi sumtum kamar an hura (baloon). A hankali ya soma taku ya isa ga gadon da take kwance, ya ja kujera ya zauna dai-dai fuskarta yana fuskantar ta. Ya kai hannu bisa goshin ta wanda ke nade cikin bandeji, kamar an ce da ita bude idon ki. Suka yi ido hudu da Sulaiman din ta, ta dubi dakin ta dubi kanta, ta tabbatar a kwance take a gadon asibiti. Ta maido duban ta ga Sulaiman wanda ke binta da ido, da zuciya, ta ce cikin kankanuwar murya, “Accident na yi ko?” Ya daga mata kai. Ta dora hannunta mai rangwamen raunika bisa nashi dake goshin ta, ta sauke, don ji take kamar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse. Ta yunkura da niyyar ta tashi zaune amma ta ji kamar ba jikinta ba, ya mike ya kama ta ya mikar da ita zaune. Ya janyo pillow ya tusa mata don ta ji dadin jinginar, ya tabbatar dai da gaske ne Hadizar shi ta zama disabled (nakasasshiya), sai jikinsa ya soma kyarma. Duk dauriyar da yake yi abin ya ci tura, da sauri ya rungume ta, cikin shesshekar kuka ya ce, “Cikin kowanne hali, INA SON KI HADIZAH”” Kuka suke dukkanin su babu mai rarrashin wani, don ita Hadiza ta tabbatar abin da zai sa Sulaiman kuka, to tabbata ba karamin abu bane, wannan shi ya gigita ta, ita ma ta fashe da kuka. Fati a gaba, Yaya, Malam, Hamza da babban Yayan su Mukhtar suka shigo, daga Hadiza har Sulaiman babu wanda ya san da shigowar su, shessehekar kukan Fati ne ya ankarar da Sulaiman cewa akwai mutane a dakin. A hankali ya zare jikinsa daga na Hadiza ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya
Table of Contents