Chapter 14
Chapter 14
easy (ba ka daukan abubuwa da sauki). Ka bini a hankali in maka bayani”. Ya kunna computer inda (record) din Hadiza yake yana nuna masa yadda ciwon ya ci karfin ta a yanzu, da irin taimakon da ya ba ta. Shi kan sa Bunza sai da ya yi hawaye balle gogan, wanda gudun jini ya katse a jijiyoyin jikinsa. 2K 2K 2 K arfe shida na safe Dr. Surayyah ta fito da jaririyar da aka cirowa Hadiza, kamar ta daya da Baban ta kamar ya yi kaki ya tofar, har duhun kalar nashi ne. A lokacin ne jama’ar gidan su Hadiza suka iso, Dr. Surayyah ta sanar da su. Fati karfe bakwai na safe ta iso asibitin, ta baro yaran da Alti ta zo a (keke-napep). Dai-dai lokacin da aka turo Hadiza za a mai da ita ICU, ya yi dai-dai da sanda Surayyah ta mika mishi jaririyar ya ki amsa, sai Fati ce ta amsa. Za a wuce da Hadiza ta rike hannun sister Magajiya ta rada mata cikin nishi, “Ina son yin magana da su…..”. Don haka sister ta dakata. Sulaiman da Fati suka garzayo gareta, kowanne ya fita hayyacinsa. Fati rungume da jaririya tsantsan tana ta tsala ihu. Itama Fatin Kukan take.Hadiza ta runtse ido hawaye na zirara, ta ce, “Fati ina alkawarin mu?” Cikin Kuka ta ce, “Yana nan Yaya Hadiza”. Ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, duk su Malam Ja’afar na kallo, ta ce, “Fati har da shi a alkawarin fa………. Ta yi sharbe ta yarfar da majina da hawaye ta ce, “In kula da shi? Yaya Hadiza ai shi babba ne?’ “Babba ba ya _ bukatar kulawa Fati…… ?” Ta ce, “Ban sani ba”. Ta ce, “To yana bukata, shi ma kamar Munib ne, bambancinsu shine shi Munib kulawar UWA yake nema, shi kuwa Sulaman kulawar MATA yake ne Ta yi murmushi ta runtse idonta, cikin azabar da take dandana. Sulaiman ya russuna ya sumbaci goshinta, “You will get well soon Hadizah…… , bana bukatar kulawar kowa sai taki, in ba taki ba na yafe, zafin ciwo yake sa ki yin irin wannan magana……… Ta girgiza kai ta kara manne hannun su ta ce, “Sulaiman-Fati………… ” Dr. Bunza ya karaso ya tura gadon da kanshi yana ta yiwa sister Magaji fada. Yaya ta karaso ta karbi ‘yar da ke hannun Fati ganin tana neman kwala ta da kasa. Dr. Sulaiman ya mai da hannun shi cikin aljihu, yana so ya yi kuka amma idanun sun bushe kamar soyayyar gyada marau-marau. Sai Malam Ja‘afar ya iso gare shi ya kamo hannun sa suka zauna tare, yana cewa, “Karbi ‘yar ka sa mata albarka”. Amma Sulaiman ya ki, sai kirjin shi da ke ta kai kawo kamar zuciyar ta ballo allon kirjinsa ta fito. Ana shigar da ita cikin computer don a yi hoton kwakwalwar ta kamin likitocin su san me za su yi a kai, ta soma ta yi salati rai bakon duniya ya yi halinsa. “Allah ya ji kan Dr. Hadizah!” Abin da dukkanin likitocin suka furta kenan, a lokaci guda suna share ambaliyar hawaye daga idanuwan su, tare da kai hannu su rufe mata idanun ta. 2K OK KK A n bawa Malam Ja’afar da Sulaiman gawar Hadiza cikin mota ambulance, zuwa nan unguwar Karkasara. Inda daruruwar jama’‘a suka yi jana’‘izar ta. Mijinta da Mahaifinta suka sanya ta a kabarin ta, suna masu yi mata addu’ar fatan alheri, yafiya, afuwa da addu’ar Allah ya yi mata masauki da aljanna, Annabi ya san da zuwan ta. Su kuma ya basu imanin jurewa. Sulaiman ya baiwa kowa mamaki, saboda yadda ya tsaya a kan jana’izar Hadizah, babu ko digon hawaye a idanunsa. Ba su san shi kansa kukan na zuwa ne idan an san abin da ake yi ba. To bai san me yake yi ba, bai san halin da kwakwalwarshi ke ciki ba. Ya san dai kawai Hadizar sa ta rasu, sun kaita makwancin ta na gaskiya, bayan wannan bai san komi ba, bai san kansa ba, bai san a ina yake ba. Ya dai bude ido ya gan shi a gidan su Hadizah, dakin Mukhtar, ba ya rintsawa, yadda ya ga rana haka yake ganin dare, ya wuni yana_ karbar ta’aziyyar ‘yan uwa da abokan arziki. Tun a ranar Inna Halima, Malam Sulaiman da sauran kannen shi suka zo Kano, da su ake karbar gaisuwa har zuwa kwana uku. Ranar lahadi suka juya Bakori cike da juyayin halin da Sulaiman ke ciki. Malam ya ce zai dinga aiko mishi da rubutu tsayin kwana bakwai. Ya ce, “To”. Wadda ta zama kalma mafi saukin fada a bakinsa, sai kuma bin kowa da ido, amma abinci da ruwa wannan kwanan shi uku bai dandana su ba. Alti ma tana gidan ita da yara wadanda suka damu kowa da tambayar ina Momin su? Alhamis aka yi sadakar uku, Alti ta koma kauyen su tana kuka da hawayen ta, ta ce sai ranar sadakar arba’in za ta dawo. Tambaye ni ina baiwar Allah Fatima Ja’afar Mai-Yadi? Tana can dakinta tana kuka, tana fama da jaririya, bini-bini ta hada madarar (SMA) ta dura mata, ta ba ta ruwan zam-zam. Ba ta barin ta tayi kuka, idan ta bata madarar da ruwan sai ta sa ta a baya ta goye, ta zauna ta yi ta jijjiga ta, har sai ta samu barci, ta sakko ta ta sanya ta a gadon ta, ta zauna a gabanta ta yi ta girka kuka. Idan kukan ya ishe ta sai ta bude littattafan addu’o’in ta, ta yi ta karantawa tana rokon Allah ya kai ladan makwancin rabin jikin ta Dr. Hadiza Ja’afar MaiYadi. Mutuwar Hadiza ta girgiza kowa a gidan nan, haka duk wanda ya santa ya koka ya gode Allah. Kada Dr. Surayyah ta ji labari, to ina ga wanda farin cikin rayuwar sa ya ta’allaka a wuyan ta? Ya ke kwana da ita yake tashi da ita, yake yi mata son da ko iyayen ta sai dai su ce su suka haife ta? Don haka Doctor Sulaiman-Sulaiman Bakori, yana cikin wani irin hali da duk masoyinsa dole ya koka masa, in har yana da imani, ya bishi da addu’ar Allah ya ba shi dangana da YAKANAH! Tuni Mukhtar ya koma Kaduna, ranar da aka yi bakwai shi ma Malam Ja’afar ya ce ya koma bakin aikin sa. Ya bishi da “To”. Kamar yadda yake bin kowa da ita. Ya tattara ya koma gidansa, shi kadai kwal kamar maye. Sai da ya gwammace da bai dawo ba, a lokacin da ya ci karo da wheel chair din Hadiza da kayan ta dake watse a dakin barcin su, a nan ne komi ya dawo masa danye, karo na uku da ya soma kukan da ya tabbatar har abada ba zai daina ba. Haka ya kulle kansa, ba shi da abinci sai ruwan lipton wanda yake dafawa a kettle ya dura a flask ya wuni yana sha, babu ko tunanin sa sukari. Cikin kwanaki ashirin da mutuwar Hadiza ya zama babu kyawun gani, kasumba ta cika fuskar sa. Duk wannan gayun ya daina shi, wanka ma ba kullum yake yi ba sai ya ji alamar jikin shi na dan wari-wari, ya kashe wayoyinsa gaba daya, ya yi sallama da aikin sa,
Table of Contents