Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Yakanah Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

yarinya ce mai tsananin son addini da nutsuwa, ba ta da rawar kai ko kadan irin na ‘yammatan zamanin nan, komi nata cikin hankali da nutsuwa yake. Ita da Hadiza kamar an tsaga kara, sai dai Hadiza fara ce sol, yayin da Fati ta kasance wankan tarwada. Amma hatta yanayin tafiyar su da murmushin su iri daya ne. Ss ulayman Bakori, mutumin — garin Bakori ne ta jihar Katsina, daga kallo na farko mawuyaci ne ka bambance daga kabilar da ya fito, wani irin mutum ma’abocin cikar zati da kamala da duk wani nau’in daidaito na rayuwa, ga dimbin ilimi a cikin fannonin kiwon lafiya daban-daban. Ya ci sunan mahaifinshi ne don haka a gidan su ake kiran shi mai sunan Malam. Mahaifin shi Malam Sulaiman, Malami ne mai karantarwa, yana baiwa magidanta anguwar su karatun buzu. Duk wani da ya kwana ya tashi a garin Bakori ya san Malam Sulaiman Mai-Gafaka. Mutum ne da al’ummarsa ke matukar ganin girman sa, kuma ya yi fice a garin Bakori baki daya saboda ilimin da Allah ya ba shi, kowa yana daraja shi. Shi ne da na biyu a gidansu, yayar shi Jummai ta rasu wajen haihuwar fari, sai kannen shi Ramatu, Saude da Ruma, duk suna gidan aure. Sai Khalid wanda ke karatun sakandire a halin yanzu. Sulaiman ya yi dukkan karatun shi ne da taimakon gwamnati da mahaifiyar shi Inna Halima, wadda duk lokacin da hidimar karatun ta tashi take fitar da kadararta ta siyar ta yi masa. In dan ta Malam ne sakandire ma kawai ta isa. Burinsa Sulayman ya zauna a gida ya tallafa mishi kasuwancin shi na fata, ya yi aure ya haifa mishi jikoki shi kuma zai yi masa komai. Amma Sulaiman ya ki, ya dage ga son cimma burinsa na son zama likita. Ba abin da yake so a rayuwar shi irin yau ace ya zama likita yana yiwa mutane allura. Irin yaran nan ne gifted tun suna kanana, wato ‘yan baiwa. Wata irin kwakwalwa gare shi da ba duk mutane Allah yake baiwa ba, duk inda yayi karatu malaman shi sai sun san shi, sun kuma ja shi a jiki, sun so shi saboda hazakar shi. Ya yi gaba dayan karatun shi daga jami’ar Najeriya (NSUKKA). Bayan ya kammala MBBS din shi ya yi nasarar samun_ scholarship zuwa jami’ar (Manchester) inda ya yi specializing a kan zuciya da duk abin da ya shafe ta. Bayan kammalawar shi da dawowar shi ya soma aiki da federal, hakan ne ya sa ake yawan canza mishi wajen aiki. Ya fara ne da aiki a babbn asibitin koyarwa na Ibadan, daga baya suka mai da shi ABU Teaching Hospital. Nan din bai dade ba suka dawo da shi nan AKTH na Kano, inda Allah ya hada shi da Hadizah. Haduwar su haduwa ce _ special kuma haduwa ba ta dadi ba. Yana tare da patient da ya yiwa aiki satin da ya wuce, Hadizah Ja’afar, da wasu abokan karatun ta suka shigo domin daukar lacca. Ko kallon su bai yi ba, balle ya tantance kamannin su, kasancewar Allah bai dora mishi lalurar yiwa mata kallon kurilla ba. Tsakanin shi da kowacce diya mace, kallo daya ne, da kau da kai. Suka samu_ kujeru. suka zauna, kowacce da jotter din ta da biro a hannu. Yana ta yi musu bayani cikin lafiyayyen turancinshi na _ Birtaniya mara surki, wani zubin ya yiwa mara lafiyar tambaya ta ba shi amsa. Wata amsa da patient din ta bayar ta sanya su murmushi dukkanin su (ban da Hadiza), cikin kalaman ta za ka fahimci kwakwalwarta ta tabu sakamakon bacin zuciya da damuwa. Ta ce, “Likita nifa ‘yar sarauta ce ba mara lafiya ba!”. (Wannan ne ya sanya su yin murmushi). Ya ce, “Wacce sarauta gare ki don mu fara girmama ki?” Gaba daya daliban suka yi dariya don yadda yake biye ma shirmen matar dole ya baka dariya. Ta ce, “Sarautar Kano gare ni”. Yace, “Wacce ke nan?” Ta ce, “Nice ‘yar ruwatan Kano”. Gaba daya suka yi murmushi, wannan karon ma ban da Hadizah, wadda a lokacin hankalinta baya tare dasu, yana ga halin da ta baro Mamansu a ciki na rashin lafiya mai tsanani. Ba zato Dr. Bakori ya jefo tambaya, “Mene ne delusion?” Ya kuma nuna Hadiza da ya lura hankalinta ba ya tare da shi matsayin wadda za ta amsa mishi tambayar shi. Ya yi mata magana ya kai sau uku ba ta san yana yi ba. Hadiza ta damu da Mamanta sosai, kasancewar ta jarumar Uwa mai hidimtawa rayuwar su, tun daga yarinta har a girman su. Yaya, (Sa’adatu), ba ta huta da dawainiyar su ba. Don haka jin ciwon ta suke tamkar a gangar jikin su. Duka kawayen ta babu wadda ta zungure ta, don sun san da ta ji za ta ba da amsa a yabe ta kamar yadda manyan likitoci suke yabon ta a kullum saboda kokarin ta. Ya buga tebir din gaban shi da karfi har ta razana, ya nuna mata hanyar waje ya ce, ‘You can go out….. in kin gama tunanin kya dawo”. Ta mike sumi-sumi ta fita, murna gun su Hafsat kamar su yi yaya, yau Allah ya nuna musu likitan da ya yi maganin ‘yar gaban goshin likitoci. Ya yi (referring patient) din zuwa psychiatric, su kuma ya sallame su. Ya koma gida a wannan ranar, bayan ya gama duk abubuwan da ya saba na al’adar rayuwar shi kamin ya kwanta, kamar shan fruit da edcercise saboda shi da daddare yake edcercise din sa kasancewar da safe ba shi da lokaci. Amma abin mamaki ya kasa runtsa idonsa, tunanin fuskar dalibar da ya kora a yau ke gilma mishi, ya hana shi sakat, ya hana shi sukuni, ya yi duk kokarin da zai yi don ya samu barci amma hakan ya faskara. Ya ko kasa runtsa idon sa, wani bakon al’amari ne mai takura zuciya da bai taba tsintar kansa a ciki ba. Hadiza ba wata muguwar kyakkyawa ba ce cancan, tana da kyau dai-dai nata, sai dai kuma yarinya ce mai aji na karshe. Fuskarta zagayayya mai dauke da dara-daran fararen idanu masu sheki da walainiya, hancinta kamar an sanya ruler an ja shi an daidaita shi a kan (obal -shaped) fuskarta. Bakinta dan karami kamar cokali baya shige ba. A kan tsinin hancinta tawwadar Allah ce da aka haife ta da ita, fara ce sol! Irin farin nan da wadataccen ilimin boko ke taimakawa wajen zahharar sa. Bai taba ganin yarinyar da (lab-coat) ta yi ma kyau kamar Hadizah ba. Ba Sai ya tsaya wahalar da kanshi wajen tunanin abin da ke faruwa da shi ba, ya tabbata son Hadiza ne ke ratsa kowanne sako a jikinsa. Abin haushin ko sunan ta bai sani ba, zuciya ta kwashe shi ya yi abin da ya zo ya dame shi. Bai taba tsintar kansa a kwatankwacin irin wannan yanayin ba, a kan diya mace. Sai dai shi a ce ana son sa yana hura hanci, kada hakan ya janyo raini, baya fatan hakan ya kasance sakayya ce Allah ya yiwa dimbin matan da ke binsa agindi-agindi don ya so su yana yakice su. Tare da yi musu wulakancin da ko a hanya suka ganshi bazasu yi fatan ace sun

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18