Chapter 11
Chapter 11
murmushi, “Cewa_nake watarana aure za ki yi Fati?” Nan da nan Fati ta yi kicin-kicin da fuska, ta juya mata baya ba ta ce komi ba. Hadiza ta ce, “Ko baki ji ni ba? Aure za ki yi Fati dole ba da jimawa ba, don haka ki tsaya ki gina rayuwar ki kamar yadda muka gina tamu, bana so saboda amfanin kaina ke in tauye ki. Don haka na baki kwana biyu ki yi tunani, an fara sai da JAMB na wannan shekarar, don haka ki nutsu ki kama abin da zai taimake ki ranar da bani. Duk wata kauna da dan uwa na gari zai nuna wa dan uwansa kin nuna min ita, sakayyar ki na wajen Allah. Sai dai ba zan bari ki kari rayuwar ki baki dandani zakin ilimin ko auren da na dandana ba, dole in samar miki future kafin Allah ya yi hukuncin da ya So a kaina….” Fati ta yi saurin juyowa ta dubi Hadiza, domin a da ta bata baya ne. Ba ta gane abinda take nufi ba. Hadiza ta yi murmushin karfin hali ta ce, “Fati zan gaya miki wani abu, amma bana so ki daga hankalin ki, bani da lafiya Fati, amma don Allah ko Yaya ban yarda ki gayawa ba balle Sulaiman. Fati na dade ina fama da ciwon kai wanda nake yi lokaci-lokaci, Sulaiman ya sani ina yawan fama da (migrain) amma bai taba zurfafa bincike ba, don ban taba gaya masa yadda nake ji ba. Ba tare da sanin sa ba na je wajen Dr. Bunza mijin Surayyah, da ke likitan kwakwalwa ne, cikin sirri ya yi min bincike mai zurfi inda ya sanar dani ina fama da kansar kwakwalwa (brain cancer)”. Fati ta zazzaro ido ta sulale ta zauna a kasa, ta kai hannu ta dafe kirjinta, sai ga hawaye suna shatata! Hadiza ta yi murmushi ta matso da kujerar ta inda Fati take, ta dora hannu a kanta. “A‘a, Fati kada mu yi haka da ke, ama nar rayuwata nake gaya miki, wadda bani da wanda zan bawa sai ke. Ba wanda zan iya gaya ma wa Sai ke, ciwon bai yi tsanani ba, kuma ina shan magani a boye, ko Surayya ba ta sani ba. Fati abin da ya sa na gaya miki don ki tallafa min ne, Sulaiman likita ne wanda ke bukatar kwanciyar hankali don samun (confidance) wajen gudanar da aikinsa na ceton rayuwar al’umma, idan ya ji wannan maganar ba zai taba samun kwanciyar hankali ba. Fati Sulaiman yana sona, sosai, irin son da zai iya bani rayuwar shi, bana son abin da zai dagula masa lissafi, ki rike min amanata, ki rike min ‘ya’yana, ki basu tarbiyya irin taki kada ki bari Sulaiman ya tagayyara a bayana. Ina son shi yadda yake so na, na so in Ci gaba da rayuwa tare da shi, in ci gaba da haifa mishi ‘ya’ya kamar yadda yake so, amma ban san ya ya Allah zai yi dani da rayuwata ba. Ki rike min Sulaiman Fati bana so rashi na ya tagayyara shi…….. ” Zuwa wannan lokacin duka ‘yan uwan biyu sharbe suke, na hawaye da majina. Girki yana ta kauri, amma ba su kula ba. Fati ta rage sautin kukan ta, ta ce, “Shi brain cancer ba’a warkewa?” Hadiza ta ce, “Ba a warkewa gaba daya, ko ya lafa zai tashi, amma ina kula da shan magani”. Fati ta yarfe hawaye ta ce, “Wannan ba abun boyewa bane Yaya Hadiza, ki daina fidda rai da rayuwa saboda ciwo. Insha Allah ke za ki aurar da Munib da Muniba, ya kamata ki sanar da Dr. domin ya taimaka miki da addu’a, duk wani hali da zai shiga ai shi musulmi ne ya san duk son da yake miki ya san bai kai wanda Ubangijin ki yake miki ba. If the condition become worst, ba zai taba yafe Hadiza ta yi shiru tana mamakin Zurfin hankali irin na Fati, yarinyag karama sai tunanin manya. Ta ce, “Zan duba shawarar ki Fati, Allah ya kara. min YAKANAH, ya_ bawa ‘ya’yana tarbiyya irin taki. Ai dai za ki kula min dasu ko Fati?” Cikin kuka ta ce, “Yaya Hadiza ki daina yi min wannan maganar, bani da jarumtakar sauraron ta…… “, Ta ce, “Na rantse da Allah idan baki yi min wannan alkawarin ba nima ba zan bi shawarar ki ba”. Cikin makyarkyatar murya ta ce, “Eh…….eh……na yi alkawarin zan kula dasu”. Ta ce, “To nima zan bi shawarar ki, amma ba yanzu ba. Tashi sauke tukunyar can tana kauri”. Ta share idonta ta mike ta sauke, ilahirin jikinta sai rawa yake. Ta kashe komi ta maido Hadiza falo, ta yi dakin su ta rufe ta fada kan gadon su ta soma girka kuka. Ta ga kukan ba zai amfane ta da komai ba, sai ta je bandaki ta dauro alwala, ta shimfida sallaya ta soma Sallah, a kowacce sujjadarta tana yiwa Hadiza addu’ar Allah ya ba ta lafiya. Wayar Hadiza ta yi kara, a lokacin tana bisa sallaya tana azkar, don haka ba ta daga ba har ta tsinke. Sai ya yo tedt, ta dauka ta duba Sulaiman ne yake gaya mata suna bisa hanya har da Inna Halima za ta zo ta duba ta kuma za ta ga likita, don haka a gyara mata daki don za ta kwana biyu. Hadiza ta ji dadin zuwan Inna, domin Innar Sulaiman mutum ce har mutum, ma’abociyar raha da sanin mutunci. Don haka ta kira Fati a waya ta ce ta kara yawan abinci da ta aje a falo, ta kuma canza shimfidar gadon dakinta, don kullum a gyare yake Fati ba ta wasa da tsabtarsa. Tara na dare dai-dai suka shigo, Inna dauke da Muniba da tayi barci a kafadunta. Hadiza da Fati suka yi mata sauka ta ban girma. Sai lokacin kwanciya ne aka kai ruwa rana da Inna, don ta ce ba za ta zaunawa Hadiza a daki ba, sai tare da ‘yan jikokinta, dole suka kyale ta. Duk juyin da Inna ta yi a wannan dare, Fati take gani a kan sallaya, ta yi sallah, ta yi lazimi. Da asubahi kuwa ta soma rero (Suratul Yaseen) da sauti irin na Khusairi. Sannan ne ta dan samu barci. Karfe shida ta fada kitchen ta soma aikace-aikace, Inna na hankalce da damuwar da yarinyar ke ciki, ta rasa abin da ke damun ta kankanuwa da ita haka. To haka a washegari ma, har cikin kitchen wannan yarinya ba ta rabo da hijabi da carbi, tun tana burge ta har ta koma bata tausayi. Washegari litinin bayan sun yi kalaci, Inna da Sulaiman suka wuce asibiti in da za ta ga likitan ido, ba su dawo ba sai da rana ta take, yana sauke Inna ya juya. Sun fara cin abinci ita da Hadiza a kan darduma irin traditional carpet din nan na fata, an kuma shimfida ledar cin abinci. Don Fati ba ta cin abinci cikin mutane, loma ta farko, ta biyu, ta uku Hadiza ta soma kelayo amai kamar ta amayar da ‘yan hanjinta. Da sauri Fati ta shigo, Inna na rike da Hadiza, ita kuma ta kawo ruwa da roba Hadiza ta kuskure bakin ta. Fati ta sa moper ta gyare wajen, ta koma kitchen
Table of Contents