Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Yakanah Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

don hidimar abincin dare. Ko me take yi cikin kitchen bakinta ba ya rabo da ambaton Allah, duk a kan lafiyar ‘yar uwarta. Ita dai Inna haka nan ta ji Fati tana burge ta, tana bata sha’awa. Zahidah ce, babu duniya a gabanta, gata da dan banzan kyau da fata lafiyayya, amma ba sa gabanta, lahira take nema da harshen ta da goshin ta da gwiwoyin ta, ba ta furuci Sai wanda ya zame mata dole, ko in an tambaye ta. Amma a kwanaki bakwai da ta yi, Inna Halima babba ce mai cikakken hankali, ta lura Sulaiman ko ganin Fati a gidan shi ba ya son yi, don dai ba yadda zai yi ne, kuma bai son abin da zai bata ran Hadiza. Suna falo ita da Sulaiman misalin karfe sha daya na dare suna hira a nutse irin ta da da mahaifi, ta ce, “Wai ni mai sunan Malam me yarinyar nan kanwar Hadiza ta yi maka ko kallon ta ba ka yi? Dazu da safe ina kallo tana gayas da kai ka dauke kai ka fita, haka tun zuwana ban taba ganin ka yi mata magana ba, balle wasan nan irin na mijin ya da kanwarta. In kana wuri ta shigo sai ka tashi, in kana falo ta ganka sai ta koma ta yi ta zaman daki. Ita da ganin ‘yar uwarta sai in baka nan, mene ne manufar hakan?” Ya juyo yana kallon Inna ya ce, “Wacce yarinya kike magana?” Ta ce, “Fatima”. Yace, “Fati wai?” “Eh, ita”. Ya rausayar da kai ya ce, “Raini ne bana so, kuma ni ban iya wani wasan kanin miji ko kanin mata ba”. Ta yi sakale tana jin sa, ta ce, “Hala wani laifi ta yi maka? Har Hadiza na lura ranta yana baci da irin halin ko in kulan da kake yiwa ‘yar uwarta. Ban san ka da bakar zuciya ba, kada ka a fara a kan Fatima, domin mutum ce cikin ‘yammatan da babu irin su a yanzu, wannan yarinyar tana da halayen ‘yan aljanna, ka yi a hankali baka sani ba ko waliyya ce”. Shi abin ma sai ya ba shi dariya, ya ce, “A wannan kalatacciyar duniyar tamu dama akwai sauran waliyyai Inna?” Ta harare shi ta ce, “Dariya ma kake min?” Ya yi saurin cewa, “A’a, yi hakuri Inna”. Ta ce, “To ka gyara ma’amalar ku, zai fi kyau a ce akwai kyakkyawar alaka a tsakanin ku saboda Hadiza, in ta gaishe ka ka dinga amsawa cikin walwala da sakin fuska, wanda ya rike ibada ba ya wulakanta a duniya da Jahira. Baka sani ba ko ta fi ka matsayi a wajen Allah, ka canza takun ka a kanta, ai ba haka na ga kana yiwa su Ruma ba, to matsayin ta daya dasu a gare ka, ka ji na gaya maka”. Bai ce komi ba ya jawo wata hirar, don dai a sauya wannan. He is not interested at all (Fati is not the kind of person) wato ba ta daga cikin irin mutanen da yake son yin mu’amala dasu. Haka nan jinin su bai hadu ba, don yana son Ya, ba dole sai ya yi wata kakkarfar alaka da kanwar ta ba, bayan wadda musulunci ya ce, ai ba sa’ar wasan shi ba ce kanwar shi ce. Kwana bakwai din da Inna Halima ta yi jinyar Hadiza suke ita da Fati, komai ta ci sai ta amayar, ga zazzabi da ciwon kai mai zafi, sai ta rike kanta idan ciwon ya motsa mata tana wani irin kuka mai keta zuciyar duk mai imani. Sulaiman da farko bai sani ba, don ya dauka laulayin ciki ne irin wanda ta saba, kuma ciwon baya tasar mata da daddare lokacin da suke tare kenan. Ita ma Inna ta lura ta san laulayi ne na sabon ciki, amma wannan buga kan da Hadiza take yi a jikin bango da kukan da take yi na azaba ta fahimci akwai dai wani abun, amma tana ganin dukkan su likitoci ne sun san abin da ke damun ta, kuma ta ga Hadiza tana shan magani, sai ba ta yi magana ba, amma dai ba ta taba ganin irin wannan laulayin cikin ba. Don haka ta kara sati saboda lafiyar Hadiza wadda ta daina cin komai sai ruwan bakin lipton da ruwan tsamiya. Gaba daya ta rame ta fita hayyacin ta, ba ta taba yin cikin da yake wahalar da ita irin wannan ba. Tun Sulaiman bai gane ba har ya fahimci Hadiza ba ta da lafiya sosai, wannan ya wuce laulayi kuma wannan (migrain) yana bukatar bincike. A daren ya fito daga wanka yana tsane kanshi da dan kankanin towell, tana kwance rigingine a gefen gado, cikin doguwar rigar barci mai santsi mara hannu ruwan madara, kyawawan kafafunta da cinyoyin ta a mike sambal, a haka sai ka rantse lafiyar ta kalau ba ta tare da wata lalura. Son matarshi da kaunar ta na kara girgiza zuciyar sa, yana hargitsa gangar jikinsa. Ta kure fanka da A.C amma ba ta daina zufa (gumi) ba. Da sauri ya karasa zarga igiyar pyjamas din shi ya yiwa kanshi kyakkyawan matsuguni a bayan ta, ya daura hannu a kan goshin ta, zafi rau! Dole ya hadiye nashi bukatan ya soma ba ta kyakkyawar kulawa ta hanyar sanya karamin towell a ruwa yana goge mata kanta don zafin kan ya ragu. Sannan ya soma bin gabban jikinta da message don ta ji dadin kasusuwan ta. Ya juyo ta ya rungume ta yana furzar da numfashi da sauri da sauri, ya sake cewa, “Cikin kowanne hali, INA SON KI HADIZAH!”” Ta bude idanunta a hankali, wadanda suka kankance suka yi jawur tana kallon abin son ta, shi ma kallon ta yake kallon yaya zan yi da raina? Ya ce a galabaice, “Gobe zan dauko Dr. Bunza ya duba ki”. Gabanta ya yi wani irin faduwa, ta runtse idon ta da karfi ta ce, “Bana so, kada ka dauko shi, idan kuma har ka dage sai ka dauko shi to zan koma Karkasara’”. Ya girgiza ta da karfi ya ce, “What do you mean (me kike nufi)? In barki a gida kina ciwo ban nema miki magani ba? Ai Allah sai ya tambaye ni, tyayen ki da suka danka min ke su tuhume ni. Wannan ciwon kan bana wasa bane yana bukatar bincike”. Ta ce, “Ai ba yau na fara ba, kuma da na sha magani shi ke nan _ yake lafawa”. “Ina maganin? Dauko min in gani”. Ta ce, “Ya kare dazu, da safe nake shirin in aiki Fati ta siyo wasu”. Yace, “Wane magani ne?” Ta yi shiru. ““Tambayar ki nake yi, ina maganin? Ya ya sunan sa?’ Ta ce, “Panadol”. A mamakance ya maimaita “Panadol?” “Eh”. Ya ce, “You are silly ko in ce you are nonsense Doctor! I did not beliebe YOU… “(kina shirme, ke shashashar likita ce, ban yarda dake ba). Ya tashi a fusace ya fizgi waya ya kira Dr. Bashir, ‘consultant’ na ‘psychiatrist’, Surayya ce ta dauka, bai ko amsa gaisuwar da take mishi ba ya ce, “Ina mijin ki?’ Ta amsa “An kira shi a ‘emergency’ kuma ‘he is on call’ yanzu ya fita, ya manta wayar”. Ya kashe wayar ya cillar ya zauna a gefen gado

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18