Chapter 10
Chapter 10
matar? Ashe you are not serious…!” Ta juyar da kai, sai ga hawaye sharrr! Sun zubo a kan kundukukin ta. Kiris ya rage dariya ta kubce masa, amma ya danne kada ya kara laifi. A gicciye ba tare da ya dube ta ba ya ce, “Wai ko a cikin student din ward din ku, irin ‘yan yara-yaran ‘yammatan nan? Ko rikakkun ‘yammatan likitoci irin su Dr. Surayyah”. Haushi ya kama Hadiza, don ta lura ya mai da abin zolaya. Ta yi shiru ba ta ba shi amsa ba. Ya rungumota ta baya, ya dora kan shi a kafadun ta, yana sakin ajiyar zuciya mai nauyi. A sanyaye ya ce, “Ko kin daina sona ne Hadizahh? Kike neman kai dani? A da ko kallo na wata ta yi, kallon da bai yi miki ba, sai kin kwana bakya yi min magana, amma yanzu duk kin daga hankalin ki wai in yi aure. Which mean……. na gundire ki…. kina neman mataimakiya don ki huta….. Ni ina ruwana da wasu kafafun ki tunda ba su nake aure ba? Inda nake aure zam-zam yake. Da aka yi accident din ma, kamar an kara masa armashi. Kafafu? Ni ba ina da su ba? Kuma ba ina daukar ki dasu ba? To meye damuwar ki? In gaya miki gaskiya, ba zan iya sharing kaina ba, saboda ina da kyama, ba kowacce mace zan iya hada jiki da ita ba. Babu, ban taba ba, bana fata, kada ki tursasa ni, don ba zan iya ba, ba zan iya adalci ba. An ce kuma in ba za ku iya adalci ba, to ku zauna da daya. Amma in kin gwammace ranar kiyama in tashi da shanyayyen barin jiki, all the same, sai in auri Surayyah! Kinga daga nan sai ku kara dankon zumunci…….. Ta ture shi da sauri, duk da jikinta ya yi sanyi da maganganun sa, ta tabbatar iya gaskiyar shi yake fadi, don shi bai fadin abin da ba haka bane a zuciyar shi. Don kaji dadi, ko don ya faranta maka. In haka ne kenan Sulaiman da gaske za ka iya auren Dr. Surayyah?” Sai hawaye suka zubo. Magana take a zuci, ba ta san cewa a fili ta yi ba. Ya sauka daga gadon ya zauna dabas a kan kafet, ya dauki hannu ya rafka uban tagumi, “Ni SuJaiman na shige su, duk yadda na yi, ban iya ba. To ki fadi yadda kike so, ni kuma mijin ta ce ne!” Idon ta fal hawaye ta dube shi cikin ido, abin da bata yi sai rana ta kure, “Ka gaya min gaskiya Sulaiman, Surayyah kake so?” Ya yi murmushi ya shafi siraran lebbansa, “Ya ya ba zan so ta ba tunda tana son ki, tana son ‘ya’yana?” “Ni ba wannan son nake nufi ba…….. Ya mike tsaye ya bata baya zai fice, “Koma wanne kike nufi shi ne, yarinyar nan rikicinki ya ishe ni, son ta nake na soyayya, soyet. Ki yi kulikulin kubura dani, ko ki yi ta kuka, har hawayen ya kare…….. ” Duk da kuka take ba ta san sanda ta yi dariya ba, ganin kuma ya dawo ya cafko ta yana son a sauya hirar da irin wacce ya fi so ayi, mai ma’ana da tsayawa a zuci, hadi da dimbin lada. Ba ta da zabi (she habe no choice) ban da ta rungumi mijinta, mai son ta, mai kaunar ta. Ta nuna mishi son shi kawai ya sani, bai san nata ba. Duk hasashe take, amma ita ma ta san ba za ta iya raba Sulaiman din ta da kowa ba. 2K OK D a wannan Sulaiman ya kashe bakin Hadiza da maganar ya kara aure, saboda ita ta nakasa. Don ta san cewa zai yi zai auri Dr. Surayyah, ita kuma in da abin da ta tsana ya fito daga bakin sa, to bai wuce wannan furucin ba. Surayyar ba ta watsar da Hadiza ba, ta kan zo in ta samu sararin aiki kuma suna yawan yin waya. Tayi-tayi Hadiza ta koma aiki in ya so sai Fati ta dinga kula da zirga-zirgar ta amma ta ki. A ganin ta ita Fatin zaman ta kenan ba za ta yi nata auren ba? Ko ko haka za ta karar da rayuwar ta wajen hidimar ta alhalin bata kai ga cimma komai a rayuwa ba? Gara ita ta kai ga matakin da duk dan adam ke burin samu; tayi ilmi, tanada kwali, tayi aure, ta hayayyafa. Don ta zauna gida a halin yanzu babu komi. Ta ce, “Surayyah mune bamu gane ba, ko da yake mu namu aikin mai tushe ne daga addini. Amma ba abin da ya kai mace ta zauna a dakin mijinta ta yi biyayyar aure dadi da kwanciyar hankali, amma ina amfanin da auren ki da mijin ki da ‘ya’yan ki amma kin watsar dasu kin barwa mai aiki kullum kina titi, bayan mijin ya tsare miki dukkan bukatun ki na rayuwa?” Surayyah ta ce, “Ke din ce dai kawai kin yi sa’a Hadiza, amma ba ko wadanne maza ne irin Dr. Sulaiman ba”. Kishi ya motsawa Hadiza ta hadiye shi mukut, amma ta san Surayya gaskiya ta fada, Sulaiman is unikue, akwai wani simpleness a tare da shi wanda maza da yawa basu da shi. Hadiza ba ta samu kwanciyar hankali ba sai da Dr. Surayyah Yahya ta kawo mata katin auren ta da Dr. Bashir Bunza, cike da shakiyanci ta nunawa Sulaiman. Ya karanta ya ciji yatsa, “Shege Bunza, ya kasa ni”. Ta kyalkyace da dariya ta ce, “Eh, to kai ne ka tsaya sanya”. Ya harare ta da idanun kauna, “Haka ma za ki ce? Bayan ke kika kashe min gwiwa, ai da tuni na karkata hula nasa kai, wallahi da ni zan kasa shi”. Ta sake yin dariya ta ce, “Oho dai, sai abi wani sarkin ba Ado ba”. 2K KK OK A sabar ce sassanya mai dauke da wani irin lullumi mai sanya nishadi a zukatan dan adam, ana saura kwana biyar a kama azumin watan Ramadan, kamar kowacce asabar din karshen wata. Dr. Sulaiman ya zuba ‘ya’yan shi a mota suka nufi Bakori ainihin gidan iyayen shi kamar yadda suka saba, can za su wuni, wani zubin har yamma ko dare. To yau ma hakan. Gidan ya rage daga Hadiza sai Fati, don Alti ta je kauyen su Kukawa ganin gida za ta yi sati biyu tunda yaran ma cikin hutu suke. Fati ta tura Hadiza_ kitchen kamar yadda ta bukata, ita tana girki Hadiza na mata hira. Ta ce, “Fati yau shekara guda cur da faruwar al’amarin nan, nayi-nayi ki kara neman wani admission din amma kin ki, kina nufin haka za ki yi ta zama kina yi min bauta ba karatu ba aure? In don nice wallahi bana cikin matsala a halin yanzu I can take a good care of myself (zan iya kula da kaina) ko daa ce ni kadai ce a cikin gidan nan”. Fati ta sauke tukunya ta dora wata, ta yarfar da hannu don zafi. Sannan ta dubi ‘yar uwarta, “Yaya Hadiza ba zan iya barin ki ke kadai in tafi makaranta ba, ko na tafi tunanin halin da kike ciki ba zai barni in mai da hankali a kan karatun ba”. Ta yi
Table of Contents