Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Yakanah Book One Complete Hausa Novel 609 words 0 views Progress saved
Download Book

ta a rayuwa ya tagayyara shi ba. Sannan kai Sulaiman Hadiza za ta yi farin ciki idan har ya zamto ka rungumi amanar rayuwar ‘yar uwarta ta hanyar aure, muna neman hadin kan ku, za mu samu Fatima da Sulaiman?” Da a ce Malam Sulaiman ya lura, da ya ga irin jibin (zufar) da ke ambaliya a fuska da jikin Sulaiman, yayin da gudun jini ya katse a jikin Fati, idanuwanta suka juye suka kada suka yi jazur, hanjin cikinta ya dunkule waje daya ko dan yatsanta ta kasa dagawa balle ta motsa bakinta. Tana addu’a cikin zuciyarta idan mafarki take Ubangiji Allah subhana ya yi gaggawar farkar da ita. Sai dai a bangaren shi Sulaiman, ya so a ce shi da iyayen shi ne kadai su kai wannan maganar, da a take zai ce dasu idan kasa da sama za ta hadu bai amince ba. To an ce wai ko mutuwa tana kunyar iyaye, balle iyayen Hadiza? Ya zai yi ya iya ya budi baki a gabansu ya ce baya son jinin Hadiza? Shi tunda ya rasa Hadiza bai kara tunanin nan gaba zai kara yin aure ba, bai kara tunanin wai yana da future ba, balle ya yi tunanin yin aure. Kuma a rasa wadda za a aura masa sai wannan yarinyar da bai san a matsayin da ya ajiye ta a zuciyar sa ba. Duk da yadda take hidima da ‘ya’yansa, Fati ba ta taba burge shi ba, Allah bai sa masa kaunar ta a zuciyar sa ba, sannan kuma wai auren ma daga yin arba’in din Hadiza? Sannan da shakikiyar ta? Fati ba ta taba burge shi ba balle ya so ta, bai taba tunanin irin ta a matsayin matar shi ba. Ya ya ma za ai wannan kidahumar yarinyar ‘yar sakandire ta maye gurbin Hadiza? Ta ya ya mahaifan shi suke tunanin zai iya rayuwa da kanwar Hadiza? Ya yada girman sa ya yi mu’amalar aure da ita? Kwarai ya fahimci abin da Hadiza ke nufi tsakanin shi da Fati a ranar da Allah zai dauki ranta, amma (he is sorry to say) ba zai iya cikawa Hadiza burinta ba. In don ‘ya’yan shi ne a ba shi abinsa ya rike ko ya bai wa Inna, ba sai an makala mishi auren da bai san ya ya zai yi da shi ba. Malam Ja’afar ya ce, “Duk kun yi shiru, ko da yake shirun alamar amincewa ne, To ku tashi ku je Allah ya yi muku albarka, dama mun sanar daku ne kada sai gobe ku ji an daura aure ku ce ba a sanar daku ba. In kuma akwai mai magana to ya yi, a shirye muke da mu bai wa kowannen ku hakkin sa”. Inna tana murmushi ta dubi Sulaiman ta ce, “Ni na san mai sunan Malam ba zai ki abin da muke so ba”. Jikinsa ya yi sanyi kalau, ya nemi duk wata hujja da zai bayar ya neme ta ya rasa. Zuwa lokacin Fati ta mike za ta fita, juwa na kwasar ta, da dafa bango ta samu ta bar falon. Ta yi dakinta ta dauki ‘yar jaririyar ta wadda ke ta tsala kuka a dalilin ta manta ba ta sa mata gidan sauro ba ta fita, sauro ya hana mata barci. Shi ma bai yi magana ba yana jin su suna ta kida suna rawar su na addu’o’’l, sa albarka da fatan alheri a gare shi. Gwiwa a salube ya fito jikin mota ya baro su suna ta sallama. Mu tara a littafi na 2. Kuma na karshe inshallahu. Wanda tare suke da dan uwansa. Maman Safah da Marwah ce, ke yi muku fatan alheri. c a _=> – = – —= _= —= – > Advertisements

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18