Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Mutum Ko Aljan Book One Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ __________________________________________________ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ ________________________________________________ *Diamond Star💎 🌟 Ladies 🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 Paid Book ₦500 Free page 7️⃣ Bismillahi rahmani rahim Karasa in da suka ga magen su ka yi, ɗago wa magen ya yi su ka yi ido huɗu da shi, wani irin mage ne da tun da suke ba su taba ganin irin sa ba, Musab kam kallo ɗaya ya yi wa magen ya juya ya koma cikin mota. Shi kuwa Asaf runtse ido ya yi ya shiga karanta ɗan karatun da aka ɗan koya masa. Dan ba wani ilimi ne da shi sosai ba,dan ko s'auƙar alkur'ani ma bayyi ba,amma dai ya fi Aliya ilimi nisa ba kusa ba,kawai dai s'aukan ne da bai samu ya yi ba. Bayan ya ɗan karanta ne ya buɗe ido ya ga wayam ba bu mage,murmushi ya ɗan yi sannan ya miƙe ya bar wajan ya koma cikin mota shi ma, Kallon Asaf! Musab ya yi ya shiga tambayarsa "Magen ya tafi ne ?" Wani irin harara Asaf ya dallawa Musab kana ya ce"Kai ka je ka duba mana, ni ban sa ni ba".Ya kare maganar ya na haɗa rai, Hannu Musab ya sa da niyar buɗe kofar sai Asaf ya yi magana "Kaga malam ka ja motar nan mu tafi " Jin Asaf ya yi magana ne ya Musab fasa fitan da ya yi niyar yi, ya ta da mota. Ta da mota ya ke yi amma mota yaƙi ta shi,kallon Musab Asaf ya yi ya ce. "Lafiya?". "Wallahi! ni ma ban san me ya samu motar ba yaƙi ta shi dan kafin mu fita lafiya lau na du ba motar kuma ba bu wata mas'ala, m'ai ma jiya da daɗɗare na je na sha." "Ɗan fita ka du ba dan Allah! Musab dan gaskiya b'ai kamata motan nan ya lalace mana a wannan k'auyen ba." "Toh shi ke nan bari na je na du ba." Musab ya yi maganar ya na buɗe kofa, Karasa gaban motar ya yi ya buɗe wajan ya dudduba amma bai ga in da ya lalace ba, "Musab ! ya ɗai ka ga in da ya lalace ɗin ne ?". "A'a gaskiya ban ga komai ba amma dai bari na ɗan zu ba ma ta ruwa" "Okay ka zuba muga ni ko Allah zai sa ta tashi ". Ruwa Musab ya je ya ɗ'auka a bayan mota sannan ya zo ya zuba wa motar, Zuwa ya yi ya kara gwaɗa wa amma shiru still yaƙi ta shi, "Yanzu mai abun yi Asaf ?". Ba tare da Asaf ya kula Musab ba ya fito daga cikin motar ya jingina bayansa da jikin motar ya na shaƙar ɗaɗdaɗen iskan dake kaɗawa a wajan yana yi yana lumshe ido,dan shi mutun ne mai son irin wannan iskan. Shi ma dai Musab fito wa ya yi ya zo ya saya kusa da shi ba tare da ya kara tanka masa ba. Dan ya san tsar'ai tunani yake ta in da zai samo musu mafita, Wani ɗottijon ne ya zo wuce wa kan kekensa ya gansu,kallo ɗaya ya yi musu ya gane su na bukatar taimako dan haka tsayawa ya yi a gabansu ya s'auka daga kan kekensa ya karasa in da suke saye "Assalamu alaikum". Ɗagowa Musab da Asaf ya yi suka yi suna amsa sallamar da ya yi musu. "Wa'alaikum salam" Hannu mutumin ya miƙawa Musab suka gaisa sannan ya miƙawa Asaf ma,hannu Asaf ya kawo da niyar g'aisawa da mutumin idonsa ya s'auka a hannu mutumin sai ya fa sa, ya d'auke hannunsa da niyar mai da shi cikin aljihun sai idanun su ya tsarke dana juna, saboda kwanjinin mutumin da kamalarsa bai san san da ya dawo da hannunsa ba, ya miƙawa mutumin alamar su yi musabaha! Murmushi ya dan yi kana ya haɗa hannunsa da na Asaf suka gaisa, Sannan ya shiga tambarsu. "Lafiya suke saye a nan?" "Ina fa lafiya Baba motar mu ce ta samu mas'ala ?" Asaf ya ba shi amsa cikin sakin fuska. Musab kam sai bin Asaf ya ke da kallo dan ya na y'in yan da ya ga Asaf na yiwa mutumin magana ba karamin ba sa mamaki ya yi ba. Dan tun da yake bai taɓa ganin ya sakar wa mutun fuska sosai irin yan da ya sakarwa wannan mutumin ba. Ga shi wannan ko ganinshi bai ta ba yi ba amma ya saki jiki yana ba shi amsa ba tare da ya haɗa rai ko ka ɗan ba. "Subhanallah! Gashi kuma ba mu da bakaniki anan sai mutun ɗaya shi kuma ba ya nan d'azu ya yi tafiya sai dare zai dawo" Kai Asaf ya d'afa kana ya furta"Ya salam yanzu mai abun yi Musab ?" "Wallahi ban sa ni ba ni ma". Dan gajeran tsaki Asaf ya yi kana ya kara kallon mutumin ya ce" Toh Baba yanzu ba bu wani kwata- kwata da ya iya gyara mota sai mutun ɗaya duka k'auyen nan?". "Kwarai kuwa Ɗana sai wanda na gaya muku d'in ne kawai ". "Mas'ala ta da k'auyen ke nan wallahi "Cewar Asaf ! Murmushi kawai mutumin da Asaf ya kira sa da Baba ya yi kana ya ce"Mai zai hana ku je gidana kafin ya dawo". Musab ne ya ce. "Toh Baba mai zai hana dan na san gwara gidan naka s'au dubu a kan tsayuwar titi.ko ya ka ce Asaf " "Haka ne amma dai zai dawo Kafin dare dai ko Baba?" "Eh zai iya dawowa kafin dare zai kuma iya kaiwa dare,kun ga in ya kai dare sai dai ku kwana in ya so gobe da sassafe ya gyara muku sai ku wuce in da kuke son zuwa." "Wai kana nufin in ya kai dare sai dai mu kwana a wannan k'auyen?". "Eh Ɗana haka na ke nufi" Ɗan jim Asaf ya yi kana ya juya ya kalli Musab,kai Musab ya geɗa masa alamar su amince kawai,dan murmushin Asaf ya yi wa mutumin kana ya ce"Shi ke nan muje Baba". Kai Baba ya geɗa musu sannan ya yi musu nuni da su tafi sai suka soma tafiya, Wannan karon Malam Iliyasu bai h'au kekensa ba da kafa yaƙe tak'owa shi ma. "Baba ka h'au keken mana" "A'a Ɗana ku dai bari mu tafi tare yafi dad'i akan na yi gaba ni ƙad'ai ". Murmushi Asaf ya ɗan yi sannan shi ma ya ce"Baba gaskiya abokina ya faɗa ka h'au kekenka, ka ga mu yara ne zamu iya yin dogon tafiya lafiya lau " Wani irin kallo Musab ya yi wa Asaf irin karya ka ke yi d'in nan, Dan tun da yaƙe da Asaf bai taɓa ganin ya yi tafiya mai nisa ba. Amma shi ne yanzu yaƙe cewa su yara ne za su iyayin tafiya mai nisa. Daƙer aka lallaɓa malam Iliyasu ya h'au kekensa suka bisa a baya. Wata ƙwa ta ,ce suka zo sallakawa sai Asaf ya faɗi a ciki, "Subhanallah!". Malam Iliyasu ya faɗi yana s'auka daga kan kekensa sannan ya karasa wajan Musab kam dariya ya kama yi, yan da yaga Asaf cikin ƙwa ta Kunu

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20