Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Mutum Ko Aljan Book One Complete Hausa Novel 1,227 words 0 views Progress saved
Download Book

karki min haka kin ji Bestyna wannan karon cikin rarrashi ta ke magana,amma still Aliya bata tashi ba. Tambayar kansa likita ya shiga yi akan maganar Aljana da Hanifa ta yi yanzu.'Kamar ya Aljana bazai kashe mata Besty ba?Ganin da ya yi ba bu mai basa wannan amsar ne ya sa shi watsar da maganar,"Humm saboda ta riki ce ne kawai ya sa take maganar Aljana"Kai kawai ya girgiza kana ya juya ya yi bakin kofar, Jin karatun da Hanifa ta fara yi ne ya sa likita dakatar da tafiyan da ya yi niyar yi, ya juyo ya zuba mata ido, Ayatul kursiwu da suratul Nasi da falhagi ne ta ke karanta wa ko wanne sai data karanta kafa uƙu _uƙu sai Amanar Rasulu data fara karantashi bata ma karasa ba taji Aliya ta yi wani irin attishawa da karfi haɗe da buɗe ido Aliya na buɗe ido Hanifa ta faɗi ta suma...... Ina so naga ruwan comments dan wancan page din dana turo baku min comments 😒 Yawan comments yawan typing ✍️ Comments and share fisabilillah *Fulanin of Jajirtattu ce ✍️* [24/08, 23:45] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫 MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹 💫 Story and written ✍️ By: Sakeena Isma'il Cameroon (Mom Muwadda) __________________________________________________ Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ __________________________________________________ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ __________________________________________________ *Diamond💎 Star⭐ Ladies🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 Paid Book ₦500 Free Page 4️⃣ Bismillahi rahmani rahim Ba ta ma karasa ba ta ji Aliya ta yi attishawa da karfi haɗe da buɗe ido, buɗe idon Aliya ya ke da wuya Hanifa ta faɗi kasa ta suma, Tashi zaune Aliya ta yi ta shiga kallon dakin kamar wata zararriya haka ta koma sai data karewa dakin kallon saf sannan idonta ya sauka akan na Likita sai a lokacin ta gane asibiti take baki ta buɗe daker ta fara magana "Doctor me ya sa meni ?" Sai a lokacin doctor ya dan motsa daga inda ya ke tsaye ya karasa kusa da gadon dan tun ɗazu yake saye kusa da bakin kofa tun lokacin da ya ga Hanifa ta suma ya kasa kwakkwaran motsi dan sai a lokacin ya samu amsar tambayar da ya yi wa kansa akan maganar Aljana ta Hanifa ta yi akan Aliya. Dan ba karamin tsoro ya ji ba a lokacin da ya ga Hanifa ta faɗi ta suma, "Doctor ina maka magana ka yi shiru" Aliya ta sake dafi a karo na biyu "Sorry! ɗazu ne Mom ɗinki da wannan kawar taƙi suka kawo ki nan kamar gawa muna duba ki muka tarar kin mutu ashe ba mutuwa ki ke yi ba aikin Aljanu ne amma mai kuka masa haka har ya aikata miki wannan danyen aikin?dan na san ba karamin wahala ki ka sha ba saboda a wuyanki na gano hakan" Doctor ya yi magana yana ɗagowa,ya ga wayam bai ga komai ba juyowa ya yi ya ganta durkushe a gaban Hanifa ta na kiran sunanta"Hani! Hani na dan Allah ki tashi me ya sa meki haka ?" Shiru ba amsa, ɗagowa ta yi idonta ya yi jajawur kamar karwashin wuta ta zuba su kan Likita dake saye kamar tsoko yana kallon su. A fusa ce ta saki Hanifa ta miƙe ta tako ta karasa gaban Likita kana ta fara magana "Wai kai wana irin Likita ne?taya bestyna ya suma ba za ka taimaka mata ba?ko uniform naka na karya ne kawai?". Sai a lokacin likita ya saƙi murmushin mai ciwo dan maganar Aliya ya dan ɓata masa rai "Humm! Aliya ki Ke ko wa? Naji Bastyn naki na kiranki dashi.toh ba ni ne tsilar saka Bastyn ki a wannan halin da ta ke ciki ba.ke ce tsila dan haka ke ya kamata ki taimaka mata kamar yanda ita ta taimaka miki a lokacin da ki ka suma"Likita na gama fad'ar haka ya juya a fusa ce ya yi bakin kofa ga t'ausayin Hanifa dake ratsa mai zuciya yana son yi mata addu'a amma yana tsoron a bin da zai je ya dawo, Har ya dora hannunsa samar kofar da niyar buɗewa sai ya ji ta yi magana cikin sanyin muryar"Dan Allah likita ka fahimtar dani wallahi bangane in da maganarka ta dotsa ba sam".Ba tare da Likita ya juya ba ya ce "Mu a lokacin da aka kawo ki nan muna yin bincike muka gano cewa kin mutu amma Bestynki ta ce sam baki mutu ba dan har magana nayi mata akan cewa me ya sa ba za ta d'auki jarabawan da Allah ya aiko mata dashi ba ta nuna sam ita bata yedda ba a taƙai ce dai ita ta miki addu'a cikin idon Allah ki ka farfaɗo nima da ki ka farka ba karamin mamaki na yi ba.dan haka kema yanzu ya kamata ki yi wani abu ta samu ta farfaɗo" Hawaye Aliya ta share kana ta ce"Ni wallahi ! doctor ban iya karatu ba". "Toh amma ai kin iya karanta suratul nasi da kuma falhagi.ko suma baki iya ba?" "Ummm !toh shima na fara mantawa".Cikin mamaki doctor ya ke kallon Aliya dan har mamakin ya kasa ɓoyuwa akan fuskarsa "Yanzu kina nufin shima kin manta shi?"."Eh "Aliya ta bashi amsa. "Toh in kina sallah me ki ke karantawa"?."Wallahi ni na kwana biyu ban yi sallah ba gaskiya"Aliya ta faɗa ba tare da ta ji kunya faɗa ba. "Hummm! Allah ya shiryeki wannan a bu In da ki ke yi ma ai dole Aljanu su samu wajan shigarki a duk lokacin da suke so". Ido Aliya ta zaro waje cikin tsoro da firkici Aliya take tambayar doctor. "Doctor ! Kana nufin saboda bana sallah ne ya sa Aljanu shiga jikina ?"."Kwarai kuwa dan da ace kin rik'e addini ba bu a bin da zai sameki ko ya sameki ma ba za ki sha wahala sosai ba,ni dan Allah bani waje na duba ta" Doctor ya yi magana haɗe da fara takowa ya nufi in da Hanifa ta ke kwan ce Durkusawa ya yi gabanta hannusa biyu ya sa ya dago kanta ya gora saman cinyarsa rumtse ido ya yi ya buɗe dan tunda ya ke bai taɓa jin a bin da ya ji yau ba.bakin sa ya s'aita dai _dai kunnenta ya fara mata karatu, Bai wani dau lokaci sosai ya na karatu ba ya ji ta fara sauke ajiyar zuciya a samar fuskarsa wani irin ya ji a lokacin da ji saukar numfashin ta a saman kunnan sa Kara runtse ido ya yi a karo na biyu wannan karon bai buɗe idon sa ba, a haka ya ci gaba da karatu, Tun lokacin da doctor ya fara karatu Aliya ya zuba masa ido bata taɓa na dama akan rashin karatun da bata yi ba sai yau, yana y'in yanda doctor ya ke karatun ba karamin burgeta ya yi ba,har ta ji da ma ita ce, Buɗe ido ta yi a hankali ta dora a kan fuskar sa kallon sa ta ke ba bu ko kiftawa yana da kyau ba laifi duk da kuwa baƙi ne amma komai nashi mai kyau kama daga hanci har fuska,idonta ne ya sauka

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20