Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Mutum Ko Aljan Book One Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

raba ka da wannan muguwar Aljanar lafiya " Tsaki duk suka ji an yi su na juyowa suka ga Aunty Jamilah ce ta yi,kafin su yi magana ta miƙe ta bar palon ta wuce bangarenta,suka bita da kallon mamaki. Miƙewa ya yi ya je gaban akwatinsa ya kwantar da akwatin a hankali ya buɗe ya d'auƙo kwalbar da aka rufe Aljanar Mazwara a cikin wanda Malam Shuaibu ya kawo masa da daddare ya ce in ya koma gida ya samu wajen da ba wanda yake shiga a cikin sai family dinsu kawai ya samu waje mai kyau a ciki ya boye kwalbar . Ya ce wa Malam Shuaibu mai zai hana shi ya ajiye kwanbar a wajan shi.ya ce a'a shi ba shi da wani mahalli mai kyau da zai ajiye mai a cikin dan in har ya ajiye zai samu yaran da za su buɗe kwalbar ku ma in an buɗe aiki zai dawo baya, Juyowa ya yi ya kalle su ɗaya bayan ɗaya ya ce " " Kunganta gata nan ɗuk suka miƙe suka taho in da yake ido huɗu suka yi da Aljanar Mazwara cikin kwalba sai mutsu _mutsu take tana zazzare ido,cikin tsoro Mom ta kalli Asaf ta ce "Kaga Asaf ta shi ka je ka ɓoye ta a ɗak'in ma ajin kaya na musamman "." Da toh "Asaf ya amsa sannan ya maida kwalbar cikin akwatin ya rufe ya yi musu sallama ya wuce cikin. Ya na barin wajan bai saya ko ina ba sai cikin ɗak'in ajiye kaya na musamman. Waje na musamman ya nemo ya tire kwalbar daga cikin akwatin ya ɓoye. Sannan ya juya ya fita daga cikin ɗak'in ya sa key ya kulle ɗak'in sannan ya ja akwatinsa ya bar wajan ya nufi part dinsa..... *Fulanin of Jajirtattu ce✍️* Comments and share fisabilillah 👏 [20/09, 23:15] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹💫 Story and Written ✍️ By: Sakeena Isma'il Cameroon (Mom Muwadda) ________________________________________________ Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ ________________________________________________ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ ________________________________________________ *Diamond 💎Star 🌟 Ladies* 🧝‍♀️ *(We stand together)* 🤝🤝🤝 Paid Book ₦500 Free page1️⃣1️⃣ Bismillahi rahmani rahim Sannan ya juya ya fita da ga cikin ɗakin , ya sa key ya kulle ɗakin, sannan ya ja akwatinsa ya bar wajan ya nufi part dinsa, Yana zuwa part dinsa bai saya palo ba ya wuce ɗaki darek, Yana shiga ya ajiye akwatin gefen wardrobe d'insa ya shiga rage ƙananan kayan da ke jikinsa. Bayan ya kammala rage kayan ne ya d'auki tawol ya d'aura ya wuce toilet, Sai a lokacin na karewa ɗakin kallo. Komai na ɗak'in fari da gwalɗin ne,kama daga bed, wardrobe, dressing mirror, carpet ɗin da ke sakiyar dakin har ma da kujerar mai zaman mutun biƴun da ya saka a can gefe,ɗuk fari da gwalɗin ne,sai lamulayen ne ƙad'ai mai kala gwalɗin. Ɗakin ya haɗu iya haɗuwa,dan ita wardrobe din sakiyar sa ma glass ne. Bayan na karewa ɗakin kallo na fita na ja masa ƙofa na wuce wajan su Siyama dan ganin me suke yi a cikin ɗakin baƙin da aka ba su😂 *Bangaren su Siyama da Goggo* Bayan Sa'ade ta kai su wani haɗɗan wani ɗakin baki mai masifar kyau ne ta nuna mu su komai har da toilet ta fita ta bar su. Ɗakin d'auke yake da ƙananun gaɗo guda ɓiyu sai dan karamin wardrobe a sakiya Ɗakin ya yi kyau ba bu laifi, Goggo ce tun da ta shigo ɗakin take nuna k'auyenci, Ta taɓa wannan ta taɓa wancan Ni kam sai kawai nake girgiza wa. Ɗuk da kuwa ni ma ina so na yi kallon amma in na yi za su raina ni tun yanzu shi ya sa na dage na haƙura Baki na buɗe na ce "Haba Goggo mai haka dan Allah ki dena nuna wannan k'auyenci karki zubar min da mutunci tun yanzu,yanzu ma kina ganin ko kallo bamu ishi wa su ba.ba dan yellow na da kirki ba ma da tuni mun daɗe da barin gidan nan" Na ƙare magana ina mai miƙawa daga kan gadon da nake zaune,na wuce toilet domin yin alwala dan Allah ma ya sani ba zan yi wanka yanzu ba.tun da ban daɗe da yi ba. Har na buɗe kofar toilet zan shiga sai na ji Goggo na cewa" Mara kunya in ba ki yi haka ba ma baza'a gane Zainabu ce uwar....".Goggo ba ta karasa magana ba ta ji ina cewa"Goggo yi sauri ki zo ki ga wani abu ".Yana yin yan da na yi maganar ne ya sa Goggo saurin karasa in da nake kafin Goggo ta buɗe baki ta yi magana idonta ya sauka in da nake kallo. Toilet ne mai kyau hadda su mirror da bahon wanka da dai sauran su. Toilet din ya yi kyau ba laifi, Goggo ce ta kalli Siyama ta ce "Wai Siyama anya wannan bayan gida ne kuwa ?"."Eh Goggo bayan gida ne,saboda na taɓa gani a wani film ni da Indo lokacin da mu ka je wannan gidan kallon ta unguwar mu ". "Ki na nufin gidan kallon na Ado ?". "Eh can nake nufi Goggo". " Rannar zagayowa ranar haihuwata ce Baba ya ba ni ɗari biyar shine na d'auki Indo muka tafi gidan kallo aka saka mana film mai dad'i , a cikin film din ne aka nuno wata yarinya ta shiga toilet ɗin ta hau wancan abun ".Ta faɗa tana nuna wa Goggo mats'ai Kallon wajan Goggo ta yi ta ce " Ikon Allah !yanzu Siyama ki na nufin a nan zan hau in ina jin kashi?"."Kwarai kuwa Goggo tsaya ma ki ga na nuna miki". Na faɗi ina shiga cikin toilet ɗin, Zama na yi akan mas'ai ɗin. Ina washe baƙi ,na ce " Goggo ha ka zaki dinga yi kin ga in kin gama sai ki ta shi ki ɗanna anan ". Na faɗi ina saƙin ihu kamar mara hankali, Saboda yana yin yan da na ji wannan abun da yake kore kashin dana taɓa yana ɗan yin kara. Dariya Goggo ta saƙi tana tafa hannu, "Yauwa Siyama fita toh da ma kashin nake ji " "Kai Goggo wai ke ko kunya ma bakya ji ne ? Zaki din ga wani cewa kashi_ kashi dan Allah in wani ya shigo fah " Goggo ba ta ce komai ba ta karasa cikin toilet din,ci kanta ban ce ba. na juya zan fita ban san ya aka yi hannuna ya taɓa wajan kunna famfon saman nan ba. kawai saukara na yi a kaina. Goggo na ganin haka ta fashe da dariyan mugunta. Ƙ'ok'arin kashe famfon nake amma na ƙasa, Da yake ina da cutar limoniya ne ya sa bana son ruwa san yi ya taɓa mun jiki ko ka ɗan ballanta na a kai, Shi ya sa ko a gida in na je wajan ɗibar ruwa da zarar na ga haɗari a gari nake yin saurin komawa gida. Numfashi na ne ya din ga yin sama da kasa. Ya fito daga wanka kenan sai ya tuna da su, "Kai shaf na manta wallahi ban gaya wa Sa'ade ta

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20