Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Mutum Ko Aljan Book One Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
Download Book

saboda yan da Bedsheet din ya baci da jini. Zaro ido waje ya yi ya matso yana taɓa jinin dake kan gadon,ya ga tabbas jinin ne. "Ya salam ". Ya furta. "Allah! ya isa saka nina dake Aljanar Mazwara kike ko wa? Allah.ba zan taɓa yafe miki ba,haka kawai ka sani ina koƙarin kashe ƴar muta ne a banza,yarinya kara ". Iska mai zafi ya busar daga cikin bakinsa kana ya juya fuuu kamar zai ta shi sama ya wuce inda jallabiyansa yake ya dauka ya saka ya ɗauki key ya fita ya kullo kofar ya wuce part din Mom dinsa. Tana sallar dare ta ji ana mata nocking ɗin kofa,kallon Dad da ke kwance yana bacci ta yi,kana ta miƙe ta nufi bakin kofa da sauri gudun kar mai nocking ɗin ya kara wani nocking ya ta shi Dad. Tana karasa bakin kofa aka kuma yin wani nocking din. " Waye?". Ta faɗi, "Mom ni ne ". Ta ji Asaf ya yi magana, "Muhammad Asaf kai ne a daren nan ?". "Eh ". Ya ce a taƙai ce. Buɗe kofar ta yi ka ɗan ta leka,ganin da gaske shi ne din ne ya sata buɗe kofar gaba ɗaya. Kallonsa ta yi ta shiga tambarsa "Asaf lafiya na ganka da sakyar daren nan?". "Mom dan Allah biyo ni akwai mas'ala na kusa kashe ƴar mutane ". Ya faɗi yana kamo hannun Mom. "Dakata Asaf ka saya ka yi mun baya ni tukun ta yanda zan fahimta,wa ka kusa kashe wa ?". "Kinga Mom in mun je can ki ya samu duka amsar tambayoyinki a can yanzu dai dan Allah !ki zo mu je ". "Shi ke nan bari na rufe kofa ". Mom ta faɗa tana tire key dake kan kofar, Kulle kofar ta yi ta waje sannan ta kalli Asaf ta ce " Mu je". Kai kawai Asaf ya geɗa mata da shi sannan ya kama hannunta suka wuce part dinsa. *Part din Asaf* Suna zuwa ba su saya ko ina ba sai cikin ɗakin,sai yanzu Hajiya Rukayya ta fahimci akan wa Asaf yake magana,cikin tashin hankali ta juya ta kalli Asaf ta ce "Asaf tana ina ?kuma mai ka yi mata ?". "Mom Mazwara ce take son sani na yi kisan kai". "Wace ce Mazwara kuma ?". Mom ta tambayi Asaf. "Mom wannan fa aljanar ce, da ta hanani aure ". "Toh ba ita ce aka rufe cikin kwalba_ ba ?". "Eh Mom ita ce,ni ma abun ya bani mamaki sosai,dan Siyama ta ganta ido da ido dan har barazana ma ta yi mata ". "Zo kiga wani abu Mom". Asaf ya fadi yana kara kamo hannun Hajiya Rukayya suka nufi baƙin gado . Jinin ɗazu da ya gani ne ya nuna wa Mom dinsa, Mom na gani ta shi ga furta "Innalillahi wa inna ilahi rajiun !." Shi ne kalmar da take ta maimaita wa ke nan. "Yanzu kana nufin Asaf kai ne ka yi wannan ɗanyen aikin ? Yanzu tana ina ?". Toilet Asaf ta nuna mata da hannu ta juya a fusa ce ta yi hanyar toilet ɗin. Tana zuwa bakin kofar toilet din ta murɗa da niyar shi ga ta yi kicimis da Siyama za ta fito, Sai cize labe take ,tana daɗdafa bango tana ganin Mom ta juya za ta koma toilet dan kunya fito da tawol a gabanta take yi. Saurin rike hannunta Mom ta yi, Siyama kamar jira take sai kawai ta faɗa jikinta ta saƙi wani kuka mai suma zuciya, Mom bata hana ta kukan ba, ta barta sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shiru tana maida numfashi, Karaso wa bakin kofar toilet din ya yi ya na fadin " Haba Mom barinta fa kika yi tana kuka?". "An barta ɗin,kai ba kaga abunda ka yi mata ba?mara kunya kawai ". Asaf bai ce komai ba sai ma karaso wa da ya yi ya sungumi abarsa sai cikin ɗaki. Akan kujera dake cikin ɗakin ya ajiye ta,kana ya je gaban wardrobe ya buɗe ya tiro wani Bedsheet din ya zo ya ya ye wan can ya shimfida wanda ya ɗauko. Lokacin Mom ma har ta karaso wajan Siyama, Bayan Asaf ya kammala gyaran gadon ne ya sake zuwa ya ɗauko ta ya kai ta kan gadon. Kallon Asaf Mom ta yi ta ce " Ka fita ka bamu waje ka koma palo in mun gama komai za mu yi magana?". Baki Asaf ya buɗe da niyar yin magana sai Mom ta haɗa rai ,ba shiri Asaf ya bar ɗakin ya koma palo. Ƴata Siyama kwanta,ba musu na kwanta, ɗuk da ina son yin magana amma ba fuska, Dan har ga Allah ba na son kwanciya da wannan tawol din a jikina,tun da a gida ma,zani nake d'aura wa idan na ta shi yin wanka. Yanzu ma dalilin da ya sa na d'aura tawol din ban samu abun d'aura wa ba ne,kuma ba na son fitowa a haka.shi ya sa Kawai na d'aura. Bayan na kwanta Mom ta saka hannunta ta kwance tawol din dake jikina ta shiga ware min kafafuna, Saurin haɗe kafafun nawa na yi na shiga faɗin "Dan Allah! Hajiya ki yi haƙuri ". "Siyama da ma ɗa yana boyewa uwa wani abu ne ?". "A'a ".Na fada, "Toh in dai har ɗa baya boyewa uwa wani abu ina so ki bani haɗin kai a matsayina _na mahaifiyarki kuma tsohuwar likina na duba ki ". Ido na zaro waje kana na ce"laa! Hajiya ke ma likita ce ?". Kai Mom ta geɗa min tana dan yin murmushi,saboda daga yana yin yanda take magana zai tabbatar maka ita din yarinya ce, Duba Siyama Hajiya Rukayya ta yi, taga iri barnar da ɗanta ya yi mata. Tunda taga wajan ta san ba karamin ɗauriya Siyama take yi ba. Wani irin t'ausayinta ne ya kamata , Dole ta yi mata dinki,ta kuma samo mata paracetamol ta sha kar zazzabi ya rufe ta,amma kafin nan dole sai ta fara sanin meye faru ?mai kuma wannan aljanar ta faɗa mata ? Gyara zama Mom ta yi kana ta kamo hannun Siyama ta hada da na ta ta shiga tambayarta . "Siyama ina so ki fada min duk abunda ya faru tun daga farko har karshen saboda mu san ta inda zamu bullowa alamarin ". "Toh ". Na ce sannun na shiga bata labarin abunda ya faru saka ni na da Sir yellow,har da abunda Mazwara ta fada min ɗuka ban boye mata ba. Cikin mamaki da kuma tashin hankali Mom ta saki hannuna ta mike ta fita ta bar ɗakin, Tana fita ta samu Asaf a palo, Asaf na ganin Mom dinsa ya mike yana tambayarta "Ya Mom kin duba ta ne ?". "Na duba ta naga aika_ aikan da ka yi ". "Mom wallahi ba da sani na ba ne na aikata mata wannan abun,asali ma ni ban san lokacin da wani abu ya shiga saka nin mu ba.sai bayan angama komai.....". "Gaga daka ta asaf !ta fada min duk abunda ya faru zo ka raka ni ɗakin ajiye kayan sirri na duba in ina da kayan aiki acan na zo na na yi mata ɗinki,dan dole sai an yi mata ɗinkinki sannan zata dawo daidai ". "Toh

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20