Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Mutum Ko Aljan Book One Complete Hausa Novel 1,239 words 0 views Progress saved
Download Book

ba aka fusgi wayan da ke hannunta dago wa ta yi taga Maman Aliya ce saye gabanta idonta ya yi jajur saboda kukan data sha. "Hello yauwa bari ku ji wallahi idan ƴata ta mutu sai na yi sharia da ku ta na kaiwa nan kitt ta katse kiran, "Mommy! Ya jikin Aliyan? Ta farfaɗo ne ?" Hanifa ta tambaya,baki Maman Aliya ta buɗe da niyar bawa Hanifa amsa sai suka ji muryar likita a bayan su,duk juyo wa suka yi suka buɗe baki a tare suka shiga tambayar likitan "Likita ta farfaɗo ne ? Shiru likita ya yi na ɗan wani lokaci kana ya ce "Ku yi haƙuri Hajiya tun da na shiga na ɗubata na tarar Allah ya yi mata rasuwa kuma da dukkan alamun sun nuna cewa ta sha wahala sosai kafin ta rasu kuma ku san minti talatin ta yi da rasuwa dan ba yanzu ta rasu ba". Wani irin ihu Maman Aliya ta kurma kana ta ce"Wallahi Karya ne wallahi basu isa ba wallahi ba zan yedda ba sai sun dawo min da ƴata dan su ne silar komai su suka kashe min ƴata"ta na kaiwa nan fuuu tabar wajan kamar za ta tashi sama ta yi bakin kofar fita a sibitin sai data kai bakin kofar sannun ta juya ta kalli Hanifa da jajayen idanunta ta ce "Hanifa ki zauna da ita bari na je na dawo"Ta na kaiwa nan bata saya jiran mai Hanifa zata ce ba ta karasa fita. Kai kwai likita ya girgiza sannan ya juya ya bar wajan ya wuce offince dinsa,ita kuma Hanifa ta wuce dakin da Aliya take. Cikin tsoro na ke guɗu ƙare na bina a baya ban saya ko ina ba sai a gaban wani dan karamin kofa turo kofar na yi da sauri naci karo da wani dattijo da alama fita zai yi da guɗu na karasa na buya a bayansa ina ɗan leko da kaina kaɗan dan gani in karen"Siyama laifiya kika shigo mana gida ba bu ko sallama?".Ba tare data yi magana ba ta nuna mai karen da ke gabansa da hannunta,sai a lokacin Babban ya lura da karen da ke gaban nashi kansa ya girgiza yana murmushi kana ya ce "Haba Diyana wai yaushe zaki yi girma ne ?" Mai ma kon ta bawa Baban amsa sai ma kara riƙe shi data yi,ba tare da Baban ya yi magana ba ya shiga koran karen,babu jimawa karen ya tafi sai a lokacin yar buduwar ta fito daga bayan mahaifinta... Kuyi haƙuri da wannan jiya na dawo na gaji Comments and share fisabilillah 👏😍 *Fulanin of Jajirtattu ce ✍️* [22/08, 16:23] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫 MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹 💫 Story and written ✍️ By: Sakeena Isma'il Cameroon (Mom Muwadda) __________________________________________________ Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V __________________________________________________ Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ __________________________________________________ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ __________________________________________________ *Diamond💎 Star⭐ Ladies🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 Paid Book₦500 Free page 3️⃣ Bismillahi rahmani rahim Ba bu jimawa karen ya tafi sai a lokacin 'yar buduwar da a shekaru ba za ta haura 16 ba. fitowa ta yi da ga bayan mahaifin na ta,sai a lokacin na kare mata kallo sosai, kyakkyawa ce ajin karshe,ta na da dogon fuska da kuma dogon hanci sai dan karamin bakinta dake d'auke da Pink din lips sai zara zaran gashin ido da kuma ta gira,ba ta da wani haske sosai,dan kuwa ba za'a kira ta da fara ba.ba za kuma a kira ta da baƙa ba.irin kalan farar nan nata ne ake kira da wankan tarwaɗa. Siririya ce amma ba sosai ba ,ta na da books da kuma hips sosai,idan aka ganta zaka d'auka ta yi shekara 20 nan kuwa 16 ne kawai saboda har tsayi ma ta na da ita ma sha Allah! Kallon mahaifina na yi ina murmushi haɗe da turo baki gaba kana ganin yanda nake yi kaga yarinta a tattare da ni "Siyama ina ruwan da ka ɗebo?".Ware manya _manyan idanuna na yi waje dan sai a lokacin na tuna da abun ɗiba ruwa na dana yer a hanya saboda karen daya biyo ni,bakina na buɗe na ce "Laa!wallahi Baba ruwan ya ɓare a hanya"."Toh da ki ka barar da ruwan ina botiƙin ya ke?"Wallahi harda shi na bari a hanya na dawo gida saboda wannan karen"."Wai ni Siyama yau ki ka fara ganin kare ne?"."A'a Baba ni fah bana tsoron kare kawai dai idon karen ne ya bani tsoro saboda tunda na ke ban taɓa ganin idon kare green ba sai yau ga kuma wani irin kallo da ya ke min shi ya sa na ji tsoro na guɗu shi kuma ya biyo ni ". Shiru Malam Iliyasu ya yi yana nazarin maganar yar tasa,dan tabbas shi ma ya lura da idon karen "Tabbas ni ma naga idon karen amma kin san ba bu irin yanda Allah baya halittan abu ke dai abun da na ke so dake karki watsa da addu'a a ɗuk in da ki ke Allah yana tare da ke" Kaina na gyaɗa ina faɗin "Toh Baba in sha Allah zan yi kamar yanda ka ce " Shafa kaina Baba ya yi yana faɗin"Allah ya yi miƙi albarka".Na amsa da"Ameen" sannun na shige gida shi kuma Babana ya wuce ma sallamaci, *Bangaren su Hanifa* Cikin ɗak'in da Aliya take ciki ta nufa ta na zuwa ta turo kofar a hankali ta shiga ta maida kofar ta rufe hango Aliya ta yi an lulluɓe ta da farin zanin gadon asibitin,wani irin kuka ta saki da s'auri ta kara so kusa da gadon hannunta na rawa ta sa ta yaye abun da aka rufe ta da shi ido huɗu ta yi da fuskar Bastynta ga idonta dake a rufe ga kuma gefe _gefen fuskarta da ta yi jajawur saboda wahala data sha jijjigata ta shiga yi ta na kiran sunanta "Besty ! Besty!dan Allah ki tashi karki min haka.dan Allah karki tafi ki barni me ya sa ki ka ƙi yerda da shawarata Besty? Sai dana faɗa miƙi ki haƙura da Asaf amma kink'i yeɗda.gashi yanzu sun kashe min ke dan Allah ki taimaka ki tashi karki mutu yanzu muna da buririkan de ya wa daya kamata mu cika shi"Haka Hanifa ta dinga faɗa ta na yi ta na girgiza Aliya ta na kuka,ana haka ne likitan ɗazu ya turo kofar ya shigo ya sameta, Kallon Hanifa ya yi ya ce"Haba baiwar Allah me ya sa baza ku karɓi kaddara ba ? Ya kamata ku karbi jarabawan da Allah ya aiko muku da shi hannu bibbiyu kufah muslimai ne bai kamata ku dinga yin haka ba". Wani irin kallo Hanifa ta jefawa likata da shi,likita bai san sanda ya haɗiye sauran maganar da ya yi niyar yi ba, "Karka kara cewa Bestyna ta mutu dan Bestyna ba yanzu zata mutu ba,ko yanzu zata mutu ba dai Aljana zata kashe ta ba dan haka ba ruwanka kawai ka kyaleni" ta na kaiwa nan taci gaba da kiran sunan Aliya "Aliya tashi kin ji haba Aliyata

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20