Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

Mutum Ko Aljan Book One Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
Download Book

ya yi mata ba,da zata zauna tana kuka. Kawar da zancen yayi a cikin ransa ya saka hannu ya shiga share mata hawayen dake zubowa. Ina cikin kuka na ji ana taba min fuska,saurin bude idona na yi ina cewa "Wallahi munfi karfin ki Mazwara ta Allah !ba "….. Ganin shine_ne ya sani yin shiru ban karasa maganar da na yi niyar yi ba,na ja bakina na yi shiru. "Ke dawa kike magana ?".Ya jefa min tambaya, Mai ma kon na ba shi amsa sai ma kara magana da na yi "Dan Allah ka daga ni zan je toilet ". Wannan karon bai ce min komai ba,dan shi mutun ne da in har an haɗa shi da Allah! toh magama takare. Daga ni ya yi na sauka daga kan gadon ina cize labe,hannuna na saka ina rufe irjina, ɗayan hannun kuma na rufe bayana da shi, na nufi toilet ina dan dingisawa. Wani irin zaro ido waje ya yi a lokacin da idanunsa ya sauka akan cinyoyinta da ta baci da jini, Jinin har ya fara bushewa. Ai yana ganin haka bai san lokacin da ya diro daga kan gadon ba,ya nufeta da sauri, Yana karasa inda take bai yi wata _wata ba ya d'auke ta cak ya nufi toilet da ita, Bai a jiyeta a ko ina ba.sai a cikin ɓahon wanka, Sugunnawa ya yi ya kama hannunta ya shiga yi mata tambaya kamar haka "Siyama me ye same ki naga jini akan cinyoyinki ". Kallon mamaki na saya yi masa Tunawan da na yi da maganar Mazwara ce ya sani shanye mamakina na ce "Kai ne mana ?". Cikin mamaki yake kallon ta har zai yi magana sai kuma idonsa ya sauka akan gabansa da ya baci da jini shi ma, Cikin mamaki ya ɗago ya kalleta ya kara matse hannayenta cikin nasa, kana ya ce "Ina so ki faɗa min duk abunda na yi miki daga farko har karshe ba na so ki boye min komai,idan kuma kika boye min wani abu toh zan yi miki abunda yafi wanda na yi miki ". Ya kare maganar yana dan haɗe rai dan ya san in ya sakar maya fuska ba lallai ne ta fada masa komai da komai da ya faru ba. Labarin abunda ya faru na faɗa masa har da maganganun da Mazwara ta faɗa min,babu abunda na boye masa. Bayan na kammala bashi labarin komai ne na dago ina share kwallan da ya zubo min, Ido muka haɗa muna haɗawa wani irin runguma ya yi min yana sakin kuka kamar karamin yaro,yana yi yana cewa "I'm so sorry my heart! Wallahi ba san san da na yi duka wayennan abubuwan ba,dan Allah ki yi hakuri kin ji ?".Ya faɗi yana kara rungumeni a jikinsa kamar akwai wanda zai kwace mishi ni, Ajiyar zuciya na sauke na ce"Wallahi Sir yellow ba laifinka ba ne ". Sa ki na ya yi ya ɗora hannunsa kan bakina ya ce "Shiiiiii ! Karki kara cewa ba ni da laifi ina da laifi, Yanzu da a ce ban fara taɓa ki ba.da babu abunda zai faru da ke ". "Toh shi ke nan,na ji ka yi laifi kuma na yafe maka ". Murmushi ya dan yi kana ya ce" Da gaske kin yafe min ?". Kai kawai na geɗa masa ya tashi tsaye ya kalle ni ya ce"Ina zuwa bari na je na kira Mom ta zo ta taimaka miki ki yi wanka dan ni ban san ya zan yi ba gaskiya,kuma daga nan ina so na san ya aka yi wannan aljanar ta fito ?". Ya faɗi sannan ya juya zai bar wajan na yi saurin rike masa hannu daga zaunen da nake. Na ce "A'a dan Allah ! karka kira kowa ni wallahi kunya nake ji". Murmushin ya sakar min sannan ya ce"Toh shi ke nan ba zan kira kowa ba.bari na dawo yan zun nan ɗaki kawai zan je ". Bai saya jin mai zan kara cewa ba ya bar toilet ɗin. Wayarsa ya ɗauka ya daddawa doctor Jamil kira, Doctor Jamil da bai daɗe da idar da sallar daren da yake yi ba ya ji wayarsa na ringing,ka san cewa shi doctor ne shi ya sa ko karfe nawa aka kira shi baya ba shi tsoro. Duba wayan ya yi yaga Asaf ne yake kiran shi,cikin mamaki yake kallon kiran dan tunda yake da Asaf bai taɓa kiran shi kamar wannan lokacin ba. Ɗagowa ya yi ya ce "Sir Asaf lafiya kuwa?". Ɗan sosa ƙeya Asaf ya yi kana ya ce "Lafiya lau doctor da ma ina so ka faɗa min waca irin taimako za'a ba wa macen da bata taɓa sanin na miji ba?". Faɗawa Asaf yan da zai yi doctor Jamil ya yi,bayan ya gama baya ni godiya Asaf ya yi masa kana ya katse kiran, wayan ya ajiye ya juya ya koma toilet din....... *Fulanin of Jajirtattu ce ✍️* Comment's and share fisabilillah 👏 [28/09, 16:26] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹💫 Story and Written ✍️ By: Sakeena Isma'il Cameroon (Mom Muwadda) ________________________________________________ Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ ________________________________________________ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ ________________________________________________ *Diamond 💎Star 🌟 Ladies* 🧝‍♀️ *(We stand together)* 🤝🤝🤝 Paid Book ₦500 Free page 1️⃣4️⃣ Bismillahi rahmani rahim Faɗawa Asaf yan da zai yi doctor Jamil ya yi,bayan ya gama yi masa baya ni,godiya Asaf ya yi masa kana ya katse kiran,wayan ya ajiye ya juya ya koma toilet ɗin,domin taimaka mata ta yi wankan. Yana shiga toilet din ya tadda ita tana zaune a cikin bahon cusa kanta cikin cinyoyinta tana kuka. A gigice ya karasa kusa da ita ya sugun na a gabanta ya ɗago fuskarta, Ɗagowa na yi amma kaina na kasa na kasa ɗago wa na kallesa. Tallafo duka kuma tuna ya yi ya ce "Kin ga my heart ɗago ki kalle ni ". Ɗago idanuna _na yi na ɗora su a kansa, Kwayar idanunsa na kallon nawa ya shiga tambaya ta " Ya aka yi? Me ya saki kuka? Ko wani abu na kara yi miki bayan wannan?". Ya jero min wayenan tambayoyin ɗuka a lokaci ɗaya. Kara fashe masa da kuka na yi ina nuna mai gabana dake min zafi da dayan hannuna, "Sorry okay? Bari na yi miki wanka zaki ji dad'in jikinki in sha Allah!". Kaina kawai na iya geɗa masa dan ba zan iya yin magana ba,dan wa ni irin azabar zafi nake ji a gabana. Kamar yan da doctor Jamil ya kwatan ta masa haka ya yi wa Siyama, Dan kuwa sai ɗaya saka ta a cikin ruwan zafi s'au shiɗa sannun ya kyaleta,ya fita ya barta ta yi wankan tsarki. Ba laifi da ya saka ni a cikin ruwan zafi na ji dad'in jikina sosai, ɗuk da kuwa har yanzu wajan bai dena min zafi ba,amma Alhamdulillah ! Miƙe wa na yi na fara wankan tsarki. Yana fita daga cikin toilet ɗin,ya wuce kan dagon da niyar gyara wa, Yana tire bargon dake kai idonsa ya yi tozari da jinin dake kan gado,kai sai ka ɗauka rago aka yanka

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20