Chapter 10
Chapter 10
ta kalli kayan da ke cikinsu ta ɗaure fuska ta juya ta kalli Asaf ta shiga tambayarsa "Asaf su waye way'ennan kuma ?". Ɗan haɗa rai shima Asaf ya yi sannan ya buɗe baki ya ce "Haba Aunty Jamilah daga dawowa.ko shigowa ba mu yi ba shine zaki saya kina min tambaya ".Baki Aunty Jamilah ta buɗe da niyar kara yin magana sai ta ji Hajiya Rukayya ta yi magana"Bar su _su shigo Jamilah ?". Ba shiri Jamilah ta matsa, Kallon su Siyama da jikinsu ɗuk ya yi san yi ya yi ya ce "Ku zo mu shiga daga ciki ". Kai suka geɗa masa sannan suka bi bayan sa, Da suka shiga palon gidan suka haɗu da ƴayyan Asaf a palo da suka gansu suka buɗe baki za su yi tambaya su na haɗa ido da Mom ta girgiza mu su kai alamar su bari ba yanzu ba. Sai kawai suka haƙura suka yi shiru, Kallon su na yi na ce "Ina kwan ku ?" "Da lafiya lau suka amsa gaba ɗayan su amma ban da Aunty Jamilah da ta suƙe fuska kamar bata taba yin dariya ba. G'aisawa suka yi da goggo ma kafin Hajiya Rukayya ta fara kiran mai aikin su. Mai aiki Hajiya Rukayya ta shiga kwallawa kira "Sa'ade! Sa'ade!!. Can ciki aka amsa da"Na'am Hajiya gani nan zuwa ". Ba bu jimawa wacca aka kira da Sa'ade ta karaso palon Har k'asa ta durƙusa ta ce"Hajiya Babba gani ?".Ki je da way'ennan baƙin ki kai su ɗak'in baƙi su samu su yi wanka". " Toh Hajiya ", Sa'ade ta amsa sannan ta kalli su Goggo ta ce "Ku zo,na kai ku ma s'auƙin ku". Kai Goggo ta geɗa sannan ta juya ta fara bin bayan Sa'ade,jin bata ji Siyama a bayanta ba ne ya sa ta juyowa ta ganta saye in da ta barta, "Ki zo mu tafi mana " Ban tankawa goggo ba na juya na kalli yellow mutumin muna hada ido ya geɗa min kai alamar na bisu,kai na geɗa sannan na bi bayan su Goggo, Da kallon mamaki mutanan palon suka bini da shi, Ga mamakin da ya kasa ɓoyuwa akan fuskokin ko wannen su, Ba mamakin komai suke yi ba illa irin kallon da suka ga Asaf na yiwa Siyama,ga shi kuma sai da ya ce mata tabi su Sa'ade sannan ta bi su. Abun ya ba su mamaki matuƙa, Juyowa shi ma Asaf ya yi ya so ma jan akwatinsa da zummar barin palon sai mahaifiyarsa ta yi Magana "Dawo Asaf magana za mu yi"Ya ji mahaifirsa ta yi magana, Ba shiri ya dakatar da tafiyan da yake yi ya dawo ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da ke cikin palon. Yana jira Mahaifiyarsa ya yi mai tambaya,dan ya san tambayar da za ta mai bai wuce na su Siyama ba. "Su waye way'ennan ?Kuma mai alakar ka da wannan yarinyar da take neman izininka kafin ta bi wannan matar da suka zo tare?". Irjinsa ne ya buga da karfi ya dage ya buɗe baki ya ce "Matata ce" " Meee?" Mutanan palon ɗuk suka haɗa baki wajan faɗi. In ka tire Alhaji da ke zaune akan kekensa yana saƙin murmushi da alama maganar da Asaf ya yi ba karamin dad'i ya yi masa ba. "Mom kalli Dada yana murmushi Mu'azzam ya faɗi ". Ɗuk kallon Alhaji suka yi suka ga gaskiya ne murmushin yake yi Ita ma Hajiya Rukayya bata san_ san da ita ma ta saki murmushi ba.dan rabon da daga Alhaji ya yi murmushi an ɗaɗe dan tun kafin ya kwanta ciwo. Ba karamin farin ciki Hajiya Rukayya ta yi ba. Asaf ma ɗagowa ya yi yana sakin murmushi da bai san yana yi ba, A zuciyarsa kuwa son Siyama ne ya ji yana kara rasa mai jiki da jijiya dan ya tabbata shigowar ta rayuwarsu alheri ne,tun da ko kwana ɗaya ba ta yi a cikin gidinsu ba amma ya fara ganin canji. Ha ka ma bangaren Hajiya Rukayya dan ita ma kallo ɗaya ta yi wa yarinyar ta ji ta kwanta mata a rai, Matsowa Hajiya Rukayya ta yi kusa da Mijinta ta durkusa a gabansa ta fara magana "Alhaji ya na ga da Asaf ya ce wancan yarinyar matarsa ce ka yi murmushi ?". Abun mamaki sai ya kara sakin wani murmushin wanda yafi na ɗazu yana geda kai sannan ya shiga ƙ'okarin daga hanunsa amma ya ka sa ganin abunda yake son yi ne ya sa Hajiya Rukayya taimaka masa daga hannun good 👍ya yi da babban yatsun hannunsa kana ya ci gaba da sakin murmushi. "Alhamdulillah tun da ka amince da maganar auren mu ma mun amince ", "Amma gaskiya Asaf sai ka gaya min yaushe ku ka haɗu har ku ka fara soyayya kaje ka aure ta ba tare da kowa ya sa ni ba ?". Ɗan busar da iska Asaf ya yi daga cikin bakinsa kafin ya buɗe baki ya fara magana kamar haka "Wallahi Mom jiya ne da muka yi tafiya ko isowa in da zamu je ma ba mu yi ba motar mu ta lalace a wani Ƙauye...." Kwashe komai ya yi ya gaya mu su daga haɗuwar su da Malam Iliyasu har da taimak'on Siyama da ya yi a lokacin da take son faɗuwan har da irin maganganun da 'ƴan Ƙauyen suka dinga yi,da kuma wanda Baba Siyama ya gaya mai,har da zuwan su wajan Malam Shuaibu da kuma irin wahalan da ya sha kafin ya rufe Aljanar Mazwara cikin kwalba. Duk sai da ya gaya musu ba bu abunda ya boye mu su. Bayan ya gama yi mu su ba ya nin komai ne ya ɗago ya dubi mahaifiyarsa ya ce "Mom kin ji dalilin da ya sa aka d'aura auren ba tare da an faɗa muku ba ke nan ", "Ba dan komai ya sa na bari aka d'aura wannan auren jiya ba.sai dan irin son ganin na yi auren da kuke yi ", Da a ce jiyan nan ba'a d'aura wannan auren ba. da tuni aljanar nan ta aure ni,kuma in ta aure ni _ni da aure har abadan ha ka Malam Shuaibu ya ce min ". Ajiyar zuciya ɗuk mutan palon suka s'auke Hajiya ce ta yi magana kamar haka"Gaskiya abunda ka yi shi ne daidai,da a ce ba ka yi ha kan ba. da ba zan taɓa yafe maka ba Asaf ". Lumsh ido Asaf ya yi ya buɗe ya dora su akan ƴaƴansa kuda ɓiyu Su ma kai suka geɗa alamar sun gamsu sosai da maganarsa. Kallon yayan mahaifinsa ma ya yi wa toh goggonsa ke nan,ita ma geɗa masa kai ta yi tana murmushi sannan ta ce "yarona abunda ka yi.ya yi daidai ". Miƙewa ya yi ya je kusa da Auntynsa Zahra matar yayansa Mu'azzam ya zauna kusa da ita kana ya ce " Mom karama ke fa ?". Murmushi ta sakar masa sannan ta ɗora hannunta samar kansa cewa "Haba Boy ai ni ko kowa bai amince ba ni zan amince saboda nafi kowa son ganin matarka kuma Alhamdulillah! na gani kuma na ji dad'i ɗuk da ba haka na so auren ya kasan ce ba amma ba bu komai tun da lafiya aka d'aura an kuma
Table of Contents