Chapter 20
Chapter 20
cewa "Komai mu na da shi Baba ba sai ka siyo mata komai ba" Baba ya buɗe baki zai yi magana Mus'ab ya karbi zancen da cewa "Da gaske kwai komai Baba karka samu damuwa". "Shi ke nan Allah ya yi muku albarka ya kuma baku zaman lafiya" Suka amsa da "Ameen" Har baƙin mota Malam Iliyasu ya raka su, Muta nan Ƙauye ma ba'a barsu a baya ba,dan kuwa suma sun zo su ba wa idanun su abinci. Rungume mahaifina na yi ina kuka. Shafa kaina Baba ya yi cikin sanyin murya ya ce"Haba Siyama ba fa rabuwa muka yi ba.zan dinga zuwa ina kawo miki ziyara kema in an kwana ɓiyu za ki kawo min ziyara ". Da haka dai Baba ya samu ya rarrashe ni na haƙura, Bayan motar da Mus'ab ya buɗe mun ne na shiga ya rufe kuma dama ita goggo ta riga da ta shiga tun tuni,saboda goggo akwai ta da son mota Kamar me. Tada motar Mus'ab ya yi suka ɗagowa Malam hannu ya ja suka bar Ƙauyen. Karfe goma na safe suka isa kofar gidan su Asaf, Home Mus'ab ya yi mai gadi ya wangele mu su gate ya cilla hancin motar cikin gidan. Kallon kallo muka shiga yi, ni da goggo,har aka yi parking, Shanye mamakin na nayi na fito daga cikin motar Ita ma goggo fitowa ta yi tana zazzare ido. Muje suka ji Asaf ya faɗa Soma tafiya suka fara yi har suka karasa bakin kofar, Danna kararawar ya yi ba bu jimawa aka zo aka buɗe kofar suka yi ido huɗu da....... *Fulanin of Jajirtattu ce ✍️* Comment's and share fisabilillah 👏
Table of Contents