Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

Mutum Ko Aljan Book One Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

mu je Mom ". Asaf ya faɗa sannan suka gyera suka tafi. Suna zuwa ya sa key ya bude kofar ɗakin,ma kunnin ya taba ya kunna fitilar ɗakin sai haske ya gauraye ko ina. Ido suka zaro waje gaba ɗayan su a lokacin da idanun su ya yi tozari akan...... In na kara one page nagama free page 😉🥰 Duk wacca ta shirya biya ga number din da zai yi min magana. 07049322735 .wannan ita ce number,sai a yi min magana a WhatsApp. Sai na jiku masoyan Asaf da Siyama 🥰 har ma da Mazwara duka 😆 dan na tabbata ita ma tana da masoya 😂😂💃 *Fulanin of Jajirtattu ce ✍️* Comment's and share fisabilillah 👏 [30/09, 23:04] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹💫 Story and Written ✍️ By: Sakeena Isma'il Cameroon (Mom Muwadda) ________________________________________________ Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ ________________________________________________ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ ________________________________________________ *Diamond 💎Star 🌟 Ladies* 🧝‍♀️ *(We stand together)* 🤝🤝🤝 Paid Book ₦500 Karshen free page 1️⃣5️⃣ Kamar yanda na sanar da ku cewa daga wannan page ɗin na kammala free page,dan haka ɗuk wacca ta shiya yin palmpay kofar a buɗe take,ga account number ɗina nan 8068569407. Sai a tura shaidar biya ta wannan number 07049322735.sai na ji ku masoyana masoyan littafin Mutun ko Aljana 😍bari muga irin son da kuke yi wa Asaf da Siyama shin mai karfi ne. ko kuwa?😂 Bismillahi rahmani rahim Ido suka zaro waje gaba ɗayan su a lokacin da idanun su ya yi tozari akan kwalbar dake tarwatse a kasar tayel ɗin ɗakin. Cikin sauri suka karasa inda kwalbar ta fashe,har suna rige _rige Sugunnawa Mom ta yi ta kalli kwalbar da kyallen dake gefe,ta juya ta kalli Asaf da shi ma yake a durkushe,kana ta ce "Asaf wannan ba kwalbar da ka dawo da shi ɗazu da safe ba ne ?". Kyallen ya ɗauka ya kare mata kallo sosai kana ya juya cikin mamaki ya ce "Wallahi shi ne Mom ". Asaf ya faɗa yana kallon mahaifiyarsa. "Toh waye fasa shi?ko ba ka ajiye shi inda ya ce ba ne ?". "Wallahi Mom na ajiye ta inda ya dace, ban san ya aka yi ta faɗi ta fashe ba.sai dai in wani ne ya shigo ɗakin ya ɗauka ya fasa ". Asaf ya kare magana cikin sanyin murya. " Haba karka gaya min maganar ban za Asaf. wa zai shigo ɗakin nan ? Kafi kowa sanin cewa iya mu ƴan gidan kawai muke bude wannan ɗakin,bayan mu babu kowa,kuma ka san s'arai ma su aiki ba su da key ɗin ɗakin nan da sai mu ce su suka shigo ɗakin suka fasa " . "Haka ne Mom amma ni abun ba karamin mamaki ya ba ni ba gaskiya ". "Ni ba wannan ba.ta shi ka nuna min wajan daka ajiye ". Kai Asaf ya geɗa yana miƙe wa ya nufi wajan da ya ajiye kwalbar kafin ta fashe . Wajan ya nuna wa Mom d'insa ya ce "Mom nan na ajiye fa ". "Haba_ haba wannan wajan da ka ajiye ba dole ta faɗi ta fashe ba Asaf ?gaskiya koma wa kauye ya kamaka gobe ya zama dole ka koma gobe_ goben nan dan ba zai yu ba, ka zauna da ƴar muta ne a haka ba.dole sai ka koma ,dan kana ganin fitowar ta yau daga cikin kwalbar nan abunda ya jawo maka ka kusa kashe ƴar muta ne, Ni bari ma na duba abunda ya kawo ni na koma wajanta na yi sauri da gama na koma wajan Dadinku kar ya farka bai ganni ba ". Ta faɗi tana karasa inda take ajiye kayanta ma su mahimmanci , Buɗe wajan ta yi ta d'auko akwatin ta juya ta kalli Asaf ta ce "Mu je". Kai kawai ya geɗa masa suka fita ya kulle kofar suka bar wajan. Kafin su karasa part dinsa ne Mom ta kalli Asaf ta ce "Sai ka faɗa wa Goggo ta shirya ku tafi tare daga nan ka maida ita ". "Ta tafi ". Ya bata amsa "Ta tafi ina ?". Mom ita ma ta tambaye shi, "Na sa dreve ya maida ita dan ba zai yu na barta anan ba ". "Wai yanzu Asaf sai daka sa aka maida matan nan ?". "Toh ai Mom ita ta jawo da bata yi abunda za'a maida ita ba ai da yanzu tana nan ". "Gaskiya ba ka kyauta ba. ta ya ya ko kwana ɗaya mutun bata yi ba ka sa a maida ita ?ai ko mai ta yi bai kamata a maida ita yau_ yau ɗin nan ba ". "Dan Allah Mom ki yi hakuri ki zo mu karasa dare na yi ". Da haka suka karasa ba tare da kowa ya kara cewa komai ba. Ana zuwa Mom ta cewa Asaf ta jira su a palo ko kuma ya wuce ɗayan ɗakin in yana jin bacci ya kwanta,ya ce a'a zai jira ta a haka dai ya samu waje akan ɗaya daga cikin kujerun palon ya zauna,ita kuma ta karasa cikin ɗaki,domin yiwa Siyama ɗinki. Mom na shiga ya miƙe ya nufi ɗayan dakin domin yin wankan tsarkin da bai samu ya yi ba tun ɗazu,dan ya ma manta shaf da maganar wanka tun lokacin da ya ga Siyama a wannan yana yin Sai yanzu abun ya faɗo masa. Mom tana shiga ta tarar da Siyama kwance akan gado ,bacci har ta fara daukarta,ta ji shigowar mutun zumbur ta _tashi daga kwancen da take. " Sannu ƴata ". Mom ta faɗi tana karasa baƙin gadon ta zauna , "Yauwa sannu Hajiya ". Ni ma na faɗi cikin jin kunya, *Bayan awa ɗaya* Bayan Mom ta gama yi min dinki ne ta miƙe ta nufi inda Asaf yake ajiye magungunan sa ta buɗe ta duba min paracetamol da ibuprofen ta kawo min da ruwa na sha, Bayan na kammala sha ta karbi glass cup din ta ajiye sannan ta kalle ni ta ce "Yauwa ƴata Allah ya kara sauƙi ni zan tafi sai na dawo da safe mai kike so a faɗa miki ?". Cikin jin kunya na ce "A'a Hajiya ni bana son komai,bai kamata a matsayinki na babba na saki girgi ba,ni ce ma ya kama a ce na yi miki girki ba ke ba ". Ƴata ke nan ba ni ce zan yi ba wannan yarinyar da ta kai ku ɗakin bakin nan ne take yi,dan haka ki faɗi abunda kike so a dafa miki?". Shiru na yi kamar ba zan ce komai ba.tuna wa da na yi da wannan girkin da na gani wata ƴar burni ta dafa a cikin film din da na gani rannan ne ya sa na ɗago da sauri ina cewa "Yauwa Hajiya akwai wani abinci da na ga wata ƴar burni ta yi a TV rannan shi nake so a dafa min ". Dan murmusha wa Hajiya Rukayya ta yi kana ta matso kusa da ni ta ce"Toh ya sunan abincin ƴata?". Jin Mom ta tambaye ni sunan abincin ne ya sa jikina yin sanyi,dan kuwa ko za'a kashe ni ba zan

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20