Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Azizu Da Aziza Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

isa wurin hasken nan sai na sami wata makekiyar shimfid’a a wani muhimmin wuri, wanda aka bi duk aka bice da shimfid’u na alharini fari mai adon dinari, an kuma yi masa wani irin zanen fulawa na azurfa. An yi masa k’ubba da hauren giwa a samansa, ga kuma wani ginshik’i a wurin, ga fitilu an rarrataya, a tsakiyar k’ubbar, sa'annan kuma ga sham’a an kunna a cikin wani kasko na zinari. A k’arshen fitilun kuma an yi wad’ansu hotuna iri-iri a jikin wani abu mai kamar bangon littafi. A wurin kuma akwai akusa na abinci wadanda aka rufe su da mayani na hariri, akwai kuma wata babbar randa ta k’arfe wadda ba kome a cikinta sai giya mai darajar gaske, sa'annan kuma a gefen randar ga kofuna iri-iri an daje su da zinari. Kusa da wannan wurin kuma ga wani faifai babba na azurfa an rufe wani tire shi ma na azurfa da shi, sa'annan an kawo tumak’asa an d’ora a kai. Sa'ar da na ga wannan shiri, sai na yi karambani, na bud’e na ga babu kome a ciki sai ‘ya’yan itace cike fal masu zak’in da laushin gaske. Har wa yau kuma a kan wani d’an teburi mai k’yalli ga turare a cikin wadansu ‘yan kananan kwalabe an dasa, wurin ya bice da k’amshi wanda ke busowa a hankali kad’an-kad’an. Lokacin da na ga wannan k’asaitaccen shiri sai na d’imauta, na zama kamar dadai da duniya ban taba ganin inda aka shirya abin arzik’i kamar wannan ba. Na yi farin ciki matuk’a, duk bak’in cikin da na sha fama da shi ya gushe nan take. To amma duk wannan shiri a banza yake wurina, saboda ni dai buk’atata saduwa da wannan matar. To, bayan na k’are kallon duk abubuwan nan sai na duba ko’ina ban ga wani mahaluki ba a cikin gonar ba. Saurayi ya ci gaba da shaida wa Tajul Muluk labarinsa ya ce, na duba ko’ina ban ga wani bawa ba balle kuyanga, na hak’ura na nemi wuri mai ni'ima na zauna, ina jiran zuwan matar nan, har wajen sa’a guda, amma ba ta zo ba, na zauna shiru sai k’ura ido nake in ga b’ullowanta, amma ban ganta ba, yunwa kuwa ta addabe ni, hankalina ya tashi, tuni dai bak’in ciki ne ke hana ni jin yunwa, yanzu kuwa da hankalina ya kwanta, sai duk abin ya cakud’e saboda tsananin yunwa. K’amshin abincin nan yana bugu na kad’an-kad’an, na kasa hak’uri sai na matsa kusa da kwanukan abincin nan, na bude mayanin da ke kan wani kwanon, na sami wani faranti da ke ciki an saka gasassun kaji guda hud’u, an kuma zuba musu kayan k’amshi da na yaji, a d’ayan farantin kuma ga wani romon ‘yan shila, wani farantin kuma ga toye-toye iri-iri na alfarma. Na ji wani yawun kwad’ayi na zubo min, sai na sa hannu na yanki kad’an daga cikin wannan kayan tuya. Na ji wani irin dad’in mai gamsarwa, na hangi wani kayan tire a wani gefen can daban, na juya can na bud’a sai na sami wata waina narkakkiya ga nama a jere, sai na zaci ko ina gidan Aljanna ne, don na ga abincin kamar yana zuwa wurina da kansa ne, na hau da ci, shi ma na ci gwargwadon cikina, sa'annan kuma na nufi wurin ‘ya’yan itace, su ma na yanki kamar loma hud’u, na juyo ga kajin nan, su ma na d’an gutsura sai na ji cikina ya cika fam, na yi shakkar kada wani abu ya auku na rashin kunya, na je na nemi ruwa na wanke hannuna, sa'annan na koma wurin zamana. Na zauna kenan gyangyad’i ya soma d’iba ta, na d’ora kaina a kan wani matashi mai laushin gaske, ban san lokacin da barci ya kwashe ni ba, ban farka ba sai da na ji zafin rana na buguna. Yayin da na farka sai na gan ni a rigingine, sa'annan kuma ga gawayi da gishiri a kan ruwan cikina, na mike tsaye na karkad’e rigata na duba kudu da arewa ban ga kowa ba, sa'annan kuma nan wurin da na farka babu wata shimfid’a wadda na sani tun kafin barci ya kwashe ni. Na yi mamakin haka gaya, na d’imauta, raina ya b’aci ainun, hawaye suka zubo mini, raina ya yi bak’in k’irin. Na tashi na nufo gida, na sami ‘yar uwata tana dukan k’irjinta tana faman kuka. Da ta ji motsina sai ta rera wadansu baitoci kamar haka: Iska ta taso, ta bice furanni masu k’amshi, Ta motsa wa tsananin so ciwonsa. Haba iskar kudu zo mana nan wurimmu, Kowane yana bakin iyakar son sa To kuma lalle da iyakar rabonsa a wurinsa Kai, wannan ciwon so ina jin zafinsa Ina ma ina da iko na yi runguma tamkarsa Tamkar da ya rungumi kirjin abar sonsa. Idan dai har dan uwan nan nawa ya mutu, Ya Allah ka haramta min rayuwa bayansa Kada Allah ya jiyar da ni dadin duniya in ya mutu, Aaa’aha yanzu ne zuciyata ke zafin son sa Haka shi ma tasa take kunar son waccan mata, Amma fa ni ga wannan ba na ganin laifinsa. Sa'ar da ta waigo ta gan ni sai ta zabura cikin hanzari ta shafe hawayen da ke idonta, ta zo wurina ta shiga yi mini magana kamar yadda ta saba, ta ce mini. Allahu Akbar, d’an uwana har yanzu kana cikin ciwon son matar nan, ni kuma ina cikin ciwon son ka, mutane suna yi da ni cewar wai na cika rashin hankali tun da na dami kaina da son masoyin wata, amma ni duk wannan bai dame ni ba, na riga na yafe maka komai a kan wannan al’amari, ba na fatar Allah ya saka mini duka wani abin da ka yi mini." Bayan ta k’are wad’annan maganganu sai ta yi murmushi, ta zo ta tub’e mini rigata, ta shanya sai ta sunsuna rigar ba ta ji kome ba sai ta ce, "wallahi wannan rigar babu wani k’amshin saduwar masoyi da masoyiya." Sa'ar nan ta dawo wurina ta ce, na gaya mata abin da ya gudana tsakanina da waccan mata, ni kuma na kwashe duk abin da ya faru gare ni na gaya mata. Sa'ar nan da ta ji sai ta yi dariya ta ce, Allahu Akbar, wannan mata tana wahalar da kai dan uwana, babu shakka ina ji maka tsoro game da wannan mata. Gishirin nan da ka samu an zuba a jikinka wai tana nufin kai mai nauyin barci ne, saboda haka take son ka sa wa ranka gishiri tun da yake ka bayyana kai mai ciwon so ne, alhalin kuwa barci haramun ne ga dukan mai ciwon so, wai har ta ce maganar son da kake yi mata k’arya ne, saboda haka ta bayyana maka cewa ita ma k’arya take maka ba ta sonka, ta dai rud’e ka ne kawai. Lalle kuwa da son da take maka gaskiya ne da ta tashe ka daga barci. Ma'anar gawayi da ta d’ora a kan ruwan cikin ka kuwa, wai tana nufin Allah ya bakanta fuskarka tun da ka yi da'awar sonta bisa ga k’arya, har ta ce, wai kai yaro ne, ciwon so bai kamace ka ba tukuna, ta kuma k’ara da cewar ba abin da ya kamace ka sai cin

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16