Chapter 13
Chapter 13
wuri mafi daraja a wurinta. Wannan dare ba zan iya kwatanta shi da kowane dare ba game da farin ciki, kamar yadda wani mawak’i ke cewa: Dare daya tak ya fi dukkanin darare, Ni’ima da jin dadi a dukkan rayuwata Lokacin da na sha kofi na girma sassanya Na zam tare da yari da awarwaro b’arya ta Nan muka kwanta rungume da juna muka yi barci, yayin da gari ya waye na tashi zan tafo gida, sai matar nan ta kama ni ta ce, "tsaya na gaya maka wata magana." Saurayi ya ce da Tajul Muluk, yayin da na tashi zan tafo gida sai ta ce da ni in tsaya ta fada min wata magana ta wasiyya, sai na tsaya cif da k’afafuna, sa'annan sai ta kwance wani mayani ta fito da wannan k’yalle ta shimfid’a shi a gabana, na duba na ga wadannan surori na hoton barewa kamar yadda yake d’in nan, mamaki ya kama ni matuk’a, har na yi sha'awarsa, na karb’e shi daga wurinta. Muka yi alkawari da ni da ita, kowane dare zan tafi wurinta in same ta a cikin gonar nan da muka hadu tun farko. Na kama hanya na taho gida ina cike da farin ciki, don tsananin murna da farin ciki har na manta ban rera wak’ar nan da ‘yar uwata ta ce min na yi ba. Yayin da ta ba ni mayanin nan mai zanen bareyi ta ce min, “ka adana wannan da kyau, wata ‘yar uwata ce take yin su.” Na tambaye ta yaya sunanta? Ta ce min sunanta Nurul Huda. TALLA Zaku iya karanta wasu hikayoyinmu na daban a zaurenmu na sirri akan kudi 200 kacal zamu baku labarai da dama acikin kwanaki talatin akan 200 kawai' sannan kuna iya samun karashen HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN, DA HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI'.07 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO Nace mata yaya sunanta ita mai yin zanen tace'' nurul huda, Yayin da na shiga gida wurin ‘yar uwata sai na same ta a kwance, da ta ji zuwana sai ta taso hawaye na zuba a idonta ta zo wurina ta kama ni ta rungume a k’irjinta, ta tambaye ni ta ce, "shin ko ka yi mini abin da na gaya maka na game da baitin wak’ar nan da na ba ka na ce ka rera wa wannan mata idan ka sami biyan bukatarka game da ita a lokacin da za ku rabu ?" Na ce da ita, "ai kuwa na manta, babu kuma abin da ya sa sai rudewar da na yi game da surorin hotunan wannan barewa na jikin wannan kyallen." Na jefa mata k’yallen a gabanta, sai ta zabura, ba ta sami ikon yin hak’uri ba, hawaye suka rik’a zubowa daga idanunta, har ta yi wak’a tana cewa: Haba mai neman rabo saurara, Kada yawan runguma ya rud’e ka, Dakata dai ka k’ara hak’uri, Da sannu za ka cimma burinka Lokacin da ta gama wak’arta sai ta ce da ni, 'dan'uwana. Ina son ka ba ni wannan k’yalle. Ban yi wata wata ba sai na d’auka na ba ta. Ta karb’a ta shimfid’a ta ga abin da ke ciki. Sa'ar da lokacin komawata wurin waccan mata ya yi, sai ‘yar baffana ta ce da ni, "kada ka damu, je ka abin ka cikin kwanciyar hankali da jin dadi, amma idan za ku rabu ka wak’e mata baitin wak’ar nan wanda na gaya maka tun farko kada ka yarda ka mance shi." Na tashi na kama hanya bayan ta sake biya mini baitin wak’ar ina tafe kurum, na kamo hanyar gona har na iso gun gonar na shiga ciki na sami wurin zamana an shirya shi tsaf, a gefe daya kuma ga yarinya har ta riga ni zuwa, ta ma dad’e tana jira na, da gani na sai ta tashi ta kamo ni ta rungume ni sa'annan bayan ta numfasa sai ta zaunar da ni a kan cinyarta, bayan mun d’an huta kadan muka shiga cin abinci, ina zaune a kan cinyarta muka ci, muka sha, muka yi wasa, sa'annan muka biya buk’atarmu kamar yadda muka yi tun farko. Da zan tafi sai na wak’e mata baitin wakar nan na ‘yar uwata wanda ta koya mini ina cewa: Ya ku masoya na gama ku da Allah ga tambaya, Shin menene abin yi da maganin ciwon so? Da ta ji haka sai ga hawayen na zubowa daga idanunta. Lokacin da take kukan nan sai ta rera mini wannan baitin: Matuk’ar yana bukatar maganin ciwon so Ya zam mai hak’uri da boye so da dauriya A lokacin da take rera wak’ar na yi k’ok’arin haddacewa, na yi farin ciki da ganin bukatar ‘yar uwata ma ta biya, na cika mata burinta kamar yadda nata nema daga gare ni. Da na isa gida na tarar da ‘yar uwata tana kwance, a gefe d’aya kuma ga uwata zaune kusa da ita a daidai kanta tana kuka saboda ganin irin halin da yarinyar take ciki. Da shiga ta cikin dakin sai uwata ta yi mini tsawa ta ce, "amma kai dai baka da kirki!" Yaya za ka fita ka bar ‘yar uwarka kwance ba ta da lafiya sa'annan kuma bayan ka dawo ba za ka tambayi yadda ta k’ara ji ba?" Lokacin da ‘yar uwata ta ji fad’an da uwata take yi mini, sai ta d’aga kanta ta dube ni, ta ce, "ya Azizu, ko ka wak’e wa budurwarka baitin wak’ata ? " Sai na ce mata, “eh na wak’e mata shi.” Sa'ar da ta ji haka sai ta fashe da kuka ta sake wak’e min wad’annan baitoci: Hak’uri tuni ya kare babu abin yi, Firgitar zuciya da ciwo ya yi tsanani Sa'annan ta ce na fad’a mata abin da waccan matar ta fada bayan na rera mata baitin wak’arta. Na rera mata, da ta ji sai ta b’arke da kuka, ta yi kuka mai tsanani. Sa'an nan ta ce mini idan na je wurin budurwar nan tawa kamar yadda na saba in wak’e mata wannan baitin, na ce mata, “na ji na yarda.” Da safiya ta yi lokacin tafiya ya yi na fito gida, na kama hanya har cikin gonar da muke haduwa da wannan mata. Muka shiga sha’anin holewa da jin dadin juna fiye da yadda harshe zai bayyana. Yayin da na tashi zan tafi bayan wayewar gari sai na rera mata baitin wak’ar da ‘yar uwata ta sake ba ni . Yayin da matar nan ta ji wannan baitin wak’ar sai hawaye kuma suka zubo mata a k’irjinta. Ita ma sai ta wak’e wani baiti guda ta ce: Matuk’ar hak’uri da ciwon so ya gagara, Babu shakka dai mutuwa ce magani. Na sake haddace baitin wak’ar na kamo hanya sai gida, da shiga ta cikin gidan sai na sami yarinya ‘yar uwata tana kwance, ta yi kuka har ta some, ga kuma uwata a zaune kusa da kanta tana kallon halin da yarinya take ciki. Yayin da ta ji motsin shigowa ta sai ta bud’e idanunta ta ce da ni, "Azizu, yaya ka karanta mata wak’ata?” Na ce mata “eh ban manta ba na karanta mata, amma fa na ga ta fashe da kuka kuma ta ce na fada miki cewa, ‘Matuk’ar hak’uri da ciwon so ya gagara, babu shakka
Table of Contents