Chapter 7
Chapter 7
wurina, ta dauke ni, ta tuɓe mini riga, ta shafe mini fuska da hannun zaninta. Sa'annan ta tambaye ni yadda muka yi da waccan mata wadda na fito daga wurinta. Na kwashe duk abin da ya auku na gaya mata, sai ta ce, "nunin da ta yi maka na tafin hannu da kuma yatsu biyar, tana nufin wai bayan kwana biyar ka je can wajenta, nunin madubi da ta yi maka har ta fito da kanta ta taga ma'anarsa wai ka je ka zauna a rumfar marina za ka ga manzonta ta aiko shi wurinka." Yayin da na ji wannan fassarar ta ‘yar uwar nan tawa sai raina ya tafi, na kagauta matuƙar kagauta. Zuciyata ta dau zafin doki har na ce da ‘yar uwar nan tawa “don Allah ki gaya mini gaskiyar wannan fassara mana, shin ko kuwa kina yi mini ba'a ne. Lalle kam na hadu da wani Bayahude kan hanya a cikin lungun nan da nake bi zuwa gidan wannan mata” Sai na fashe da kuka don tausayin kaina, ‘yar uwan nan tawa ta ce da ni, "haba jinina, tashi ka ƙarfafa zuciyarka mana, ai ka san akwai wanda ciwon so ya auka masa ya yi kuwa haƙuri shekara da shekaru, yana daurewa zafin zuciyarsa ballantana kai mai jiyyar kwana bakwai kadai, a cikin wannan masiba, amma ga shi duk ka murd’e ka yanƙwane, sa'annan kuma duk ka dami kanka da al'amarin da yake galabaitarka. Ina a ce duhu ne kake suka ba gaskiya ba ?” Bayan ta gaya mini haka sai ta riƙa rarrashina tana ba ni magana, ta je ta kawo mini abinci, na yanki loma daya kawai ita ma na kasa hadiyewa, shi ke nan kuma sai ci da sha suka gagare ni. Na kaurace wa abinci, kamannina suka juya nan take, kyawuna ya dushe, ya jirkita gaba daya, saboda ni tun da nake ban taba fadawa jarrabar so ba sai a wannan lokaci. ‘yar uwata ta rika yi mini tadin maza ma'abuta ciwon so saboda hankalina ya kwanta, a cikin wannan lokacin sai barci yakan rika diba ta kadan, amma idan na farka sai na gan ta tana zaune zugum ta kasa yin barci, saboda ni, sai kuka kawai take rabsawa, hawaye na zuba daga idonta, haka dai muka dinga fama da wannan al'amari har kwana biyar suka cika. A daidai wannan lokaci ne sai ‘yar uwar nan tawa ta tashi ta d’umama mini ruwa ta dauke ni ta kai bayan daki ta yi mini wanka, ta kuma dauko mini wadansu tufafina masu kyawon gaske, ta bice su da turare, sa'annan ta sanya mini, ta ce tashi ka tafi wurin tauraruwarka, Allah ya biya maka bukatarka, Allah ya sa ka dace da abin nufinka game da wannan mace wadda kake so. Lokacin da ta kare mini shiri kaf sai na tashi na kama hanya har na kai wurin lungun nan iska na d’ibana saboda rashin ƙarfi. Ranar Asabar ce kuwa, sai na samu rumfar marini amma a kulle, na zauna a wurin har aka yi kiran sallar La'asar. Ina nan zaune wurin har dai rana ta tasar wa faduwa, kai har dai ta fadi aka kira sallar magriba, isha’i ta kama aka yi salla duk dai ina nan zaune har dare ya kama sosai, ni dai ban d’aga ba, amma ban ga wannan matar ba, ban kuma ji motsinta ba, tsoro ya kama ni. Ina zaune ni kadai sai na mike tsaye na tashi, sai ka ce wanda ya sha giya, ina tafe ina tangadi cikina ya murd’e saboda zafin bak’in ciki, haka dai nake tafiya ina fad’uwa kan hanya a cikintsakar dare har na iso gida. Sa'ar da na iso gida sai na shiga na sami ‘yar uwan nan tawa Azizatu ta rike wani turke wanda aka kafa a jikin katanga ta aza dayan hannunta a kirjinta tana rafsa kuka, tana ruri, sa'an nan kuma tana rera wak’a a cikin murya mai ban tausayi: Shin mene ne bakin cikin Balarabiya Wadda jama'arta suka yi mata nisa Wadda kuma ta ke kuka saboda nisan Hijaz da Randuh. Idan na hango ayarin matafiya sai ciwon sona ya karu da wutar gararsa, Ga kuwa hawaye na zuba daga idanuna. Watau don girman sonsa a guna Shi har ganina yake na yi masa laifi babba Wai don me nake sonsa kwarai haka. Bak’in cikin balarabiya jama’arta sun mata nisa, Ta kasa bambamce Hijaz da Farisa wanne ke da nisa, Idan na hango ayarin tafiya sai ciwon ya k’aru rashinsa Ga hawaye na ta zubar min idanuna saboda k’aunarsa Ga shi ma ganina na tafiya saboda haushin rashinsa To wai shin ina dalilin da ya sa nake a haka son sa? Yayin da ta gama wak’arta sai ta juyo ta dube ni, ta ga ina kuka, sai ta shafe nata hawayen, ta zo ta shafe mini nawa hawayen da hannun zanenta, ta yi mini wani dogon murmushi ta ce da ni, "ya dan'uwana," Allah ya jiyar da kai dad’in abin da ya ba ka. Shin me ya hana ka kwana a wurin wadda kake s ? Me ya hana ku kwana tare, me ya hana ka biyan bukatarka da ita?" Yayin da na ji haka sai na sa kafa na dake ta, na sake zuba mata tafi, na mangare a kirji, ta fadi daga jikin katanga, goshinta ya je ya daki wani turken da ke jikin katangar, ta datse goshinta, jini ya yi ta zuba. saurayi Azizu ya cigaba da shaida wa Tajul Muluk labarinsa, ya ce sa'ar da na sa kafa na doke kirjinta ta fad’i a gindin katanga har ta buge goshinta a kan turke jini ya soma zuba sai hankalina ya tashi matuk’a, amma ita sai ta yi shiru ba ta ce kome ba, sai ta yagi haɓar zanenta ta daure wurin mikin, ta shafe jinin da ya zuba ga jikinta, ta gyara jikinta, ta goge fuskarta sarai, ta gyara shimfid’ar da take barci. Ta sake shirya wuri ya zama kamar dad’ai babu abin da ya faru a wurin, sa'annan ta rarrafo ta zo wurina tana murmushi, ta shiga ba ni magana, tana rarrashina, tana kuma shafa ta, ta ce, "haba d’an uwana, ai wallahi ba izgili ne na yi maka ba, kuma ba gatse ne na yi maka ba, ko kusa kada ka zaci haka. Ina son ka huce, ka ba ni labarin abin da ya gudana tsakaninka da waccan masoyiyar taka." Nan take na kwashe duk abin da ya gudana na gaya mata, sa'annan rashin hak’uri ya same ni na fashe da kuka. ‘yar uwan nan tawa ta ce, na yi farin ciki da yi maka albishir cewan bukatarka dai za ta biya a tare da wannan mata, saboda wannan shi ne alamar yarda a tsakaninku, watau dalilin da ya sa ba ta aiko maka da sako ba, tana auna ka ne, tana son ta san irin tsawon hak’urinka, har kuma ta gane matsayin son ka da ita. Yanzu na shawarce ka da ka sake komawa gobe a can wurin haduwarku na farko, saboda ka ga abin da za ta sake nuna maka. Duk wannan magana da take ba ni sai hushi ke kara hawa mini, raina ya ɓaci ƙwarai. Ta tashi ta kawo mini abinci, na sa ƙafa na haure abincin,
Table of Contents