Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Azizu Da Aziza Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

suka kama da yawa daga namun dajin wasu kuma suka gudu. Tajul Muluk ya sauka kusa da inda ruwa ke gangarowa ya sa aka kawo namun daji da ya kama aka rarraba bayan ya ware na mahaifinsa ya bayar a kai masa gida. Ya kwanta a nan suka yi barci har gari ya waye sai ga wasu fatake suna tafe da bakaken bayi da hadimai farare suka sauka a wannan dausayi domin su huta kafin su yi gaba. Tajul Muluk na hangen su ya ce da wani yaronsa, "je ka samo min labarinsu da musabbabin tsayawar su a wannan waje." Dan aike ya garzaya ya same su ya ce, "ku fada min ba tare da bata lokaci ba ko su waye ku." Suka amsa cewa, "mu fatake ne, mun tsaya a nan ne domin mun huta, saboda zango na gaba na da nisa kwarai. Kuma mun san Sarki Sulaiman Shahu da dansa Tajul Muluk adalai ne. Mun san cewa duk wanda ya zauna a kasarsu to yana cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da tsoron wani abu ba. Sannan muna dauke da kyauta ta musamman ga yarima." Dan aike ya juya ya fada wa yarima duk abin da fatake suka fada. Dan sarki ya ce, "idan sun kawo kyauta gare ni to kuwa ba zan bar nan sai na ga wacewace irin kyauta ce." Ya hau dokinsa ya tafi tare da hadimansa da bayinsa zuwa ga wadannan fatake. Gaba daya suka mike domin girmama shi, suka yi masa addu'a da fatar alheri sannan suka nuna masa wata hema wanda aka yi mata ado da hadalashi zananniya da lu'ulu'u da jauhari. Aka shimfid’a masa shimfid’ar sarauta da labule na alharini da matashin kai zananne na zubarjadi da Tajul Muluk ya zauna hadimansa suka kewaye shi sannan ya sa aka fataken su fito da abin da suka yi nufin kai masa kyautar. Bayan sun ba shi kyautar kuma ya ce su bude hajar su domin ya sayi wani abu. Suka bude hajar tasu ya zabi abin da yake bukata ya biya kudinsu. Ya duba zuwa ga ayarin ya yi musu bankwana, sannan ya hau dokinsa zai tafi, sai idanunsa suka fada kan wani kyakkyawan saurayi yana sanye da kyawawan tufafi, goshinsa yana kyalkyali kamar hasken wata. Sai dai wannan kyakkyawar fuskar tasa ta gurbata, duk ta yi fari - fari, ga gurbin hawaye da ke surnanowa daga idanunsa saboda daga dukkan alamu ya rabu da wani abu da yake matuk’ar kauna ne. Tajul Muluki ya matsa kusa da shi ya ji yana kuka yana rera wannan wak’ar: Zuciyata ta yi bankwana da ita, Ranar rabuwa na zamto ni daya Na zamo babu aiki babu hali, Babu aboki sannan babu zuciya Ya abokina ka tsaya nan tare da ni Mu yi bankwana ko da sau daya Yayin da ya gama wannan wak’ar ya fashe da kuka ya fadi sumamme. Tajul Muluk ya dube shi cikin mamaki. Can jimawa sai ya farfado ya shaki iska sannan ya sake rera wannan wak’ar: Ku rike rumfarku daga rudadde, Madimauci da hanya ta bace masa Kaura ta jefe shi ya shiga uku Bai zamo mai tsira ba daga nahisa Kun ga idon bakunci ya gaji Da ganin kewa ba mai iya masa Ku bar yi wa kurciya dariya idan- Tana zancenta a al'amarinsa Kun ga bacin raina ya zamto, Mai dimauta hankali mai ji nasa Ya yi kuka mai yawa har sai da ya shide, Tajul Muluk da ya ga haka sai ya dimauta da al'amarinsa. Ya tafi gare shi. Da yaron ya ga dan sarki a kan sa sai ya zabura ya mike tsaye ya sumbaci hannunsa cikin girmamawa. Tajul Muluki ya ce, "me ya sa baka kawo mana kayanka mun yi maka ciniki ba?" Saurayi ya ce, "ya shugabana kayan babu wani abin ku-zo-ku gani da zai kayatar da kai ka saya." Dan sarki ya ce, "babu makawa ka kawo abin da ke tafe da kai na saya, kuma ka ba ni labarinka. Ni na ga alamar kana cikin bak’in ciki ga shi kana yawan kuka. Idan wani ne ya zalunce ka mu kamo shi mu wulkanta shi. Idan bashi ne ya karya ka, ka fada mu biya maka. Ni kam tun lokacin da na gan ka zuciyata ta konu da halin da kake ciki." Tajul Muluk ya yi umarnin a kafa gado, aka kafa masa gado na li'aji mai alfarma, mai kafafun dinari, labulensa na alharini, aka shimfid’a shimfidun alharini, Tajul Muluk ya zauna. Ya umarci saurayi da ya zauna, shi ma ya zauna a kasa. Tajul Muluk ya ce ya dawo sama ya zauna kusa da shi. Sannan ya ce masa, "kawo mana kayanka." Saurayi ya ce, "ya shugabana kada ambaci haka gare ni, kayana ba su da wani amfani gare ka." Tajul Muluk ya ce, "ya zama wajibi ka fada mini abin da nake son ji!" Ya umarci bayinsa su dauko masa kayan saurayin gabansa duk da ganin hawaye na cigaba da zubo masa bai kula ba. Saurayi ya cigaba da kuka yana ajiyar zuciya yana shessheka. Ya yi kaki ya gyara muryarsa sannan ya rera wannan wak’a: Yaushe zuciyata za ta warke, Daga azabtarwa daga gun ka? Tauraron nan na surayya, Ya fi kusaci daga gun ka Wutar bege ta kone min, Zuciyata domin na rasa ka A sannu zai zamanto mun, Yi tsammanin samu daga gun ka Babu nisan da zai zamo kusa Matuk’ar na dai rasa ka Zuciyata babu sauki babu- Jin kai domin babu ranka Ba ni da hujjar mance ka, Don haka jiddan na tuna ka. Tajul Muluk ya yi al'ajibin wannan wak’a gayar al'ajabi, bai san dalilin wannan abu ba. Ya sa saurayi ya bude kayan ya dauko wata takarda da wani kyalle. Ya ce da shi, "wannan tsumman fa da takardar nan?" Ya ce ya shugabana ba ka da bukatar wannan tsumma." Dan sarki ya ce, ka nuna min dai abin da ke ciki." Saurayi ya ce, "ya shugabana, da ma saboda ita na ki yarda a kawo maka kayana."03 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKE SO dan sarki ya ce, ka nuna min dai abin da ke ciki." Saurayi ya ce, "ya shugabana, da ma saboda ita na ki yarda a kawo maka kayana." Dan sarki ya fusata ya ce, na fada maka babu makawa sai na ga abin da ke ciki.” Saurayi ya hada kai da gwiwa ya soma kuka yana ajiyar zuciya, can jimawa sai ya nisa ya wake wadannan baitoci: Kada ku zarge ni kansa domin, Zargi yana kona zuciya matuk’a Na fada muku gaskiya tuntuni, Amma kun ki saurarona hakika Akwai kaunata a cikin tsumma, Ya zamto Zaharau cikin Falukka An yi nufin mu zamto tare sai naki, Ta zamto tana kare ni da duk halaka Hawayena suna zuba a idanuna, Na rasa mai shafe min hakika Ranar rabuwarmu na kasa barci Domin kunar zuciya ba wandaka Na kore rabona da hannayena, Bak’in ciki ya same ni ga halaka Na rasa mai shayar da ni ruwa, Na sha a kasko na warke hakika Yayin da ya gama wak’ar Tajul Muluk ya ce masa, “tun d’azu na lura da halinka, idan ka kalli wannan kyalle sai ka fashe da kuka. Fada min dalilinka game da haka.” Ya yin

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16