Chapter 11
Chapter 11
ce ko kusa kada ka saka kanka cikin masu iya rik’on al'amurran so. K’wallon dabino kuwa, tana nuna maka cewar da kai mai ciwon so ne, wanda har zuciyarsa ta k’una da so, da ba ka sake har ka ji dad’in barci ba, ka sani jin dad’in so kamar d’an dabino yake, tubali kuma abin da take nufi da shi, wai ta ce da kai, zuciyar mai so a warware take ba kome sai son kurum, ta sa a gaba, don haka ta ce ka dai hak’ura da rabuwar da za ku yi, har ma ta shawarce ka da ka tanadi irin hak’urin nan na Annabi Ayyuba, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Saurayi ya ce, sa'ar da na ji fassarar wadannan tarkacen da aka d’ora mini a ruwan cikina, sai zuciya ta sake b’aci, na auna a zuciyata cewar Allah ne ya k’addara mini yin wannan barci tare kuma da rashin rabona a wurin wannan mata. Sa'annan na ce da ‘yar uwata domin darajar rayuwata a wurinki ina son ki nuna mini dabarar yadda zan sadu da wannan mata. Na fashe da kuka ta ce, "ya Azizu d’an uwana. hakika raina a b’ace yake har ba zan iya yin wani tunani ba a halin yanzu amma na shawarce ka in dare yayi ka tafi wurin, kada ka yarda ka yi barci, za ka sami abin da kake so, wannan ita ce shawarar da nake son ka d’auka, wassalam." Sa'ar da na ji wannan shawara tata sai na ce in Allah ya so ba zan yarda na sake ba har in yi barci. ‘Yar uwan nan tawa ta tashi ta je ta kawo mini abinci ta ce na ci har na k’oshi yadda ba zan yi sha'awar cin wani abinci ba, na zauna ina jiran lokacin tafiya ta yi. Lokacin da dare ya yi ‘yar uwata ta tashi ta d’auko mini wad’ansu tufafina masu kyau, ta saka mini, sa'annan ta yi mini magiyar cewa idan na je can duk lokacin da zan dawo na rera baitin wak’ar nan nata na farko, ta sake jan kunnena a kan kada in yarda in yi barci a can na jira har lokacin zuwan matar nan ya yi yadda za ta zo ta same ni a farke. Bayan na kammala dukkan shirina sai na kamo hanya da hanzari har na iso wurin da gonar nan take, na shiga ciki na sami shirin wurin kamar yadda na saba samunsa tun farko, na sami wurin zama na hard’e, na yi shiru domin kwarjinina a matsayin jarumi. Ina cewa lalle ne yau na yi nasara kan wannan mata. Na zauna nan ni kadai ina koda kaina a cikin iska har dare ya yi tsari sai na girgiza kaina, na bude idanuna don kada barci ya kama ni..06 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO Saurayi yaci gaba da fada wa Tajul Muluk labarinsa, ya ce, sai na sami wurin zama na zauna, ina cika, ina batsewa, na shaki iska har kaina ya kumbura ina hura hanci kamar gwauron bajimi. Duk lokacin da na ji barci zai kama ni sai na girgiza kaina, ina nan cikin wannan hali na jaruntaka sai k’anshin abinci iska ta soma bugo shi a wajena, yunwa kuma ta motso mini gaba d’aya, na tuna cewar "sa raina ga abinci shi ke kawo jin yunwa." Saboda haka sai na daure, na kawar da kaina a wani gefe daban. Amma duk da haka na kasa hak’uri, na nufi wajen da abincin nan yake, na je na tsuguna a kan abinci, na yi zugum da kaina, na tank’ware gefe guda ina shawara da zuciyata, yunwa kuma sai matsa sallama take, da dai na ga yunwar ta daina sallama har duka na take, na kuwa ga alamar ba za ta bar ni ba, za ta yi min dukan falan d’aya, da na ga haka sai na cire mayanin da ke yafe a kwanon abinci, sa'annan na bud’e murfin kwanon da abinci ke ciki, na yanki loma guda na ci, na kuma ciri yankan nama d’aya na saka baki, sa'annan na juya a wajen da giya take da nufin zan wanke idona da moda guda. Na sha na farko, sai na ji marmarin na kara, na sake cika mak’ogwarona da moda ta biyu, na k’ara ta uku har dai zuwa na ashirin na ji ta kama mini daidai cikina, sai na zarce na shiga aikina daidai, na sha har na soma tumbatsa, sa'annan na juya kan mai sanyi ita ma na dibi wadansu ‘yan kananan kofofi sai iska ta bugo ni na tuntsure, daga kan kujera kamar matacce, daga nan kuma sai barci ya d’ebi abinsa, na yi ta sharar barci, ban farka ba sai bayan da rana ta fito har ta karya zuwa muhtarin la'asar. Yayin da na farka sai na ga ashe har an fitar da ni daga cikin gonar ne, an jefar da ni can gefen hanya ga ungulai kewaye da ni suna jiran tsammani. Bayan da na farka na ga wurin da nake na duba kusa gare ni, na ga wata zandamemiyar wuka mai kaifin gaske ta fad’o daga ruwan cikina, a can gefen kuma ga tanderu na bakin karfe. Yayin da na ga haka fa sai hankalina ya tashi matuk’a, na rasa inda zan saka kaina, na d’ebi wadannan munanan abubuwa na kamo hanya zuwa gida. Da na zo gida sai na sami ‘yar uwata tana cike da kewar ganina. Da shiga ta cikin gidan sai na yanke jiki na fadi k’asa ina birgima, na watsar da wuk’a da tanderu a gabanta, nan take na suma, hankalin ‘yar uwan nan tawa ya yi mummunan tashi, ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru gare ni, sa'ar da na farfad’o sai na gaya mata duk abin da ya faru, na shaida mata cewan na kasa samun biyan buk’atata game da wannan mata. Da taji haka ranta ya b’aci ainun, ta ce min, "babu shakka, ni kam na gaji da yi maka nasiha game da al'amarin matar nan!" Saurayi ya ce sai na ce da ita, '"ya yar uwata, ina son ki gaya mini, ma'anar wuk’ar nan da tanderu." Sai ta ce da ni, ma'anar tanderun nan na bak’in k’arfe da ta dora kan ruwan cikinka, watau wai ta rantse da Ubangijin talikai Allah Madaukakin Sarki, da kuma idon nan nata na dama idan har ka yarda ka sake komawa wurinta, sa'annan ka yi barci, to, lalle kuwa za ta yanka ka, da wannan wuk’ar, kamar yadda ake yanka rago, ta yi alk’awarin za ta yi maka mummunan kisa. Wannan shi ne fassarar abin da take nufi game da kai, saboda haka, dan uwana ka sani dai ni kam ina ji maka tsoro game da sharrin makircin wannan mata, babu shakka a halin yanzu, zuciyata a b’ace take game da kai, don haka ina jin ba zan iya gaya maka wata magana ba, amma idan ka ji ka amince da cewar idan ka koma wurin matar nan ba za ka yi barci ba, to, shi kenan sai ka shirya ka koma. Ni dai na rok’e ka don Allah ka fita hanyar matar nan, idan kuwa ba ka fita hanyarta ba, to, kome ya faru gare ka ba ka da kaico, idan har
Table of Contents