Chapter 10
Chapter 10
abinci da shan abin sha da barci. Da ‘yar uwar nan tawa ta gama fassara mini ma'anar wadannan abubuwa sai ta ce mini, '"dan uwana, na roki Allah ya kiyayeka ya kub’utar da kai daga sharrin wannan mata." Saurayi ya ce yayin da na ji wannan jawabi na ‘yar uwan nan tawa sai na bugi k’irjina na ce “wallahi wannan jawabi naki gaskiya ne, hak’ik’a ni kam na yi barci, lalle kuwa masu fama da ciwon so ba sa barci, babu shakka na cuci kaina yayin da na ci abincin nan, sai na tambayi ‘yar uwata na ce, to yanzu mene ne abin yi gare ni, domin duk lokacin da bak’in ciki ya taso mini sai na fashe da kuka. Na ce da i “don Allah ki gaya mini yadda zan yi na sami saduwa da wannan mata, na rok’e ki don Allah ki ji tausayina, ki taimake ni domin kuwa in ban sami saduwa da wannan mata ba, mutuwa zan yi. saurayi ya ci gaba da ba da labarinsa ga Tajul Muluk dan Sarki Sulaiman a sa'ar da suka sadu a cikin wani lambu. Ya ce yarinya ‘yar uwata ta ci gaba da gargad’ina a kan wannan mata da nake mutuwar so, ta ce “amma tun da yake har yanzu hankalinka na kan ta zan yi matuk’ar k’ok’arina na ci gaba da taimakonka har zuwa matuk’ar iyawata.” Sa'annan ta ce da ni, “ka tafi can wurin nan da kuke saduwa ka zauna, idan ka je wurin kada ka yarda ka ci wani abinci, kada kuma ka yi barci, yawan ci shi ke kawo barci saboda haka na shawarce ka duk yadda yunwa ta matsa maka ka daure, yunwa ba ta kisa sai dai wahalarwa, wahala kuwa tana tare da wanda Allah ya d’ora wa masifar son wani, amma ka ga bak’in ciki babu shakka yana kashe mutum. Ita wannan mata za ta ci gaba da jarraba ka har zuwa wani lokaci. Idan ka je wannan wurin ka tabbata za ta zo amma ba za ta zo ba sai wajen asubahi. Na roki Allah ya kiyaye ka daga sharrin wannan mata.” Saurayi ya ce yayin da na ji haka sai na yi farin ciki, na zauna ina jiran dare ya yi don na je can, sa'annan da daren ya yi na kama hanya zan tafo sai ‘yar uwan nan tawa ta ce idan har kun sadu ka rera mata baitin wak’ar nan tawa a lokacin da za ku rabu, sai na ce da ita, "To." Yayin da na fito na kamo hanya, ina tafiya har na iso wurin, na sami wurin an shirya shimfid’u kamar yadda na same su da farko, ga abubuwan ci da na sha iri daban - daban, ga kuma kayan ci na marmari daga ‘ya’yan itace zuwa kayan alfarma na toye - toye babu iyaka, sa'annan ga turare iri - iri masu k’anshin gaske, su ma an shirya su gwanin ban sha'awa. Da na k’are kallon wadannan abubuwa sai na koma wurin zama na zauna, k’anshin abincin nan yana buguna, zuciyata ta afu matuk’ar game da son in ci abincin nan amma sai na daure na k’i ma kula shi. Ni dai wallahi ban san lokacin da na rud’e ba, na kasa hak’uri, sai na zagayo na zo gun abincin nan, na bud’e mayanin da ke rufe a kai, na ga naman kaji soyayye da romo mai kyau, akwai abubuwan ci iri hudu kowane kuwa kan gaba ne wajen dad’i. Sai na kasa yin kome, na bude na yanki loma guda, guda a cikin kowane tsibin, sa'annan na koma wajen kayan zak’i su ma na ci gwargwado, na kuma dauki yankan nama guda na saka a bakina, na juya wajen kayan sha na bude na sha na cika cikina tab. Sa'annan na ce kome ta fanjama, fanjam,ni dai ba zan yarda na sake da cikina ba, saboda haka na ga ya fi kyau in kintsa. Kafin a jima sai na ji idanuna sun soma lumshewa, na jawo matashi na tada kaina, na auna cewan zan dan kishingid’a ne na huta har lokacin da za ta zo ta same ni, na sani dai barci ne ba ta son ta same ni ina yi, amma ko ta sami na ci abinci ba za ta damu ba. ‘Dora kaina ke da wuya a kan matashi sai na rufe idanuna, shi ke nan sai barci ya yi awon gaba da ni, shiru ban farka ba sai da rana ta fito ta soma buguna. Sa'ar da na farka sai na ga an d’ora wani makeken akushi a kan ruwan cikina tare da tubali daya na d’an dabino, da kuma k’wayoyin harub. Sa'annan kuma na duba ko ina ban ga kayan nan da na bari ba, ba kuma wani mahaluki a wurin sai wad’annan tarkacen da aka d’ora kan ruwan cikina. Na tashi na mik’e tsaye, na karkad’e jikina, na fito daga cikin gonar na kamo hanyar gida, ina tafe cikin haushi, ainun, na sami ‘yar uwata tana kuka tana gwama numfashi, sa'annan kuma tana rera wad’ansu baitocin wak’a kamar haka: Jiki ya rame zuciya na ciwo, Hawaye na zuba a idanuna, Wanda nake so yana da wuyar gani, Na rasa yadda zan yi da al’amarina Ya dan uwana na fa shiga damuwa, Ta ciwon son ka da ciwon idanuna Saurayi ya ce, da na ji tana wannan wak’a sai na kifa mata mari, na kwarara mata zagi yadda raina ke so, na doke ta yadda raina ke so, sannan na rabu da ita. Ita ko kula da ni ba ta yi ba, sai kawai ta share hawayenta ta zo wurina, ta kama ni ta runguma, ta hada k’irjina da nata. Ni da goga min k’ irjinta da nawa sai na ji kamar garwashin wuta ne aka goga min, sai na ja da baya na shiga k’ok’arin k’wacewa. Ita kuma tana shafa ni tana matsewa har dai ta gaji ta k’yale ni, sa'annan ta tambaye ni, ta ce, '"dan'uwana, kada dai in ce jiya ma ka yi barci ne da dare!” Sai na ce mata, “haka ne kuwa, domin ni da na je cikin gonar na ga k’asaitaccen shirin da aka yi sai na zauna na kwashi kab’aki. Ban san komai ba sai barci ya d’ebi kayansa ban farka ba sai da rana ta fito. Da na farka sai na ga an d’ora wani makeken akushi tare da tubali guda, da k’wallon dabino, da kuma k’wallon goriba. Na tashi na karkad’e su daga jikina na kamo hanya na zo gida, amma ni ban san abin da take nufi da wannan ba.” Yayin da na fad'a wa ‘yar uwan nan tawa wannan abin sai kuma zuciyata ta rufe na rasa abin da zan yi sai na fashe da kuka na matso gun ‘yar uwata na ce ta gaya mini ma'anar wannan aiki na wulak’anci da wannan mata ta yi mini. ‘Yar uwan nan tawa ta shiga fassara mini ma'anar abubuwan nan da aka d’ora mini a ruwan ciki, ta ce, "abin da take nufi k’wallon goriban da ta zuba kan cikinka, wai tana nufin kai ka zo wurin domin ta amma zuciyarka na can wani wuri, saboda haka ta gargad’e ka da cewar shi al'amarin so ba haka yake ba, har ma ta
Table of Contents