Chapter 1
Chapter 1
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng 01 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO Waziri ya ce, madalla, sa’annn ya fara " ka sani wannan labari ne na mai bege da da abin begensa. Ka sani ya kai sarki mai arziki cewa labari ya same ni na mai bege da abin begensa da mai zance tsakaninsu da abin da ya gudana gare su na al'ajabi mai gangarowa abin da ke gusar da bakin cikin zuciya. A wani lokaci mai tsawo da ya gabata, an yi wani birni da duwatsu suka kewaye shi ana ce da shi Koren Birni, sarkin birnin ana kiransa Sulaiman Shah. Ya kasance mai kyauta ne da kyautatawa, mai adalci da aminci da alheri da karramawa. Yana da kwarjini da mutunci da karramawakyautatawa, mai adalci da aminci da alheri da karramawa. Yana da kwarjini da mutunci da karramawa, ga shi yana son jama'a matafiya su rika shiga kasarsa. Sunansa ya yadu a ko'ina cikin duniya, domin ya jima sosai a bisa gadon sarauta yana yaki da aminci ga masoyansa. To sai dai shi wannan sarki gwauro ne, ba shi mata balle d'a. A tare da shi akwai wazirinsa wanda yake tarayya da shi wajen kyawawan halaye. Suna zaune a kan haka wata rana ya aika waziri ya zo ya same shi ya ce masa, "ya waziri, zuciyata ta baci, hakurina ya gaza, jikina ya raunana, na kasance yanzu nan ba ni da aure, ba ni da mata ballantana na samu magaji. Wannan kuwa ba ka'idar sarauta ba ce, idan saraki suna mulki sun fi jin dadin su mutu su bar magadan da za su hau gadon sarauta ko bayan ransu. Son samu a samu zuriya mai yawa saboda su kara karfi. Kuma manzonmu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa, "ku yi aure ku hayayyafa ku zama masu yawa, domin na yi alfahari da ku ranar lahira." Yanzu me kake gani waziri? Ina dabara?" Da waziri ya ji haka, hawaye ya zubo daga idanunsa, ya sa hannu ya shafe sannan ya ce, "Allah ya ja zamanin sarki, ni kam na nesanta kaina da jaye - jayen ubangiji mai rahama mai jin kai ba. Ko kuwa kana so na jefa kaina ciki azabar Allah? Ina ba ka shawarar ka sayo kuyanga." Sarki ya yi ajiyar zuciya ya dubi waziri ya ce, "Waziri ka sani cewa idan mai mulki ya sayi baiwa ya maida ita sad'aka bai san asalinta ba, bai san danginta ba, ba zai gane aibunta balle ya guje mata. Idan ya sadu da ita ta samu ciki ta haihu da shi, ta yiwu a samu yaro mara jin magana mai zubar da jini, mai girman kai. Ita mace kamar kasar gona take, inda yake juji ne mara kyau zai fitar da shuka mai kyau amma ba za ta yi karko ba. Inda yake akwai fako da yumbu za a sha wahalar tattalin shukar kafin ta girma, amma za ta zama mai karko a karshen lamari. To haka nan dan matar na iya gadon halinta har ya zamana Allah ya yi fushi da shi. Saboda haka, ni ba zan sayo kuyanga na mayar da ita sad'aka ba, nufina shi ne na samu 'yar sarki daga sarakunan kasashen musulmi wadda take kyakkyawa mai hankali kuma mai asali. Idan ka san wata daga 'ya'yan sarakuna to ka fada min na tafi na nemi aurenta a gaban shaidu wadanda za su zama mana masu albarka da iznin mai duka. Waziri ya ce, "Allah ya ba ka nasara, kuma ina addu'ar Allah ya sa ka cimma burinka." Sannan ya kara da cewa, "ka sani ya sarkin zamani labari ya zo min cewa Sarkin Farar kasa, Zaharshahu na da wata 'ya wadda ta kai matuka wajen cikar kyau da kyawon hali. Kalamanta na rudar da mai sauraro, ganinta na gigita masu gani, babu tamkar ta a zamaninta. Ta cika duk wasu siffofi na cikar halitta, kwayar idanunta baki suduk fuskarta na sheki, tana da manyan nonuwa masu gigita mai gani da manyan kuturi sun zauna inda ya dace. Idan ta matso kusa sai mai gani ya fitinu, idan ta juya baya sai mutum ya suma. Ita ta kasance tamkar yadda mawaki ke cewa: Ita ta kasance mai kuturi mai kyawo, Mai hasken sharaba da fuska mai haske Hasken wata bai kai ya haske nata ba Ya zarce yakutu da zinariya a haske Hakoranta na walkiya in tai dariya, Jikinta ko na walkiya ba sassake Manemanta da yawa sun hallaka, A wajen kallonta sun mace babu ke Da waziri ya kare waka, ya dubi
Table of Contents