Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Azizu Da Aziza Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

da saurayi ya ji haka sai ya ce, “ya shugabana, hakika labarina na daga cikin abubuwan mamaki, kuma game da wannan kyalle kuwa akwai ban al’ajibi da ma’abocinsa da wadda ta ba ni shi da wadda ta yi zanen.” Ya warware tsumman sai ga hoton barewa an zana da alharini an mata ado da jan zinari kusa da ita wadansu bareyin ne an zana su da zaren azurfa. A agararta an mata ado da jar zinariya da karrawa uku na zubarjadi rataye a wuyanta.Da Tajul Muluk ya ga wandannan zanen masu kyau sai ya ce, “tsarki ya tabbata ga Allah wanda sanar da mutane abin da ba su sani ba.” Zuciyar Tajul Muluk ta ratayu ga wannan yaro, ya ji yana kaunarsa. Ya kuma ji ya kagara ya ji labarinsa ya ce da shi, “fada min labarinka da kuma labarin wadda ta zana wadannan bareyin.” Saurayi ya ce “ka sani ya shugabana, mahaifina attajiri ne, Allah bai nufe shi da haifar wani da bayan ni ba. Akwai wata yarinya ‘yar baffana ana kiranta Aziza wadda muka tashi tare tun muna kanana. mahaifinta ya rasu, amma kafin ya bar duniya sun yi alkawari da mahaifina cewa za a hada mu aure idan mun girma. To ko a lokacin da na isa munzalin mazaje ita ma ta kai munzalin mace muna tare ba a raba mu ba har lokacin da na ji mahaifiyata na magana da mahaifina suna cewa, “wannan shekara ya kamata a daura auren Azizu da Aziza.” Da suka tsayar da magana sai mahaifina ya tafi domin shirya kayan hidimar aure. Duk da haka muna barcinmu waje daya da sauran al’amura ban san komai ba game da mata, kodayake ita ta fi ni wayo da fahimtar rayuwa kuma tana nuna min kauna. Mahaifina ya kammala shirye–shirye babu abin da ya rage sai a rubuta takardar aure da shaidu ni kuma na shiga wajen ‘yar baffana na take ta. Ya sa ranar daurin aure ta zamana ranar wata Juma’a bayan an sauko daga masallaci. Ya tashi ya zagaya tsakanin abokansa attajirai da fatake ya sanar musu da wannan aure. Mahaifiyata kuma duk ta gayyaci kawayenta mata da dangi na kusa da na nesa. Da ranar Juma’ar ta zo suka gyara gida saboda baki, aka wanke tukwane da sauran abubuwan gida aka kawata ko’ina. Suka daddaura tufafin alharini ko’ina cikin gidan. Mahaifina ya tafi ya sayo alewa da sukari da sauran abubuwan jin dadi, yanzu babu abin da ya rage sai kurum a shafa fatiha. Mahaifiyata ta umarce ni da na tafi gidan wanka na yi wanka ta ba ni wasu kaya masu kyau na alfarma ta ce na sanya su bayan na fito daga wanka. Bayan na fito na saka wadannan kayan, na fesa turare mai kamshin gaske wanda ya budade wajen da kamshi sannan na fito na nufi masallaci domin halartar sallar juma’a. A raina ina zucin idan an idar da salla zan je na taho da wani abokina domin ya shaida aurena. Na ce a raina, “bari na hanzarta dai kada lokacin sallah ya wuce.” Na soma hanzari domin na yi sauri na je na dawo kafin lokaci ya k’ure. Ina tafiya sai na shiga wani lungu da ban tab’a bin sa ba, ina ta kamshi abina, ina tak’ama. Lungun yana da tsayi ga matsatsi na yi tafiya mai nisa ban kai karshensa ba. Na zo wani gida mai dakali sai na shimfid’a hankici na zauna a kai ina hutawa. Gumi yana ta tsattsafo min ga rashin wadatacciyar iska, kaina ya soma ciwo ga zufa na diga har ta soma b’ata min adon da nake tak’ama da shi. Ina so na sa hankici na goge amma babu dama saboda ina zaune a kan sa. Na yi nufin na tube rigata na sha iska kenan ba zato ba nufi wani farin hankici ya fado kan cinya ta. Na dauke shi na ji yana da laushi kwarai ga wani irin kamshi mai dadi yana tashi daga jikinsa, wannan kamshi kadai ya isa ya warkar da cuta. Na daga kaina ina dube – duben ta inda wannan abu ya fado, domin dai na hakikance ba daga sararin samaniya ya sauko ba. Daga kaina ke da wuya muka yi ido hudu da matar da ke da zanen wadannan bareyin' Ta leko ta tagar karfe, idanuna ba su taba ganin kyakkyawa irin ta ba. Harshena kuwa ya yi kadan ya fadi irin tsantsar kyawon da Allah ya ba ta. Yayin da ta ga ina kallon ta sai ta daga yatsunta biyu ta sa a bakinta sannan ta hada yatsanta na tsakiya da manuninta ta dora a kirjinta a tsakanin nonuwanta. Sannan ta maida kanta ta rufe tagar. Daga rannan wuta ta huru a cikin zuciyata ta rika hauhawa tana cin dukkan tunanina, kallo dayan nan da na yi mata ya jawo min bukatar sake ganinta nan gaba. Sonta ya cika min zuciya na kasa samun sukuni. Ga shi ta yi min wasu alamu da nune – nune da hannunta wanda ban fahimci manufarsu ba, na samu kaina a mai dimaucewa na gigice saboda ban san abin da take nufi ba. Na sake duban tagar a karo na biyu amma na gan ta a rufe, na zauna a nan ina jiran na ga an sake bude kofar har rana ta fadi dare ya yi amma babu amo babu labari. Yayin da na gaji da jira na saddak’ar ba za a sake bud’e tagar ba, sai na tashi daga inda nake na bud’e hankici nan. Wani kamshi mai dadin gaske ya tashi har sai da ya buce kamshin turaren jikina. Wannan kamshin na almiski ne ya sa na ji na cika da farin ciki tamkar a aljanna. Na warware hankicin a hankali sai na ga wata takarda ta fado daga ciki. Na bude wannan takardar ita ma tana fitar da wani kamshin mai dadi. A jikinta na ga an rubuta:: Na aika masa da wasikar soyayya, Na rubuta da hannuna domin kwarewa Abokina ya ce me ya sa ki rubutun nan Mai kyau siriri, karatun bai dacewa? Sai na ce “ai mai kyau ya fita zakka, Zurfin soyayya ya sa ni rubutawa Daga nan na jefa ganina kan hankicin domin kare masa kallon kyawon tsarin da yake da shi, na ga an ja wasu layuka biyu an rubuta da zare da allura: Kundukukinsa an rubuta layi biyu, A bisansa ma da rubutun hannun Raihanu Hasken wata na da ban mamaki kwarai Jikinsa akwai ni’ima kama da ta almiskinu A daya bangaren kuma an dinka layi biyu da zaren alharini kamar haka: ‘Yan matansa sun yi rubutu a kundukukinsa da lu’ulu’u, Shedara biyu a tufa mai kyau da kyawon kallo Yayin da na gama karanta wadannan wakoki da ke jikin wannan hankici sai wutar bege ta sake ruruwa a zuciyata, na ji na kagauta sosai domin na ga wannan matar. Na dauki wannan kyalle da takardar na tafi gida da su ba tare da sanin yadda zan yin a cimma burina ba, domin ba ni da basirar soyayya kuma ban san ma’anar wadannan alamun da ta yi min ba. Ban san na isa gida ba saboda tunani, dare ya yi nisa kuwa lokacin, na shiga wurin barcinmu na tarar ‘yar baffana tana zaune tana kuka da hawaye.

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16