Chapter 12
Chapter 12
ka yi sake ka koma wurinta, ka tabbata idan har ka kuskura ka yi barci lalle za ta yanka ka. Ni dai ban ji ba, sai na ci gaba da neman taimako daga wurin yar uwan nan tawa har dai ta ce, “to, na yarda zan taimake ka amma fa sai ka tabbatar min cewan za ka yarda da dukkan abin da na gaya maka. Nan da nan a cikin marairaicewa na yarda, na ce mata zan yarda da dukkan abin da ta gaya mini, sa'annan ta yi mini alkawarin za ta gaya mini kome da kome a lokacin da zan tafi, in yamma ta yi. Can kuma sai ciwon so ya motso mata ta rungume ni a k’irjinta, ta ciccib’e ni ta d’ora ni kan shimfid’a ta shiga yi mini tausa har barci ya d’auke ni. Yayin da nake sharar barcina sai ta dauko mafici ta shiga yi mini fifita a fuska da sauran sassan jikina har yamma ta yi sa'annan ta tayar da ni daga barci. Sa'ar da na farka sai na ganta a zaune daidai kaina da mafici a hannu tana ta rafsar kuka, hawaye na zuba a idonta har zanenta ya jik’e don sharar hawaye da take yi da shi. Lokacin da ta ga na farka daga barcin sai ta tashi ta kawo mini abinci, ta ce na ci amma ni kuma sai na k’i cin abincin. Da ta ga haka sai ta ce lalle ban yi zaton za ka ji maganata ba ke nan, ta dai shiga rarrashina a kan in yarda in ci abincin nan nikuma na k’i. Da ta ga lalle ban da nufin cin abincin sai ta rik’a gutsurawa tana saka mini a baki saboda ta fahimci cewar ina bukatar cin abincin, amma rashin sabo da shi ne ya hana ni ci, da haka dai na ci abincin har na k’oshi. Sa'annan ta d’auko mini tataccen ruwan inabi ta ba ni na sha. Da na gama ta zo ta wanke mini hannuna, ta goge mini hannaye da mayani, ta kawo turaren miski da wardu ta shafe mini hannuwana da jikina sa'annan lokacin da dare ya yi ta shiga yi mini gargad’in cewan kada in yarda in yi barci, ta shaida mini cewan matar nan ba za ta zo wurin da zan jira ta ba sai kusan k’arshen dare, ta kuma yi mini kyakkyawar addu'a ta ce, "Allah ya kiyaye ka, Allah ya ba ka sa'a ya kuma dawo da kai lafiya". Daga k’arshe kuma ta ce, “ina fatar dai ba za ka manta da maganar biya mata baitin wak’ar nan idan kun sadu ba, amma kuma ta sake nanata mini cewan kada in biya wannan baitin wak’ar sai bayan mun gama za mu rabu, na komo gida. Yayin da ta ga na kama hanya sai ta fashe da kuka har ni kaina a rannan sai da hankalina ya tashi game da kukan ‘yar uwan nan tawa. Sa'annan na ce da ita shin wace wasiyya ce taki, da kike bukatar gaya mini, ta ce da ni, ba ta da wata wasiyya sai dai baitin wak’ar nan da ta ce in rera wa matar nan a lokacin da za mu rabu.Shi kenan sai na shirya na fito gida na kama hanya cikin kuzari da jin k’arfin jiki da na hali har na iso inda gonar nan ta ke. Na shiga cikin gonar, na sami wurin an shirya shi sosai, babu abin da ya ragu daga shirin farko sai ma abin da ya k’aru na daga kayan kyalli da na faranta ciki. Da zuwana sai na kama wurin zamana na zauna ina cike da farin ciki da fara'a, na shiga nishadi da zuciyata, na k’i yin barci kuma bisa sa'a a rannan babu maganar yunwa, balle barci. Na zauna a nan wurin idona biyu har wajen asubahin. Da na ga har gari zai waye ban yi barci ba babu kuma alamarsa ga idona, sai kuma na shiga damuwa saboda ni duk na rud’e da murna saboda wannan bajinta da na yi, sai na ga kuma duk daren a rannan ya yi mini tsawo saboda d’oki, a rannan daren nan ya yi tsawon shekara guda a wurina, na daure dai na k’i yin barci, har zakaru suka soma kuka, na cika da jin dadin wannan bajintar tawa. Babu jimawa duk sha'anin ya juya, abubuwa suka soma cakudewa, yunwa ta yi wo mini sallama baki daya, hankalina ya fara kad’uwa, na rasa abin da zan yi sai na tashi na nufi gefen da abinci yake, da zuwana kamar dabba sai na bude abinci, na zauna na ci, na k’oshi. Nan da nan na ji kaina ya yi nauyi ana yi mini motsi a cikin kai ta ko’ina, sai na kwanta a kishingid’e zan yi barci. Allahu mai Girma, na kishingida kenan sai na ji motsin yarinya tana zuwa daga nesa sai na mik’e tsaye na je na wanke hannuna, na goge bakina, sa'annan na kintsa jikina daidai na zauna. Bayan duk na k’are wannan sai ga yarinya ta iso tare da kuyangi su goma suna biye a bayanta. Sa'ar da suka iso wurin sai suka saka ta tsakiyarsu. Lahaula Wala Kuwwata, tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci kwad’o, lokacin da na juya na dubi matar nan, sai na ga wurin ya yi haske, yarinyar tana k’yalli sai ka ce wata a tsakanin taurari, kayan tufafin da ke jikinta na wani koren had’alashi ne, wanda aka yi wa baza da zinari ja. Kyawunta ya kasance kamar yadda wani mawak’i ya yi mata wak’a yana cewa: Wannan mata tana yanga ga masoyanta, Musamman idan ta sa kaya koraye Na tambaye ta ‘yaya sunanki gimbiya’, Ta amsa ‘ni ce mai k’ona zuciyar mazaje’ Na ce ‘to ni dai kam ina kaunar ki’ Ta ce ‘to ka fad’a wa dutse kai waye’ Sai na ce idan zuciyarki tamkar dutse take, To Allahu ya fitar da ruwa daga dutse. Yayin da ta gan ni a zaune sai ta yi dariya, ta ce, “yaya aka yi ka farka daga barci? Tunda na ga ba ka yi barci ba a wannan karo, to lalle na tabbata kana so na, domin kuwa rashin barci shi ne halin mai ciwon so.” Ta juya wurin kuyangi ta yi musu alama da idonta, ni kuma ina fake da ita, sai na ga kamar walk’iya ce aka yi saboda hasken idon nan nata da ta kada. Sa'ar da ta k’ifta musu ido sai na ga sun juya sun tafi nasu wajen daban. Yayin da suka tafi sai na ga ta zo wurina, ta kama ni ta rungume ni a k’irjinta ta kama leb’en saman bakina ta tsotsa, ni kuma na tsotsi na k’asan. Na rik’e duwawunta na matsa su, na shafa, na shafa, na yi mata cakulkuli sai dukanmu muka fad’i k’asa, sumammu. Yayin da muka farfad’o sai na ga ta sassauta daurin kamfanta zuwa daidai k’wauri muka fad’i muna runguma da shafa da sumba muna magana da juna a hankali, k’afafunmu da hard’ewa da juna muna juye – juye. Na hau bisa ruwan cikinta na yi nink’aya, na yi sukuwa na kai fage, na sake juyowa, sa’annan muka kawo numfashi baki d’aya, gab'ob'inmu suka saki. Kowannenmu ya cika da farin ciki da jin dad’i. Na samu shiga
Table of Contents