Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Azizu Da Aziza Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

ya warwatse ko’ina, sai ta ce, "kaico, lalle duk wanda ya hadu da ciwon so mahaukaci ne, shi da mahaukaci daidai suke." Yayin da ta ga haka ita ma sai nata hankalin ya tashi, hawaye suka zubo daga idonta ta ce, "wallahi dan'uwana, ni ban ga laifinka ba, wannan shi ne alamar soyayya." Sa'annan sai ta tashi, ta kwashe abincin nan da ya watse a ƙasa, ta share wuri, ta debi kwanukan abincin ta wanke, ta sake komowa wurina tana rarrashina, tana ba ni magana, amma duk a banza ni sai roƙon Allah nake ya wayi gari don na tashi na tafi wurin aminiyata. Kashegari sai na tashi a firgice ina cikin mayen so tsundum, na kama hanya da hanzari, har ma nakan had’a da gudu, har na iso ga wannan lungun, na shiga na je kan dakalin nan na zauna.zauna. Zamana ke da wuya sai na ga an bud’e tagar nan, ta fito da kanta, tana murmushin dariya, ta mayar da kanta, jim kad’an kuma ta sake leƙowa na biyu da madubi da wata jaka, sa'annan kuma da wani kasko wanda aka shuka hatsi a ciki. Hatsin ya yi tsiro, kore shar, d’ayan hannun kuma ga fitila ta riƙe. Abin da ta soma yi shi ne ta d’auko madubin nan ta sa shi a cikin jakar nan ta d’aure, ta jefa jakar cikin gida, sa'annan ta taro gashin kanta ya koma a gaban fuskarta har ya rufe fuskar, ta sake d’aukar fitilar nan ta saka a cikin shuka. Nan da nan kamar ƙiftawar ido sai shukar ta kama wuta ta ƙone ƙurmus, bayan da ta ƙare wadannan isharori sai ta mayar da tagar ta rufe. Ganin haka fa ni ko sai zuciyata ta tsinke, sai zuciyata ke bugawa na shiga tunani, na kasa gane abin da ta ke nufi da wad’annan isharorin, na tashi na nufo gida raina ɓace har na shiga na sami ‘yar uwata tana tsaye a jikin katanga ta manna fuskarta a jikin katangar. Yayin da na ga haka kuma sai zuciyata ta dad’a tsinkewa, cikina ya d’uri ruwa na rasa manufa, ita kuwa wannan ‘yar uwar tawa kome na yi mata ba ta kula ni, saboda so na da take yi, amma ni ban damu ba hankalina gaba d’aya ya koma wurin waccan mata, ita ma ‘yar uwan nan tawa ta dauki hak’uri ta d’ora wa zuciyarta, ba ta damu da duk wad’annan abubuwan da nake mata ba. Sa'ar da na dube ta na ga ta d’aure fuskarta wuri biyu, sai raina ya sake b’aci, da na duba sai na ga wuri d’aya don rauni ne ta daure, dayan kuma saboda zuban hawayenta har wurin ya yi gurbi. Lokacin da ta gan ni sai ta rera wad’annan baitoci: Kai me tafiya da zuciyata na amince, Duk inda kake Allahu ya amince maka. Na sani Allahu yana nan tare da kai, Masoyina ni kam wallahi ina kaunarka. Ni kam bak’in ciki sai karuwa yake yi, Gare ni domin na kusan na rasa ka Ya mai ceton jama’a daga ciwuta, Ga ni gare ka na zo don ludufinka Hawayena suna ta zuba a idaniyata Kaico idan na san kana wurin zan neme ka Yayin da ta gama wannan wak’a tata sai ta dubo ni, sa'annan ta shafe hawayenta, ta zo wurina amma sai ta kasa yi mini magana, ta yi shiru har wani lokaci, sa'annan ta ce, '"d’an uwana," gaya mini abin da kuka yi da yarinyarka. Na shaida mata, sa'annan ta ce da ni, "ka dauki hak’uri, lokacin saduwarku da ita ya kusanta, lalle abin da kake buk’ata game da ita, za ka samu. Watau madubi wanda ta saka a cikin jaka, tana nufin wai ka yi hak’uri har rana ta fad’i, sakin gashin kanta da ta yi har ya rufe fuskarta, tana nufin wai idan dare ya yi duhu ya kama, har ya rufe hasken rana, tana son ka je can wurinta. Dalilin shuka ta cikin kaskon kuwa, wai ka shiga cikin gona wadda ke nan kusa da lungun. Nufinta da fitila kuwa wai ka je can gonar ka shiga cikinta za ka sami fitila mai haske, idan ka sami wannan fitilar ka nufi wurin, ka je ka zauna, za ka gan ta ta zo, har ma ta k’ara da cewan wai sonka da take yi ya kusa halaka ta.” Sa'ar da na ji haka sai hankali ya kwanta sa'annan na ce da ‘yar uwar nan tawa, sau da yawa fa kina kwatanta mini cewar in hak’ura in koma, alhalin kuwa ko na tafi sai in dawo hannu wofi, ba abin da yake faruwa daga cikin buk’atata. Ni dai ban ga wata ma'ana ba a cikin wannan fassarar taki ba. Sai ‘yar uwan nan tawa ta yi dariya, ta ce da ni, "hak’urinka na wannan yini kad’ai kafin fad’uwar rana, in dai har dare ya yi, za ka sadu da abin da kake buk’ata, wannan magana tawa gaskiya ce, wadda ba ta buk’atar wata rantsuwa. Can kuma da ta nisa sai ta rera wata wak’a: Kwanaki na shigewa dare ya yi, Dakunan masu bak’in ciki bai waye ba Duk abin da samunsa ya zam wahala. To sauk’in lamarin na nan a gaba Lokacin da ta k’are wak’a sai ta zo wurina ta soma rarrashina, tana ba ni magana, amma ba ta sami damar kawo mini abinci ba don gudun zuciyata, sai ta tub’e mini rigata, sa'annan tace mini, "zo ka zauna nan d’an uwana saboda ina son in yi maka wata hira wadda za ta kwantar maka da hankali, kafin nan zuwa fad’uwar rana, in Allah ya so dare ba zai yi ba sai kana tare da wadda kake so." Ni kuwa ko kula ta ban yi ba. Ban ma san abin da take yi ba, ko wajenta ban juya ba, balle har na san tana wurin, ni a lokacin zuwan dare kad’ai na sa a zuciyata, sai fata nake Allah Ubangiji ya gaggauta zuwan daren nan a cikin zuciyata. Yayin da dare ya yi sai ‘yar uwata ta fashe da kuka, ta dauko k’wayar miski guda na asalin, ta ce da ni, hak’ura ka sa wannan k’wayar a bakinka, idan ka sadu da wadda kake mutuwar so sa'ar da ka biya buk’atarka da ita sai ka biya mata wannan baiti ka ce, "ya jama'ar masu ciwon so, ku ba ni labarin yadda in son mutum ya same ka za ka yi." Sa'an nan ta ce idan na je na sami wannan matar kuma buk’atata ta biya game da ita, na wak’a mata wannan baitin, amma kuma sai ta rantsar da ni cewan kada in yarda in yi wannan baitin sai bayan mun k’are dukan sha'aninmu, watau yayin da zan fito zuwa gida daga wurinta. Yayin da ta k’are yi mini wannan bayanin, sai na ce da ita, “na ji, na kuma yarda” Sa'annan sai na fito daga cikin gida kamar lokacin sallar isha’i na kama hanya, ina tafe har na iso wurin gonar nan da muka yi alk’awari. ZANCI GABA5 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO ina ta tafiya harna iso wurin gonar nan da mukayi alk’awarin had’uwa da matar nan, na shiga cikin gonar na hangi wani haske da nisa a cikin gonar, sai na nufi wajen hasken. Yayin da na

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16