Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Azizu Da Aziza Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

Da ta gan ni nan da nan ta share hawayenta ta mike ta tare ni da murna. Ta cire min falmaran dina sannan ta zaunar da ni tana tambaya ta dalilin bacewa ta. Ta kara da cewa, “duk mutane sun hallara, tun daga sarakuna da manyan mutane da attajirai da sauran jama’ar gari da alkalai da shaidu duka ana ta nemanka za a daura aure a shirya takardar aure ka sa hannu. Amma da suka ga ba ka zo ba lokaci kuma yana kurewa sai suka ci abincin da aka tara suka yi tafiyarsu.” Sannan ta kuma cewa, “mahaifinka ya yi fushi mai yawa, har saboda fushin ma ya yi rantsuwar ba za a daura auren ba sai shekara mai zuwa, saboda yanzu ya kashe kudade masu yawa har da basussuka a yanzu ba shi da halin sake wani bikin.” Ta dube ni sosai ta ce, “kai kuwa ina ka shiga haka ake ta nemanka sai yanzu ka dawo?” Na bude baki na ce mata, “ba na so ki matsa min da tambaya.” Sannan na kwashe labari kaf na fada mata, na dauko hankicin nan da takarda na nuna mata, ta karba ta karanta, sai na ga hawaye na kwararowa daga idanunta. Nan take ta rera wannan wak’ar: Duk wanda ya ce so a farko lokaci na da sauki, Ce masa ‘ka yi karya!’ ciwon so wahala ne Wahalar so da ciwo nai ba sa jin kunya, Ciwon so yana shiga da wuya ka gane Kudi mai kyau ba sa wuyar ganewa da na banza, To ciwon so na da azabtarwa haba mutane Ciwon so masifa ne a bisa hakikar gaskiya Yana da wahala ka kamu da shi ka warke So da kake ganinsa idan zan fada maka, Shi kan sa ya rabu gida da dama ka gane Sannan ta tambaye ni “me ta ce maka, kuma wad’anne alamu ta yi maka?” na amsa mata, “ba ta ce da ni kanzil ba, amma ta sa yatsunta a baki kuma ta dora su a kan kirjinta suna kallon kasa. Daga nan sai ta mayar da kanta ta rufe tagar. Daga nan ban sake ganin ta ba. Amma duk da haka zuciyata ta tafi wajen kaunar ta, a nan na zauna har rana ta fadi ina kallon tagar da zummar ko za ta sake lekowa. Da na ga dai babu alamar haka sai na hakura na taho gida. Wannan shi ne labarina, ina rokon ki taimake ni a wannan sha’ani” Da ta ji haka ta daga idanunta ta kalle ni sannan ta ce, “wallahi d’an uwana idan kwayar idanuna kake so zan ciro na ba ka, zan yi duk yadda zan yi ka cimma burinka, ita ma ta cimma burinta domin ita ma tana kaunarka fiye da yadda kai kake son ta ma.” “Yanzu dai menene ma’anar alamun da ta yi min?” na tambaya a kagauce. Aziza ta ce, “yatsunta da ta sa a baki tana nufin kai kana matsayin mijinta a bisa jikinta, kuma ta k’uduri niyyar saduwa da kai a zimmar miji, amma mayani cewa shi tana nufin sallamawa masoyi abin da yake so. Takarda kuwa tana nufin ta mika kanta gare ka, amma abin da take nufi da dora yatsunta a kan tsakanin nonuwanta kuwa tana nufin bayan kwana biyu ka koma inda ka gan ta domin ku sake haduwa.” ‘Yar baffana ta ce, “wallahi da ina fita waje da sai na sada ku da juna har na lullube ku a mayafi daya ku ji dad’inku. Ka sani cewa ita mai bege ce a gare ka, amintaccen so take maka. Wannan shi ne ma’anar isharorin da ta yi maka.” Saurayi ya ce, “yayin da na ji haka sai na gode mata bisa wannan fassara. Na tafi dakina na zauna kwana biyu ba na ci, bana sha. Na sa kaina a cinyar ‘yar baffana, ita kuwa tana ba ni magana mai dadi tana shafa min kai tana ce min, “ka saki ranka, ka k’arfafa aniyarka, ka cigaba da hak’uri kana mai dad’ad’a zuciyarka da tunaninka ka ƙarfafa aniyarka, ka cigaba da hak’uri kana mai dad’a ka sa kayanka ka tafi wurinta yanzu don ka nuna mata cika alkawari. Sa'annan sai ta tashi. ZANCI GABA04 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO Sannan sai ta tashi ita da kanta ta sauya mini riga mai kyau, ta kuma turara mini turaren wuta, ni kuma zuciyata ta fara saki kadan-kadan, na fito daga cikin gida na kama hanya ina tafe ina nazarin hanyar har na shigo cikin wannan lungu mai zurfi na zuwa gidan nan mai dakali. Na zauna kan dakalin nan daidai wurin da na zauna a farkon zuwana, zamana ke da wuya, sai na ga an bude tagar nan, na daga kaina sama na duba sai ga matar nan ta leko kamar yadda ta leko da farko. Sa'ar da muka hada ido fa sai na dimauce na rasa hankalina, jijiyoyin jikina duk suka yi sanyi lakwas na zauna kamar na suma. Don farin ciki har na rasa abin da zan yi. Yayin da hankalina ya komo gare ni sai na sake daga kaina na dube ta ai kuma duk abin sai ya sake rikice mini, na yi nadama da haka, sa'annan na sake dubanta na gan ta da madubi a hannu, da kuma wani hankici ja, ita kuma da ta dube ni sai ta d’aga damatsanta, ta bude su har na hangi abin da da ke cikinsu, hankalina ya girgiza. Sa'annan ta ware yatsunta guda biyar ta buga su a kirjinta, ta sake daga hannuwanta ta dauko wani ruwa da ke ajiye kan tagar nan, ta dauki hankicin nan ja ta saka shi cikin ruwan nan, ta kuma cire shi, ta zuro shi daga wajen wannan tagar, ta yi haka har sau uku sa'annan ta matse shi ta nada a hannunta, sa'annan kuma ta sunkuyar da kanta kasa ta dubo ni, sai ta mayar da kyauren tagar ta rufe, ba ta ce da ni kome ba, ta bar ni a cikin dimuwa da tunani ban san ma'anar duk abubuwan nan da ta nuna mini ba. Na zauna nan wurin ina jiran ta sake lekowa, amma shiru babu ita babu alamar ta, ban tashi daga wannan wurin ba har isha’i ta yi, sa'annan na taso na kamo hanya zuwa gida, ina ta tafiya ni kadai a tsakar dare har na iso gida. Na sami ‘yar'uwar nan tawa ta hada gumi sharaf sai hawaye ke zuba a idonta tana rera wasu baitoci kamar haka: Shin me ya sa kake zargina don ina son ka? Na fada maka dole ne wurina kaunarka Ni’imarka ta fi ta reshe gamsarwa Duk da zarginka wajena yaushe ne za ni gan ka? Na wahalta da wannan tsanani na kauna, Ya fi takobi aibu idanuwa na Baturka Wayyo ciwon so ya riga ya kama ni, Na kwanta ciwurwuta don kaunar ka Na ji haushin masu zargina kwarai, Wai don na fadi kaunarka gabanka Sa'ar da na ji wannan wak’ar tata fa sai baƙin cikina ya dad’u, raina ya dada ‘baci, na rasa ta kamawa, can na baro ba dadi nan kuma na zo na sami ba dadi, sai na fad’i a tsakiyar filin gida ina kuka da mirgina, ‘yar uwar nan tawa ta zabura da hanzari ta zo

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16