Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Azizu Da Aziza Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

sarki Sulaimanu Shah ya ce, "ina ba ka shawarar ka aika da wani mutum mai girman daraja da sanin wayon zaman duniya zuwa ga mahaifinta ya nema maka auren ta. Kuma wanda za shi din ya zamana mai iya magana domin sarkin yana da zafin rai. Domin kuwa hakika ita ce ta dace da kai, babu tamkar ta a nan kusa da nesa. Za ka ji dadinta sosai yadda ya kamata, kuma da sannu sai ka ga Allah ya cika maka burinka game da ita." Sarki ya ji dadin wannan kalami, kirjinsa ya cika da farin ciki, bacin ransa ya gushe. Ya dubi waziri ya ce, " wannan bayani naka daidai ne waziri, kuma babu wanda ya dace ya tafi wajen sarkin nan sai kai. Domin na yaba da kwazonka da mafificiyar dabararka. Yanzu ka tafi gida ka shirya ka tafi gobe da duk wadanda suka kamata ka nemo min auren wannan matar. Da fatan kuma ba za ka dawo ba sai da ita." Waziri ya amsa, "na ji na yarda." Waziri ya tafi gida ya shirya kayan tafiya, ya samu kyaututtuka manya – manya wadanda ake yi wa sarakuna na daga duwatsu masu daraja da tufafi da sauran su. Ya shirya ingarmun dawaki na hawa da kayan fada da sulken yaki irin kirar Annabi Dauda. Sannan ya shirya akwatunan dukiya mai yawa wadda baki ba zai iya lissafa ta ba. Sannan ya kawo rakuma da alfadarai da kuyangi dari. Sannan ya shirya da hakimai dari su raka shi. Aka kawo laima bias abin hawan waziri jama’a suka riki tutoci suka rankaya. Kafin tashinsu sai da sarki ya yi masa nasihar kada ya jima ya dawo da wuri da zarar bukata ta biya. Bayan sun tafi sarki ya zauna cikin kaguwar su dawo masa da labari mai dadi, kullum yana zuba ido da kasa kunnen dawowar waziri. Ayari kuwa suka yi ta tafiya dare da rana safe da yamma, har ya zamana bai fi tafiyar wuni guda ba zuwa birnin Baira’a, nan waziri ya yi umarnin a sauka gefen wani kogi. Daga nan ya tara makusantansa yatabbatar wannan aure bisa kayyadajjen sadaki. Sannan aka yi addu’a kowa ya shafa. Waziri ya tashi ya fito da kayayyaki na kyaututtuka da na ado da na kamshi duka ya shiga rarrabawa mahalarta bayan wanda ya ajiye wa sarki. Sarki ya shiga domin kintsa ‘yarsa da kuma hidima ga waziri da mutanensa domin yin biki don nuna jin dad’in faruwar wannan al’amari. Aka yi ta shagalin biki Waziri ya yi ta rabon kyaututtuka iri – iri ga manya da kananan fadawa. Suka wanzu cikin wannan sha’ani na biki har wata biyu cur ana ta annashuwa da jin dadi mai ban kaye da tausasa zukata. Bayan wannan aka shirya komai da komai na bukatar amarya, sarki ya shirya wata babbar rumfa a nan kofar fada, aka yi ta shirya wa kayanta wadanda ke cikin akwatuna manya – manya. Sannan aka hada da kuyangi na kasar Turkawa da na Girkawa da Rumawa kuma aka tanadar wa amarya wata babbar ma’ajiya ta dukiya da sauran duwatsu masu daraja. Aka sa alfadarai biyu su dauke su. Sannan aka kawo darbuka mai kyau mai cike da ado na musamman aka dibiyawa taguwa. Sarki ya zo da kansa ya yi musu rakiya farsakai masu yawa, sannan ya yi mata nasihar bin miji da hakkin aure. Sannan ya yi sallama da waziri ya juyo gida cike da farin ciki. Waziri da ‘yar sarki Gimbiya, amarya da sauran jama’a suka rankaya suka yi ta tafiya ba dare da rana har ya kasance tsakaninsu da birnin bai wuce kwana uku ba. Sannan ya tashi wakili ya garzaya domin yin albishir ga zuwansu tare da amarya. Sarki ya cika da farin ciki mai yawa, ya yi wa jakadan nan karimci mai yawa gami da sutura da sauran kyaututtuka, ya umarci manya fadawa su shirya domin zuwa taryen wannan tawagar amarya. Kowa ya shiga cikin kayan adon sarautarsa sannan suka dunguma da tutoci masu kayatarwa zuwa bayan gari. Sarki ya yi umarnin kowa da kowa ya fita babba da yaro namiji da mace su fita domin taryen amarya. Lokacin da mutanen gari suka ji haka fa sai mamaki ya kama su, duk suka fito da hanzari, amma Sarki ya ce kada a shigo da ita cikin gari, sai da dare. Manya manyan mutane, su ne suke yi wa wannan amarya ta Sarki kowace irin hidima, kafin ta iso cikin garin. Har wa yau kuma Sarki ya sa aka caba wa hanyoyin cikin gari ado ko’ina. ZANCI GABA02 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO Ita kuwa hanyar da amarya za ta biyo kuwa, sai aka rufe ta da zannuwan alharini masu alfarma, sauran hanyoyi kuwa aka yi musu ado da dardumai, aka daura fitillu masu launi iri iri. Sa'an nan a kofar fadar aka daura wata irin makekiyar fitilla mai hasken gaske,amma hasken nata kore ne shar, a gefen hanyar da amarya za ta shiga zuwa gidan Sarki aka daza mutane. Can sai ga amarya ta dumfaro, kuyangi na gabanta, barori suna biye da ita a baya, amaryar kuwa ta ci ado irin na zamani mai kayatarwar gaske, musamman mahaifinta ya hada ta da wadansu 'yan moren matansa, don su rika shirya mata ado, su kuwa wadannan 'yan moren sai da Sarki ya tura su wata kasa mai nisa don su koyo yadda ake yin ado, suka gwanance sosai. Sa'an nan suka dawo gida, suka ci gaba da yi wa 'yar nan tasa hidimar ado. A daman amarya kuwa askarawa ne wadanda ake cewa sai baba-ta-gani ke kewaye da ita haka ma a gefen hagunta, ita kuwa tana tafe a cikin darbuka kan taguwa har ta isa gidan Sarki, mutanen gari duk suka yo caa suna kallonta, ko’ina sai bushe-bushen bigila da kade-kaden ganguna ke tashi, mazaje sai karkada masu suke, suna jefa su sama, suna cafewa, abin gwanin ban sha'awa. Kamshin turare ya bice wurin ko’ina Dawakai kuwa sai barade ne ke sukuwa da su, wuri duk ya rude babu masokar tsintsiya, babu irin adon da ba ka samu a wurin. Dabbobi kuwa har na daji an hau kansu rannan, ga giwaye, ga damisu, ga zakoki, da dai sauransu birjik. Mai tutsu yana yi, mai ruri yana yi, mai yakuta yana yi, har dai aka isa filin kofar fada, sa'annan Waziri ya bi da amarya ta wata kofar asiri, wadda aka fasa musamman saboda amaryar. Lokacin da amaryar nan ta sauka, sai duk wuri ya haske, saboda kyawon fuskarta, da kyallin kayan jikinta. Fili ya haske saboda kayan lu'u-lu'u, da ya ke jikinta, sai ka ce wata ne ya sauko kasa. Sa'ar da dare ya yi aka sake bude kofar nan ta asiri za a fito da amarya zuwa gidan da Sarki ya sa aka shirya mata. Barori suka jeru cikin layi, amarya kuma ta iso da kuyangi a gaban ta sai ka ce wata a tsakanin taurari, ko kuma goran lu'u-lu'u a tsakanin kananan duwatsun lu'u-lu'u, wanda aka shirya a zare. Bayan an shigar da amarya cikin gida, sai kuma aka shirya kayayyakinta cikin daki, su gadon lu'u-lu'u, wanda aka zuba wa shimfid’a mai daraja, an kuma zayyana bangon dakin da zane na yakuti, amarya ta shiga daki ta zauna kan gado.

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16