Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Azizu Da Aziza Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

Sarki kuma ya shigo wurinta, Allah ya sanya son ta a zuciyarsa, nan take a wannan ranar ya dauke budurcinta, hankalinsa ya kwanta daga jarabarta da ya sha fama a kai, domin kuwa duk watannin nan da Waziri ya yi a wurin neman aure can a garin Madinatul Baila'a, tun ran da ya tafi Sarkin sai ya kasa barci, ya kasa zaune, ya kasa tsaye, yana tunani kan wannan yarinya da Waziri ya ba shi labarinta tun kaftn ya gan ta ya fada jarabar son saduwa da ita. Bayan da Sarki ya dauki budurcin yarinya sai ya fito filin fada ya sa aka shirya bidi'a kasaitacciya, aka kuma shirya walima muhimmiya, a wurin walimar nan babu nau'in sha da babu wurin, balle na wajen abinci, su naman 'ya'yan shila, da na sauran tsuntsayen daji, da dabbobin daji. A bangare kayan sha kuwa ga su zuma, ga giya iri daban-daban. Sarki ya sa aka nemo gwanayen masu kade – kade suka yi ta yi, ana annashuwa. Wasu kuma suka hau dawakai suka yi ta sukuwa suna nuna bajinta iri - iri. Haka aka yi ta biki da wasanni har kwana uku sannan kowa ya watse. Bayan amarya ta yi kamar wata guda sai ciki ya soma bayyana a cikin gida da wadanda ke tare da ita. Tun zuwanta kuwa Sarki bai sake fitowa fada ba, sai bayan watan nan guda, sa'annan rannan ya fito fada aka ci gaba da zaman majalisa, aka ci gaba zarafin mulki. Kwanci tashi har watannin cikin yarinya suka cika, wata tara daidai. Rannan sai ta shiga nakuda, Allah ya saukaka mata wahalar nakuda, a cikin sauki, ta haifi da namiji, mai shaidar arziki a goshinsa, yana ta kyalli, aka yi sauri aka sami Sarki a Majalisa aka ba shi labarin haihuwar. Kada ka so ka ga fuskar Sarki a rannan, ta cika da fara'a, ya yi farin ciki matuk’a, ya kawo kurfi da kayayyaki na alfarma ya bai wa masu albishir, nan da nan aka rufe zaman Majalisa. Sarki ya tashi ya shiga cikin gida ya iske Sarauniya, ya dube ta, ya dubi yaron da aka haifa, ya ga hasken nan a fuskar yaro, ya sake dubar yaro, ya yi makakin irin kyawon wannan yaro, ya tabbata ya dace da wak’ar shahararren mawaki da yake cewa a wasu baituka: Allah ya ba shi kyau, ya ba shi daukaka, Zaki na sansani, na daula, tauraro, tsinin Mashi da kaifin takobi da askarawa da mayaka Dole duk sun durkusa yayin da ya zo, Amma fa kada ka dora shi kan mama mai tudu, A’a kai dai dora shi bayan doki shi ya fi a gare shi Domin kuwa shi jinin mazaje ya fi dadin sha a gun sa. Bayan da Sarki ya kare wa jinjiri kallo sai Unguwarzoma ta zo ta dauke shi ta yanke masa cibiya ta saka masa tozali, da rana ta kewayo aka rada wa yaron suna Tajul Maluki Harun. A ranar bikin an yi shagali mai yawa, har ya fi na lokacin tarewar amarya. Shi ke nan sai akasai aka ci gaba da renon yaro, har ya kai dan shekara bakwai, sa'annan Sarki ya nemo malamai masu zurfin ilmi da gaske, suka zauna, suna karantar da yaro, har shekara bakwai. A cikin wannan lokacin ya kasance yaro yana girma ilmi na shigarsa, har ya kai matsayin ya san duk abin da ake bukatar ya sani, ya sami cikakken ilmin karatu da na rubutu. Ya san hanyoyin ladabi da hikimomi ingantattu. Yayin da malamai suka kare aikinsu sai Sarki ya yi musu sallama mai dimbin yawa, tare da kyautatawa. To, bayan yaro ya kware a fagen ilmi, sai kuma aka saka shi a hannun mayaka, saboda su koya masa dabarun yaki, su nuna masa yadda a ke sara, da suka, a fagen yaki, da kuma yadda ake amfani da karfi da jaruntaka. Yaro ya shiga cikin wannan hali har ya kai dan shekara goma sha hudu. To, shi wannan yaron kyakkyawan gaske ne, kuma lokacin da ya girma sai kyawon nasa ya karu ainun, har ya zamana duk mutumin da ya gan shi, mace ko namiji, sai ya tsaya ya dube shi, ya yi mamakin wannan cikakken kyau nasa. Tajul Muluki Karan dan sarki Sulaimanu Shahu ya gwanance wajen hawa doki kuma ya shahara wajen yaki da sadaukantaka, sannan kyawonsa ya sake bayyana, idan ya fita shagulgulansa duk inda ya gilma sai mutane su rud’e saboda kyansa da cikar halittarsa. Har wak’a jama’ar gari ke masa suna cewa: Na rungume shi na rinka mayen dad’i, Kamar reshen bishiya da iska na kad’awa Ba mayen giya ba ne kamar na bugagge, Tausasan leb’b’ansa sun fi zuma zak’ak’awa Idan dare ya tsala hasken rana ya tafi, A lokacin hasken kyawonsa ke bayyanawa Zuk’atan duka ‘yan Adam sun koma gun sa, Ba na fatar na zamo gun sa abin mantawa Idan na samu soyayya daga gun sa zan rayu, Idan na rasa soyayyarsa taho ya ki mutuwa Yayin da ya kai munzalin shekara sha takwas, kyawonsa ya dada bayyana ya zama kundukukinsa yana kyalli kamar yana makala musu jan dinari da ambar abar kallo kamar yadda mawaki ke fada: Ya zama magajin Yusufu gun kyau Masoya na firgita idan suka gan shi Mun gani a nan bisa kundukukinsa Alamun gado sun bayyana a gare shi Kwayar idanunsa sun zama baki mai kyau Sannan ya zam yana da bakin gashi Muna al’ajibin makaidaicin zamaninsa Aljanna ta tabbata da ganin murmushinshi Akwai daga al’ajabi da za a ce Musa Ya gamu da shi da ya tambayi sha’aninshi Yayin da ya zama cikin wannan hali ya kara girma ya isa ma’ishin mazaje hankali ya karu a gare shi da kuma kyawonsa ya sake bunkasa. Sai ya zamana a kullum yana dada samun sababbin abokai da masoya. Dukkan wanda ya kusata gare shi sai ya ji yana matuk’ar kaunarsa. Mutane suka rika yi masa fatar ya zama sarki bayan mutuwar mahaifinsa. Shi kuwa Tajul Muluk Allah ya sa masa matuk’ar son fita farauta, idan ya tafi daji sai ya zauna kwana da kwanaki yana farauta. Mahaifinsa ba ya son wannan dabi’ar ko kadan saboda yana ji ye masa tsoron kada wani abu ya same shi ko ya gamu da mugayen namun daji. Shi kuma ba ya jin wannan kashedin ko kadan. Har wata rana ma ya ce da hadimansa su yi shirin zaman daji na kimanin kwana goma. Su tanadi abinci da kayan bukata. Suka amsa wannan umarni. Suka debi duk abin da suke bukata suka shiga daji har tsawon kwana hudu sannan suka sauka wani waje mai cike da korran ciyawa kuma da namun daji masu yawa a wurin suna kiwo. Sannan ga bishiyoyi masu dauke ‘ya’ya nunannu da ruwan korama yana gudana. Taj ul Muluk ya ce da mabiyansa, "ku shirya tarko a wurin nan, sannan a sa faffadan ginshiki a zagaye shi da igiya." Suka bi umarninsa, babu jimawa suka kama dabbobin daji masu yawa wadanda suka yi ta gunji saboda ganin mutane alhali ba su saba da ganinsu ba. Kuma suka yi ta tsalle suna direwa saboda tsoron dawaki da irin kayan da ke shimfide a kan su. Dabbobin suka yi ta kiciniyar kubutar da kansu ta hanyar cizon tarkon tsalle da sauran dabaru. A karshe dai mafarautan

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16